← Book details Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 93

Sashe 62

Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kan Zieyaderh ne ya ɗaure sosai don sam takasa fahimtan inda kalaman Oummu suka dosa, cikin sarƙewar murya tace "Oummu Nayarda da ƙaddara me kyau da kuma akasinta"
Ajiyar zuciya Oummu ta sauƙe tare da dafa shoulder ɗinta,  cikin rauni tace
"Yana da buƙatarki acikin rayuwarsa, haƙiƙa nasan SOORAJ yana da damuwa yana kuma da buƙatar mai magance masa wannan damuwan,  kiyi haƙuri ki karɓeshi amatsayin mijinki!"
Azabure Zieyaderh ta matsa baya tare da zaro idanunta cikin wani irin kaɗuwa ta soma jijjiga kanta yayinda gaba ɗaya jikinta ya ɗauki rawa, jin sauƙan kalaman Oummun tayi tamkar sauƙan  aradu acikin kunnuwanta,  ganin yanda ta firgice yasanya Oummu kamo hannuwanta cikin sanyin murya tace "Nasan zakiji ba daɗi, sannan nasan bamu kyauta miki ba amma ya zamuyi ki ɗauka wannan tsarin Allah ne bana muba, dan Allah Zieyaderh ki riƙi aurennan amatsayin ƙaddaranki"
tuni idanun Oummu sun cicciko da ƙwalla.   Rungume Oummu Zieyaderh tayi tare da sakin wani irin fitinannen kuka, kuka sosai takeyi yayinda gaba ɗaya jikinta ke karkarawa, jin Oummun takeyi kamar uwa mahaifiya agareta, cikin kuka  tace "Kidaina roƙona Oummu ke uwace agareni kodawa kika haɗani bazan gujeba, bazan bijiremiki ba Oummu bazan taɓa gujewa hukuncinki agareni ba!!"
ta faɗi maganar tana me sakin sheshheƙan kuka, wasu irin hawayene suka sauƙo daga cikin idanun Oummu tabbas saiyanzu taƙara tabbatar da cewa batayiwa ɗan nata zaɓen tumun dare ba, wani irin ƙwarin guiwa da farincikin samun Zieyaderh amatsayi suruka da tayi tasanya hannunta akan bayan Zieyaderh dake kuka ahankali take shafa mata bayannata tare da cewa. "Nagode sosai Zieyaderh Allah yayi miki albarka!"
Zaunar da Zieyaderh'n tayi akan gadonta tare da soma ƙoƙarin share mata hawayen dake gudana akan fuskarta, cikin so da ƙaunarta tace "Ya isa haka kwanta ki huta kada ciwon kai ya kama ki!"  a irin halin da take ciki batajin zata iyayiwa Oummu musu,luf ta kwanta akan gadon Oummu'n tare da cusa kanta acikin pillow, Oummu ce tafita aɗakin don amsa ƙiran wayan da akeyi mata, tanajin ficewar Oummu aɗakin tasaki wani sabon kuka mai tsuma zuciya kuka takeyi sosai wanda har saida numfashinta yasoma ƙoƙarin ɗaukewa,   gaba ɗaya tunani da nutsuwa sun gudu daga gareta, jin motsin kamar za a bude ƙofar ɗakin ne yasanyata haɗiye kukanta tare da rufe idanunta, yanayin yanda zuciyarta ke bugawa yasanya ta sake cusa kanta acikin pillow'n, ajiyar zuciya da numfashi take ta sauƙewa ahankali, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci bacci ɓarawo yayi gaba da ita.

Tunda ya kwanta bai tashiba sai ƙarfe 4, da wani irin zazzafan zazzaɓi ya buɗe idanunsa yayinda yakejin gaba ɗaya komai na duniya bayayi masa daɗi, lumshe rinannun jajayen idanunsa yayi tare da ɗan yunƙurawa, cikin ɗan kuzarin daya rage masa ya zuro da ƙafafunsa ƙasa,   koda ya miƙe tsaye wani luuuu haka yaji tamkar wanda zai faɗi, adaddafe ya nufi bathroom ɗinsa. Shower ya kunna tare da sanya hannunsa gaba ɗaya ya dafe bango, lumshe idanunsa yayi tare da sakin ajiyar zuciya, sauƙan ruwan shower ɗin akansa ba ƙaramin nutsuwa ya samar masa ba,  sake gyara tsayuwarsa yayi still hannayensa dafe da bango ya lumshe kwawawan idanunsa, sannu ahankali komai ke dawowa cikin ƙwaƙwalwarsa, sai yanzu yakejin nutsuwar yin tunani,   wani irin saliva me ɗaci ya haɗiya amaƙoshinsa,   tabbas ƘADDARA tayi masa sauyi irin wanda bai zata ba, kusan minti 20 ya ɗauka agaban shower'n ruwa na dukan pure skin ɗinsa, jikinsa ya janye kana ya kashe shower'n, gaban sink ya ƙarasa tare da ɗauro alwala.   
Cikin wani tsadadden getzner blue colour ya shirya kansa, wanda yaji ɗinkin half jumper,  sosai kayan sukayiwa jikinsa kyau,  sallaya ya shumfuɗa inda ya gabatar da sallan La'asar, wanda baisamu daman yiba sakamakon bacci da yake.  Wayoyinsa ya tura acikin aljihun wandonsa, ɗan jim yayi tare da jingina bayansa da jikin bango, wani irin sarawa kansa keyi masa yayinda zazzaɓi ke ƙara cin ƙarfin jikinsa, idanunsa da ako yaushe suke farare ƙal sai gashi yau gaba ɗaya sun sauya kala sun koma launin ja,  key ɗin motarsa ya ɗauka inda ya murɗa handle ɗin ƙofar ya fice,  mercedes ɗinsa ya buɗe ya shiga, kansa ya kifa ajikin steering motar tare da fesar da wani irin numfashi, wayarsa ce takawo haske alaman shigowar saƙo, ganin sunan Oummu yasanyashi shiga cikin saƙon.   _"Kozo cikin gaggawa inason ganinka!"_  shine abun da aka rubuta acikin saƙon,
Murza key É—in motar yayi tare dayin reverse, maigadi ne ya wangale masa gate ya tura hancin motar tasa waje.
Gudu sosai yakeyi akan titin wanda shikansa baisan dacewa gudu yakeyi ba domin gaba É—aya nutsuwarsa bata jikinsa, gawani irin ciwon kai dake addabarsa kamar kansa zai rabe gida biyu haka yakeji.

Tashinta kenan daga baccin da tayi, wani sabon zazzaɓine yasake rufeta saidai na yanzu baikai na ɗazu ba, hakan kuma yana da nasaba da kukan da tasha ta ƙoshi, Aunty Muhibbat ce ta tursasata akan cewa taje bathroom ɗin Oummu tayi wanka tazo ashiryata don anjima da dare za'a damƙata ga Mijinta, badon tasoma haka Aunty Muhibbat tasata agaba harcikin toilet suka shiga ta haɗa mata ruwan wanka, cikin rashin kuzari tayi wanka yayinda ta ɗaura wani farin towel ajikinta, kwata kwata iya cinyarta towel ɗin ya tsaya,  hannunta tasa ta dafe kanta sakamakon tunowa da cewa tabar kayanta akan gadon Oummu, sannan kunya bazai barta tafita da wannan ɗan ƙaramin towel ɗin ba.

Daga waje yayi parking motarsa inda yashiga cikin gidannasu da ƙafafunsa dayake magriba ta kawo kai sannan gaba ɗaya mutanen da suka zo bikin suna ɗayan ɓangaren dake cikin gidannasu hakan yasa kai tsaye ya wuce ɓangaren Oummu ganin bai ganta afalo bane yasanyashi haurawa sama kaitsaye. 
Ahankali taɗan buɗe ƙofar ban ɗakin ta leƙo kanta, ganin babu kowa acikin ɗakinne yasanyata fitowa cikin sauri batare da ta tsaya goge ƙafanta dake ɗigan ruwa ba,
yana zuwa  ya ɗaura hannunsa akan handle  ɗin ƙofar tare da turata ciki, daidai lokacin ita kuma ta kawo tsakiyan ɗakin jin motsin taɓa ƙofa yasanya ta juyo arazane bisa tsautsayi ruwan dake ƙafanta ya gogi tiles take tsantsin tiles ɗin ya ɗebeta wani irin ƙara ta sake yayinda towel ɗin dake jikinta ya zame yayi ƙasa. 

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

           *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

             *WATTPAD*
        @fatymasardauna
#romance

             *Chapter 45*

Wani irin ƙara ta sake yayinda towel ɗin jikinta ya zame ya faɗi ƙasa,  cikin tsautsayi ƙafanta ya bugi jikin gado, suuuuu haka tatafi zata faɗi, cikin abun da baiwuce 1 second ba ya ƙaraso cikin ɗakin, da sauri yaƙarasa tare da sanya duka hannayensa biyu ya tarota, inda ya zube ƙasa kan guiwowinsa, cikin tsananin tsautsayin dake jansa ya sauƙe idanunsa akan naked pure white breast ɗinta, da sauri ya rumtse idanunsa yayinda lokaci guda yaji tamkar andoka masa guduma atsakiyar kansa,  gaba ɗaya jikinsa ne ya soma ɓari,
Ita kuwa Zieyaderh tamkar wata matacciya haka gaba ɗaya jikinta ya sandare, yayinda ta kulle idanunta ƙaƙam, cikin tsananin tsoron dake ɗawainiya da zuciyarta haɗi da fusgewar numfashi ta ɗan buɗe idanunta kaɗan, wani irin ƙara tasake sakamakon ganin fuskarsa da tayi, cikin tsananin ruɗewa haɗi da zabura ta tashi daga jikinsa,
aruɗe ta soma ƙoƙarin neman towel ɗinta daya faɗi, don suturce jikinta, irin yanayin ruɗewan da tayi yasanya takasa ganin towel ɗin, wanda kuma yashe yake agabanta,  cikin hanzari ta jawo blanket ɗin dake kan gadon na Oummu ta rufe gaba ɗaya jikinta dashi, zamewa ƙasa tayi tare da sakin wani irin marayan kuka wanda ke ɗauke da tsananin takaici da kuma haushin kanta, wata fitinanniyar kunyace gaba ɗaya ta rufeta.

Jin diran sautin kukanta da yayi acikin kunnuwansa, yasanyashi miƙewa daga durƙuson dayayi, cikin dauriya dason kawar da zazzafan ciwon kan daya kawo maza cafka lokaci guda, ya juya tare da nufan hanyar barin ɗakin.
Kasancewar har yanzu idanunsa arufe suke, hakan yasanya sam baikula da Oummu da kuma Aunty Muhibbat dake ƙoƙarin shigowa cikin ɗakin ba,
jin cewa yayi karo da mutum ne yasanyashi saurin buɗe idanunsa, nan ya sauƙe su akan fuskar Oummu dake tsaye tana kallonsa,  kansa ya sunkuyar ƙasa tare da raɓawa ta gefenta zai wuce, cike da mamakin yanda idanunsa sukai jajur Oummu tace.
"Kajirani a falon ƙasa".

Kansa kawai ya jinjina mata alaman. "To"
Ahankali yashiga taka matattakalan da zai sadasa da falon ƙasan. 

Oummu kuwa dubanta takai ga Aunty Muhibbat,  gane abun da Oummun ke nufi yasanya Aunty Muhibbat murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ta shiga da sauri, don ta duba Zieyaderh wacce sautin kukanta ke ratsa kunnuwansu.
Oummu kuwa juyawa tayi tare da fasa shiga ɗakin, kaitsaye tanufi matattakala don sauƙa ƙasa.

Da auri Aunty Muhibbat ta ƙaraso inda Zieyaderh'n ke zaune, yayinda ta takure jikinta waje ɗaya acikin blanket tana kuka.
Kallon towel ɗin dake ƙasa Aunty Muhibbat tayi tare da sakin murmushi, cikin kulawa ta zauna akan gado tare da sanya hannu ta dafa kafaɗa Zieyaderh.

"Jikinne har yanzu?"  ta tambaya tana me ƙoƙarin jawota ta zaunar da ita akan gadon Oummu.

Jin muryar Aunty Muhibbat acikin kunnuwanta, yasanyata sake ɓoye kanta acikin blanket, tare da ƙara sautin kukanta.

Still murmushi Aunty Muhibbat tayi cikin rarrashi tace.
"Kukan ya isa haka, ko so kike kanki yayi miki ciwo? maza  tashi ki sa kayanki kinji, ko SOORAJ yayi miki wani abune?" Aunty Muhibbat ta tambaya.

Cikin sheshsheƙan kuka tagirgiza kanta alaman.
"A'a"

Murmushi Aunty Muhibbat tayi tare da cewa.
"To tashi kisa kayanki, ko so kike kowa yazo yana ganinki ba kaya?"

Cikin nutsuwa Oummu ta kai dubanta garesa, murya asanyaye ta ƙira sunanshi.
Amsa mata kawai yayi batare daya É—ago kansa ya dubeta ba.
Chapter 62 · 0% Book details