← Book details Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 93

Sashe 77

Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

7:00 am daidai alarm ɗin dake ɗaure bisa kan bedside ɗin gadon yasoma ƙara,  sannu ahankali ƙaran alarm ɗin ke ratsa cikin kunnuwansa,  ahankali ya buɗe idanunsa inda ya sauƙesu akan kyakkyawar fuskarta wanda take gab da tasa fuskar, hannunsa yakai ya kashe alarm ɗin,  ɗan janye jikinsa daga nata yayi tare da tashi zaune, idanunsa yakai jikin window'n ɗakin, nan yaga tuni haske ya bayyana ta jikin window'n alaman Safiya tayi, hannunsa yasanya ya dafe goshinsa, sam baiso ya makara ba, ajiyar zuciya ya sauƙe cikin zuciyarsa yace. "Me yasa aduk sanda takwana ajikina saina makara?."
Ɗan lumshe idanunsa yayi tare da buɗesu alokaci guda, juyawa yayi ya kalli innocent face ɗinta,  ahankali yaƙe ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo, zara zaran eye lashes ɗinta dake kwance luf bisa idanunta ya kalla, kana ya kalli lallausan eyebrow ɗinta wanda suke baƙaƙe siɗik sai shining suke,  kallonsa yakai izuwa kan ɗan ɗan dogon hancinta dayatafi straight har kusa da bakinta,  ɗan ƙaramin bakinta ya kalla wanda laɓɓanta ke ɗauke da pitch colour, lumshe idanunsa yayi ahankali yace "You look so beautyful."  hannunsa yakai inda ya shafi gefen fuskarta,  ahankali ya sauƙo daga kan gadon,  kaitsaye bathroom ya nufa, shower ya sakarwa kansa tare da lumshe idanunsa,  baiwani jima acikin toilet ɗinba yafito,  wani combat jeans dark blue ya sanya tare da wata farar t-shirt,  agurguje ya shimfiɗa sallaya tare da tada sallah,  yana idarwa ya shafa addu'a kana ya miƙe tsaye,  jikin gadon ya ƙarasa har yanzu bacci takeyi, zama yayi agefen gadon tare da sanya hannunsa yaɗan ja yatsun ƙafarta,  kyawawan idanunsa ya zuba mata ganin ko zata buɗe idanunta, amma ko alaman motsawa batayi ba,  murmushin daya bayyana zallan kyawunsa yayi tare da sanya hannunsa yaɗan shiga jijjigata.
Cikin bacci taji yanda yake jijjiga jikinta, ɓata fuska tayi tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, ashagwaɓe ta buɗe idanunta, take idanunsu suka sarƙe cikin na juna,
da sauri ta kulle idanunta tare da sakin wani kuka mai kama da shagwaɓa, idanunsa ya zuba mata tunda yake bai taɓa ganin shagwaɓaɓɓiya kamar ta ba, komai kuka saikace wata ƴar ƙaramar yarinya.
"Tashi kiyi sallah." yafaÉ—a cikin husky voice É—insa kana yana me kau da kae daga kallonta.
Bakinta tasake turowa gaba, cikin ɗan kuzarin da take dashi ta tashi daga kwancen da take,  ɗan yaye bargon dake jikinta tayi, cikin sauri tajawo towel ɗinta dake yashe akan gadon ta ɗaura,   ɗan satan kallonsa tayi tare da yunƙurawa ta sauƙa daga kan gadon, wani irin ƙara ta sake alokacin da taji wani irin raɗaɗi ya ratsa gaba ɗaya jikinta, jitayi kamar an watsa mata barkono,  rumtse idanunta tayi tare da fashewa da kuka, cikin tsananin shagwaɓa tashiga yayyarfa hannunta, tana me ƙara sautin kukanta, lumshe idanunsa yayi tare da sanya hannunsa ya ɗan dafe kansa da har yanzu keyi masa ciwo, shikan yashiga half ya ɓarowa kansa liƙi,  juyowa yayi cikin sanyin murya yace.
"Menene?."
Bata kallesa ba, bata kuma daina kukan ba, kana kuma bata ce masa ƙala ba saima ƙara yarfa hannuwanta da takeyi, ahankali take ɗan bubbuga ƙafafunta aƙasa.
Ganin batace masa komai ba yasanyashi miƙewa tsaye ya ƙaraso inda take, yana zuwa ya kamo hannunta tare da ƙoƙarin janta zuwa toilet,  ƙara sautin kukanta tayi tare da ƙwace hannunta ta durƙushe awajen,  ɗan ranƙwafowa yayi cikin kulawa yasanya hannunsa ya kamo duka hannayenta, cikin tausasa murya yace.
"Wani abu na damunki ne?."
Kanta ta kaÉ—a masa alamar "Eh."
Kyawawan idanunsa yaɗan lumshe tare da buɗesu,  in a silent voice yace.
"To mene ke damunki, kinajin zafi ne?."
Cikin shagwaɓa ta kwaɓe fuskarta dake ɗauke da hawaye shaɓe shaɓe, zafi takeji sosai aƙasanta, amma taya zata fara faɗamai cewa nan wajenne keyi mata zafi, ita kunya takeji.
Baki ta sake buɗewa daniyar ta sakar masa kuka, da sauri ya ɗaura hannunsa akan laɓɓanta, cikin wata irin murya yace.
"Shiii stop crying, tell me what happening?." Ya faÉ—i maganar yana me kama shoulders É—inta.
Idanunta wanda sukayi jajur ta ɗago ta kalleshi kallo irin mai kama da harara,  ganin shiɗinma kallonta yake da rikitattun idanunsa yasanya ta kwaɓe fuska, cikin shagwaɓa ta shiga dukan faffaɗan ƙirjinsa,  lumshe idanunsa yayi tare da ƙara kama shoulder ɗinta,  sosai ta zage iya ƙarfinta tana dukan chest ɗinsa,  shiru yayi yanajinta, don kanta tagaji da dukan nasa ta bari, faɗawa cikin jikinsa tayi tare da sakin wani kuka marar sauti.
Caɗak ya ɗagata  tare da nufar hanyar bathroom da ita, don yafahimci cewa tafiyanne bazata iya ba.
Acikin wani haɗaɗɗen jakuzzie ya ajiye ta, duban kyakkyawar fuskarta yayi, bakinsa yakawo daidai saitin kunnenta,  cikin magana mai kama da raɗa yace.
"Inazuwa."  Juyawa yayi yafita daga cikin toilet ɗin inda yabarta kwance acikin jakuzzie, jin husky voice ɗinsa yasanya taji gaba ɗaya tsikar jikinta sun mimmiƙe, lumshe idanunta tayi tare da gyarawa kanta kwanciya acikin jakuzzie'n wanda ruwan cikinsa keta tashin daddaɗan ƙamshi.
Kaitsaye fita yayi daga ɗakin,  ƙofar da zai sadasa da ɓangaren Oummu ya nufa,  murɗa handle din ƙofar yayi take yasamu kansa acikin babban falon na Oummu, direct babban kitchine ɗin dake cikin falon ya nufa, agurguje ya dafa ruwan zafi acikin kettle,  yana fitowa daga cikin kitchine ɗin Oummu da dawowarta kenan daga tafiyar da tayi ta murɗa ƙofar falon ta shigo bakinta ɗauke da sallama,  can ƙasan maƙoshi ya amsa sallaman nata tare da tsayawa turus yana kallonta, itama tsayawa tayi tana kallonshi, cikin mamakin ganinsa a part ɗinta tace.
"RAJ me kakeyi anan?."  wani lokaci takan ƙirasa da sunan RAJ kamar yanda gaba ɗaya abokansa ke ƙiransa.

Fuska ya kwaɓe tare da yin ƙasa da kansa, kettle ɗin dake hannunsa wanda ke cike da ruwan zafi ya nuna mata, alaman shi yazo ɗauka.
Kallon tsab Oummu tayi masa, zuciyarta É—auke da mamaki don tasansa bako da yaushene yake amfani da ruwan zafi ba, musamman ma a irin wannan lokacin, me kuma zaiyi da ruwan zafi?.

(to fa readers me kuma سوراج zaiyi da ruwan zafi? Oummu na tambaya sai ku bata amsa😝 then masu cewa bana update da wuri ku kwantar da hankalinku maybe daga yau zanna baku update kullum)
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*SOORAJ!!!*

*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*Wattpad*
@fatymasardauna
#Love

*Chapter 52*
Chapter 77 · 0% Book details