Sashe 20
Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
7:00
Daidai ta gama shiryawanta, tayi kyau acikin uniform É—inta kamar kullum, tana kammala saka white socks É—inta, tasoma jin ana knocking Æ™ofar falon, school bag É—inta ta rataya bisa kafaÉ—anta sannan tafi ta zuwa falon, dama bata saba ganinshiba don haka batasa aranta zata ganshi ba. Tana buÉ—e Æ™ofar wanda ke kawo mata abinci kullum yaÉ—an yi mata murmushi, itama murmushin tayi masa tana Æ™oÆ™arin gaidashi ne ya miÆ™o mata wata kula mai kyau wacce take da É—an mariÆ™i a samanta.Â
"Madam ga saƙonki inji Oga" yace da ita.
Karɓa tayi, shikuma ya juya yayi tafiyarsa, komawa cikin falon tayi tare da buɗe kulan. Kulan irin mai hawa ukunnanne wato (3pieces) hawan farko da ta buɗe soyayyen dankali ne aciki wato chips da kuma ƙwai, sai hawa na biyun dake ɗauke da gasashshen nama mai albasa, hawan ƙarshe shine ke ɗauke da shinkafa fried rice wacce taji liver, ɗaukan kulan tayi ta riƙe ahanunta, tana fita waje ta samu Kamalu yana tsaye ajikin mota yana jiranta.  Tunda suka ɗauki hanyar makarantar yau Kamalu keta mata zuba, ita dai ba gadon magana bace hakan yasa take amsa masa kaɗan kaɗan, shikuwa sai labarai yaketa bata, ganin yanda take amsa masa ne, yasa aranshi yace "Duk yanda akayi itaɗin jinsin Oga ce, da'alama duka zuri'arsu haka suke basason magana"
Yau kam Su Nasmah sun rigata zuwa, tana zama Nasmah ta ce "Ki koma kinyi late"
Dariya ta yi tare da ɗan satan kallon Shukrah, matsawa kusa da Nasmah tayi sosai cikin ƙasa da murya tace.
"Yau maiyasamu Shukrah na sake ganin fuskarta babu walwala?"
Baki Nasmah ta taɓe haɗe da cewa. "Hmm barta kawai kekam wahalane bai ishetaba, wai fa soyayya take kullum kuma sai sunyi faɗa da saurayin"
Idanu Ziyada taÉ—an zaro waje cike da mamaki tace. "Soyayya!"
"Eh Soyyayya" Nasmah ta faÉ—a tana É—an kallonta.
Shiru Ziyada tayi tare da jin wani abu acikin ranta. "Kenan dama Soyayya gaskia ce?"Â tambayar da tayiwa kanta kenan sannan ta kuma sake tambayar kanta "Menene alamomin soyayya?"
"Yanaga kamar kina tunani" Cewar Nasmah da ta shiga mamakin yanayin da taga Ziyada ta shiga.
"Babu" Ziyada tafaÉ—i haka tana É—an yin murmushi, Malamin English ne ya shigo cikin ajin hakan yasa suka bada gaba É—aya hankalinsu gareshi.
Yau a wajen da aka tanadar musamman dan cin abincin É—alibai sukaci abincinsu,  ita dai Shukrah gaba É—aya bata da wani walwala, Ziyada da Nasmah ne kawai suketa sha'aninsu.  ShaÆ™uwar da ke tsakanin Ziyada da Nasmah shine ke Æ™arawa Ziyada jin daÉ—in rayuwar makarantar.  Yau ba atashesu ba har sai biyar da rabi kasancewar anshiga dasu meeting akan jarabawan da zasu fara next month.  Agajiye ta dawo gida ga ciwon cikin dake sanÉ—anta, da ruwan zafi tayi wanka sannan ta kwanta.Â
 11:00 ta farka daga ɗan baccin daya ɗauketa, wani irin ciwon da cikinta keyi mata shine abun daya ɗaga mata hankali, Kuka take hanunta dafe da saman mararta wanda takejinta kamar zata ɓalle.
Yana zaune akan gado yana danna laptop É—insa, ahankali Æ™aran kukanta ya shiga kawowa kunnensa ziyara. Ɗauke hanunsa yayi daga kan laptop É—in tare da yin shiru yana mai sauraran yanda kukan nata ke tashi. Kallon agogo yayi yaga Æ™arfe 11:10 na dare, wata Æ´ar Æ™aramar tsuka yaja tare da sanya hanu ya dafe goshinsa. "Me na É—aukowa kaina ne?" tambayar da yayiwa kansa kenan.Â
Jin kukannata na daɗa ƙaruwa ne yasan yashi miƙewa, ƙofar ɗakin ya buɗe ya fita, tsayawa yayi ajikin ƙofar ɗakin da take yana mai tunanin shiga cikin ɗakin. Jin taƙi daina kukan ne yasashi murɗa handle ɗin kofar ya shiga.  Yashe ya ganta aƙasa tanata birgima gaba ɗaya gashinta ya watse akan tiles, kuka take irin na fitar hayyaci. Ƙarasawa yayi inda take yashe aƙasan tana ta mutsu mutsu, hannayensa yasanya ya kama kafaɗunta, jin sauƙar hanun mutum akan kafaɗunta yasanya ta kama hunun nasa ta damƙe da ƙarfi, da ɗayan hanunnasa da bata kama ba yayi amfani wajen ɗago haɓarta, gaba ɗaya fuskarta ta ɓaci da hawaye, zara zaran eye lashes ɗinta sun jiƙe da hawaye sun manne akan fatarta. Hanunsa dake cikin hanunta ta ƙara matsewa tare da sakin wani ƙara, ji take kamar taita buga kanta ajikin gini ko zata samu salama, ganin yanda take shiɗewa ne yasanya shi ɗagata caɗak ya nufi kan gado da ita, kwantar da ita yayi, tare da ɗauko magungunanta ya bata.
***
After 30 minute har yanzu gunjin kukanta ne ke tashi acikin ɗakin, sama da mintuna talatin kenan da bata magani amma har yanzu ciwon bai lafa ba, tun tanayin kukan da duka jarumtarta har takai tanayin kukan acikin yanayi na galabaita, hankalinsa ne yasoma tashi, wayarsa ya ɗauka ya ƙira Number'n Dr.Waleey, shaida masa abun dake faruwa Sooraj yayi, shiru yayi yana maijin amsar da Dr.Waleey ke bashi, cikin rashin ƙarfin guiwa ya aje wayartasa bayan sunyi sallama da Dr.Waleey'n, shiru yayi haɗe da zuba mata mayun idanunsa, sosai zuciyarshi ta karaya akanta, wani irin tausayinta yaji ya daki zuciyarsa, duk wanda yaganta acikin irin wannan halin sai ya tausaya mata, musamman yanda tayi buji buji da gashin kanta, ga numfashinta dake ƙoƙarin sarƙewa tsabar kukan da tayi, maganganun Dr.Waleey ne suke dawowa cikin kunnensa. Bayajin zai iya aikata abun da Dr.Waleey yace yayi, sannan kuma bayajin zai iya jure ganinta acikin halin wahala, baisan maiyasa yake jin son taimakonta ba tun farko, ayanzu yanaji inama da ace tun farko bai taimaketa ba, rumtse idanunsa yayi da ƙarfi sakamakon yanda yaga takeyi, baida wani zaɓi wanda ya wuce ya taimaketa, tashi yayi ya nufi gadon, sautin bugawar zuciyarshi ne ya tsananta yayinda ƙirjinsa ke tsalle kamar zai faɗo ƙasa, da ƙarfi bugun zuciyarsa ke harbawa...
(Na yau dana gobe duka na haɗa muku😠kuji daɗinku ku more, idan ku naga kamar naso kaina, sai ku karanta rabi yau gobe ku ƙarisa karanta rabi😂)
[12/April/2020]
*Vote Me On Wattpad*
@fatymasardauna kwana biu bana baku update da wuriðŸ™ðŸ» Fans É—ina na Facebook ina gaisuwa)
ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
       *SOORAJ !!!*
  *Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
_{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://facebook.com/kainuwawritersassociation*
      *WATTPAD*
   @fatymasardauna
#romance
     *Chapter 18*
Ƙirjinsa ne ke ta dokawa kamar zai fito waje. Yana ƙarasawa gaban gadon yaja ya tsaya tare da kafeta da idanunsa, jin kukanta yake har acikin ransa, hannayen rigansa ya ɗan naɗe tare da nufar toilet ɗin ɗake cikin ɗakin,   heater ya kunna ya tari ruwan zafi acikin wani ɗan madaidaicin bucket, towel ya ɗauko sannan ya fito daga cikin toilet ɗin.  Ƙafansa ɗaya yasanya ya taka kan gadon, baisan tayaya kuma ta ina zai fara ba, hakan baikamacesa ba, sannan kuma sam hakan ba aikinsa bane, saidai kuma sosai yake tausayin halin da take ciki. Aƙalla yaɗau kusan mintuna 10 a haka ya kasa aikata komai, yayinda ita kuwa har yanzu take aikin kuka gaba ɗaya tasake fita hayyacinta,  zama yayi akan gadon tare da sanya towel ɗin acikin ruwan zafi, hannayensa ne suka ɗauki rawa, ya kasa koda kai hanunsa jikinta, zuciyarsa bugawa take, hanunsa yakai kan wuyanta ya ɗan taɓa, ji yayi babu wani zazzaɓi sosai ajikinnata,  rumtse idanunshi yayi tare da kai hanunsa kan lafeffen cikinta, tamkar wanda aka jonawa shocking haka hannayensa ke rawa, da ƙyar ya iya ɗan ɗage rigan dake jikinta yayi sama dashi,  still hannayensa na rawa yasanya hanu ya ɗanyi ƙasa da sket ɗinta, towel ɗin yaciro daga cikin ruwan zafin tare da ɗan matsawa ya rage ruwan dake jiki,  sake rumtse idanunshi yayi tare da ɗaura towel ɗin adai dai kan cikinta, wani ƙara tasanya tare da ɗan soma yunƙurin tashi zaune, baisan sanda yasanya ɗayan hanunsa ya maida ita ta kwanta ba, sai alokacin ya samu damar buɗe idanunshi ya sauƙesu akan fuskarta, hawaye ne kawai ke gangarowa ta gefen idanun ta, gaba ɗaya ta galabaita. Sake danna towel ɗin yayi akan cikinta, gani yayi ta sake rumtse idanunta, ahankali yake ɗan matsa towel ɗin akan cikinta, ƙasa ya somayi da towel ɗin daidai kan mararta ya tsaya, Yanayin yanda yake matsa towel ɗin akan maranta ne, yasanya ta jin wani ɗumi na ratsa gaba ɗaya ilahirin jikinta, sake maida towel ɗin cikin ruwa yayi tare da ɗan matsewa, sake manna mata yayi akan maranta, haka yadinga yi mata har tsawon wasu lokuta, ahankali kukanta ya tsaya cak, wani irin ajiyar zuciya take sauƙewa akai akai, fitar numfashinta ne ya soma sanja sauti, ya zama na yana fita slowly,  duk wannan abun da yake mata, bai bari idanunshi sun kaishi ga kallon jikinta ba. Cikin wani irin yanayi na wahala ta kamo hanunsa na hagu ta riƙe acikin nata hanun,  ganin haka yasa ya aje towel ɗin agefe, ɗan ranƙwafowa yayi tare da kawo bakinshi dai dai saitin kunnenta, ahankali ya soma hura mata iskan dake bakinsa acikin kunnenta. Daddaɗan ƙamshin turarensa ne ke ziyartan hancinta, yayinda iskan bakinsa dake hura mata ya kasance garkuwa wajen samun nutsuwarta, ahankali taji wani irin salama na sauƙar mata, cikin wani irin yanayi hucin numfashinsu ke gauraya waje guda, jin yanda sautin numfashinta ya sauya ne, yasanyashi ɗan ɗago da kansa ya dube ta,  gani yayi tana fitar da numfashi ahankali da alama bacci ne ya ɗauketa, wata ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauƙe, tare da ɗago kansa daga ranƙwafon da yayi, hanunsa dake cikin nata ya kalla wanda ta damƙeshi gam. Ƙoƙarin cire hanunsa daga cikin nata yayi, amma yaji ta sake riƙe shi gam, cikin ɗan dabara ya samu ya zare hanunshi, hannayensa ya ɗaura akan kafaɗunta tare da gyara mata kwanciya, blanket ya rufa mata, sannan ya rage mata hasken ƙwan wutan dake cikin ɗakin, tashi yayi ya fita tare da jawo mata ƙofar.   Ɗakinshi ya koma yayi kwanciyarsa, ya jima kafun bacci ɓarawo ya samu damar ɗaukarsa.