Sashe 53
Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Kanta ta sunkuwar ƙasa tare da ɗanyin murmushi, kallonta tamayar ga wajen ɗan shaƙatawan dake cikin gidan wanda aka ƙawatashi da wasu kujeru guda huɗu masu kyau gaba ɗaya flowers sun zagaye wajen yayinda sukayiwa rumfar dake wajen ƙawanya, kallonsa tayi sannan tanufi wajen shima ya rufa mata baya. Akan ɗaya daga cikin kujerun ta zauna yayinda shima ya zauna akan kujeran dake facing nata. Ƙasa tayi da kanta tare da soma wasa da ƴan yatsun hannunta murya asanyaye tace. "Ina wuni!" murmushin daya bayyana dimples dinsa yayi batare daya amsa taba sai idanu daya zuba mata, sosai yau ɗin tayi masa kyau, don kokaɗan meckup ɗin dake kan beauty face ɗinta bai goge ba,  jin shiru bai amsata bane yasanyata turo bakinta gaba aɗan shagwaɓe tace "To ba gaisheka nake ba kuma kaƙi amsawa!" Murmushi yayi harsai da haƙwaransa suka bayyana. "To ae banji bane, please kiɗan ƙara ɗaya sainaji!" Yafaɗa cikin salon kwaikwayon maganarta.   Idanunta ta ɗago kana taɗan watsa masa hararan wasa tare da ɗan murguɗa masa ƙaramin bakinta dayasha baby pink colour lipstick, lumshe idanunsa yayi tare da jingina bayansa da jikin kujeran, wani irin shauƙi ne ke shigansa, sosai yanda tayi da bakinta yayi masa kyau, cikin wani irin yanayi yace. "Kullum ƙara kyau kike, idan kina fushi kyau kike ƙarawa, idan kina murmushi kyau kike ƙarawa, haka ma idan kina gabana kyau kike ƙarawa, inajin kamar sonki acikin jinina yake Zieyaderh, ko sau ɗaya ne please ki amsa min cewa kina sona!" yaƙare maganar yana me kafeta da mayun idanunsa wanda suka ɗan sauya kala, gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, kanta ta sunkuyar ƙasa tare da ɗan ciza laɓɓanta, ƙirjinta ne yake bugu da sauri, maganan aurenta da Almustapha ne yazo yayi tsaye aranta, tabbas tanajin wani abu na daban dangane da Pharouk, to amma bata da tabbacin cewa wannan abun soyayyace, koda ma acd sonsa take mecece amfanin soyayyar? yanzu burinta shine ta koyawa zuciyarta soyayyar Almustspha, dan sai da soyayya ne kaɗai zata iya kyautata masa azaman aurensu. Ɗago idanunta da sukayi raurau da hawaye tayi daniyar yiwa Pharouk magana, saidai tuni maganan nata ta maƙale sakamakon Ido biyu da sukayi da Almustapha dake tunkaro inda suke, ganin ta tsaida idanunta abayansa yasanyashi ɗan waigawa don ganin abunda take kallo, idanunsa ne suka sauƙa akan kyakkyawan saurayin dake zuwa garesu, kwata kwata bai wuce saura taku shida ya ƙaraso inda suke ba, tashi tsaye yayi yana me fuskantar saurayin, daidai lokacin Almustapha ya ƙaraso, dayake shi jan ajin nasa baya hanasa fari'a, hakan yasa bawani ɓata lokaci ya miƙawa Pharouk hannu don su gaisa, ganin haka yasa Pharouk ma bashi hannu suka gaisa, cike da kulawa Almustapha ya kalli Zieyaderh wanda kanta ke ƙasa, hakanan gabanta keta faɗuwa, cikin muryarsa me ɗauke da nutsuwa yace "Inason aron baƙon naki naɗan wasu mintuna, inafatan bazan takuraki ba?"
Wani iri taji yayinda wani irin nauyi da kunyarsa suka lulluɓeta alokaci guda, jikinta asanyaye ta miƙe tsaye tare da kaɗa kanta alaman "Babu komai" cikin nutsuwa haka tajuya tanufi cikin gida, ita kanta bazata iya tantance awani hali take ciki ba awannan lokacin. Kamar wanda ƙwai ya fashewa haka ta haura sama ko lura da Oummu dake tsaye a bakin kitchine batayi ba, Ajiyar zuciya Oummu ta sauƙe tare da duban hanyar da Zieyaderh'n tabi, wani irin fargabane taji ya kamata, sai yanzu takejin tsoron haɗin da tayi, musamman ma da taga yanayin da Zieyaderh'n tashiga ayanzu, shiru tayi tare da faɗawa wani sabon duniyar tunani.
Ita kuwa Zieyaderh tana shiga ɗaki ta rufo ƙofarta, samun kanta tayi da sulalewa ta zauna daɓas aƙasa, batare da ta ankara ba taji wasu hawaye masu ɗumi suna sauƙa akan ƙuncinta, tabbas wannan sabuwar ƙaddaran da ta tsinci kanta aciki tayi mata girma, ƘADDARA tana neman haɗa aurenta da Almustapha, sannan kuma agefe guda ga Pharouk da yake neman ta amsa masa soyayyarsa, ƘADDARA mafi girma awajenta kuwa itace soyayyar Mr.Helper, hannayenta tasanya ta share hawayenta, wata zuciya ce me bata ƙwarin guiwa akan ta yarda da duk wata ƙaddara da tazo mata me kyau ko akasin haka, samun kanta tayi da kwanciya luf akan gado, mintuna ƙalilan bacci ɓarawo ya saceta.
Pharouk. Gudu sosai yake sharawa akan babban titin gaba ɗaya hankali da tunaninsa baya jikinsa, maganganun da Almustapha ya faɗa masa suketa yi masa yawo acikin ƙwaƙwalwarsa, da ƙarfi ya daki steering motar ransa amatuƙar ɓace yace
"Bazan taɓa zama looser akaro na biyu ba SOORAJ, awannan karon tabbas bazan bari kasake nasara akaina kamar lokutan baya ba, bazan taɓa bari ka auri Zieyaderh ba SOORAJ!!" wani irin murmushi yayi tare da cije laɓɓansa, ahankali yashiga rage gudun da yakeyi tare da ƙoƙarin samarwa kansa nutsuwa tahanyar aminta da shawaran da zuciyarsa ta basa.
***
Oummu ce ta shigo cikin haɗaɗɗen ɗakin wanda yake mallakin Mijinta ne, Abba dake tsaye yana sanya garen kayansa ya ɗan juyo tare da kallonta murmushi yayi mata tare da cewa "Saboda kawai ɗanki zaiyi aure shiyasa kika kasa zaune kika kasa tsaye ko Sulaimiyya!" yaƙare maganar cikin yanayi na ɗan tsokana.
Murmushine ya faÉ—aÉ—a akan fuskarta tare da cewa "Yanzuma ai nashigo ne nasanar dakai abokan tafiyanka sun iso"
Murmushi ya kumayi tare da cewa "Bake kaɗai kikejin farinciki aranki ba Sulaimiyya nima inaji, saidai kuma ata wani ɓangare na zuciyata ina ɗauke da fargaban abun da zaije ya zo"
"Insha Allah Alhajina babu wani abu da zaizo sai alkhairin Allah!" Tafaɗa cikin son ƙarfafa masa guiwa.
Yaji daɗin maganan nata sosai hakan yasa yayi murmushi, har wajen motarsa Oummu ta rakasa inda ya haɗu da manyan aminansa su Uku suka kama hanyar airport, kai tsaye suka wuce Kaduna, daga nan kuma zasu shige cikin motocinsu su wuce ƙauyen saminaka.
Itakuwa Zieyaderh gaba ɗaya wunin yau batajin daɗin jikinta, hakanan takejin kanta cikin ƙunci, wani irin kewa me taɓa zuciya takeji yana ratsa duk ilahirin jikinta, gaba ɗaya su Shukra sun lura da rashin walwalan da takeyi kwana biyu, yanzuma zaune suke su duka ukun akan wani ɗan dakali suna me shan iskan dake kaɗawa asararin samaniya. Cikin yanayi naɗan zolaya Nasmah tace "Amarya badai wai cin amarcin aka fara tun yanzu ba? naga gaba ɗaya duk kin rame, sometimes kuma kina cikin damuwa"
Hararanta Zieyaderh tayi tare daɗan murguɗa mata baki cikin yanayin ɓata fuska tace
"Ni ba amarya bace"
Dariya Nasma da Shukra suka sanya, wanda hakan yaƙara ƙular da ita. "Uhumm kigama zille zillenki yarinya wallahi sai mun fidda ankon bikin ki ehe, sannan kuma sai mun sha rawa koya kikace Besty" Shukra tafaɗa tana kallon Nasmah. "Ƙwarai kuwa" Nasmah tafaɗa tana me gimtse dariyanta. Cikin turo baki gaba Zieyaderh ta miƙe daga zaunen da take tare da nufar hanyar da zai sadata da class ɗinsu. Kallo su Nasmah suka bita dashi harta ɓacewa ganinsu, sannan suka sa dariya, har acikin ransu su mamakinta suke na yanda gaba ɗaya tabi ta takura kanta.
Acan Ƙauyen Saminaka kuwa Tuni Abba sun gana da Malam Garba baban Zieyaderh, inda yayi musu karɓa ta mutumci, babu laifi kuma sun yaba da halin karamcin daya nuna musu, nan suka zauna suna me sake fahimtan juna, sam su Abba bada wasa suka ɗauko maganan auren ba hakan yasa lokaci guda suka gama magana inda Malam Garba ya shaida musu cewa ya basu auren ƴarsa Zieyaderh, Alhaji Maham ɗaya daga cikin aminan Abba shi ya ciro wasu kuɗi dake cikin aljihunsa inda ya miƙa amatsayin sadakin auren Zieyaderh, naira dubu ɗari ne cas, cewar da sukayi basason bikin ya ɗauki lokaci ne yasanya Malam Garba cewa suyi haƙuri suɗan bashi lokaci zuwa nan da kwana huɗu zai sanar dasu kowani lokaci ya yanke, shikuwa yayi hakanne don yanason tattaunawa da Zieyaderh akan batun auren, domin tun da aka fara batun auren baiji ta bakinta ba kuma itama tana da haƙƙi, cikin mutumta juna su Abba sukaiwa Malam Garba sallama inda suka kama hanyar dawowa cikin garin Kaduna.
..........