← Book details Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 93

Sashe 44

Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Almustapha yayi tare da sanya hannuwansa ya kama na Ummu. "Bazan taɓa iya bijirewa umarninkiba Ummu, ke uwace agareni saboda haka ina maraba da duk wani zaɓinki"

Murmushin jin daɗi Ummu tayi tare da sanya hannu ta shafa kansa cike da ƙaunarsa tace "Nagode sosai Almustapha Allah ya maka albarka!"

"Ameen Ummu, amma wace me sa'ace haka tayi gamdakatar É—in samuna?" cike da zolaya yayi tambayar.
Dariya Ummu tayi tare da cewa "Kanason sani?"

"Sosaima" Almustapha yabata amsa cike da zaƙuwa.

Duk abunda suke yanajinsu yana kuma kallonsu, amma ko uhummm baice ba, azahirin gaskiya wayarsa yake dannawa abaÉ—ini kuma gaba É—aya hankalinsa na garesu.

"ZIEYADERH itace wacce na zaɓama kuma itace wacce zatayi daidai da rayuwarka!"

Maganar Ummu data faÉ—ane yasanyashi É—ago da kansa ahankali ya kalleta..

"Zieyaderh!"Almustapha ya maimaita sunan abakinsa, kansa ya sunkuyar ƙasa fuska ɗauke da murmushi yace
"Na'amince!"

Tsaida duk wani abu da yakeyi yayi yana kallonsu, hakanan yaji tamkar ruwan jikinsa na ƙonewa.

(fever na damuna so banajin daɗin jikina please kuyi manage, wannan ma da ƙƴar nayi muku, idan naji sauƙi gobe Insha Allah zakujini🙏🏻)
Naziphi Yarima:
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

              *SOORAJ!!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

              *WATTPAD*
           fatymasarduna
#romance

              *Chapter 35*

Sunkuyar da kansa ƙasa yayi tare da ɗan ciza laɓɓansa, idanunsa ya mayar kan wayansa,  samun kansa yayi da kasa cigaba da amfani da wayan, ji yayi gaba ɗaya jikinsa yayi weak.

"SOORAJ!" Oummu taƙira sunansa.

Ɗago kansa yayi ya kalleta batare daya amsa mata ba, itama bata nemi amsawar nashi ba taci gaba da cewa  "Kaji abun da muka tattauna akai, amma bakace komaiba, sannan kuma inaso na yaba maka game da namijin ƙoƙarin taimakon da kayiwa Zieyaderh, insha Allah, Allah Zai baka lada!" Oummu tafaɗi maganar tana murmushi.

Ko Uhumm  baice ba, sai ma kallon Oummu'n daya keyi, ganin damuwarta dana Almustapha zasu kasheshi yasanyashi tashi gaba ɗaya yabar musu gidan.

Kwance take luf akan bed ɗinta, biscuit ne ahannunta tanaci da kaɗan kaɗan, turo ƙofar ɗakin da akayi ya sanyata tashi zaune da sauri,   ganin Oummu yasanya tasakin murmushi tare da cewa       "Barka da shigowa Oummu"

Murmushi Oummu tayi tare da zama akan wata kujera,   cike da kulawa tace.  "Magana nazo muyi dake Zieyaderh!"

Gaban Zieyaderh ne ya faÉ—i, amma saita dake tare da cewa "To"

Murmushi Oummu tayi tare da dafa kafaɗun Zieyaderh'n tace  "Inaso kishirya ƙarshen wannan week ɗin zamuje ƙauyenku dan inason naga mahaifinki!"

Dummm haka ƙirjin Zieyaderh ya bada wani irin sauti,  hawaye ne suka cika idanunta alokaci guda,  bakinta na rawa tace "To!"
Murmushi Oummu tayi don tafahimci cewa tsoron zuwa ƙauyen Zieyaderh keyi, cikin son kwantar mata da hankali tace "Kar kisanya tsoro aranki idan munje bazan barki ahannunsu ba zandawo dake nan, kawai dai naga ya kamata ace mahaifanki susan inda kike ne!"

Ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauƙe tare da gyaɗa kanta kawai, alaman ta gamsu.   Oummu na fita daga ɗakin. Zieyaderh ta fashe da kuka, sosai tayi kewar babanta, ko awani hali yake ciki Allah masani?  duk da cewa bai nuna mata ƙauna ba, amma ita har gobe, akwai ƙaunarsa acikin jininta, saboda koba komai Uba Uba ne koda baikasance na gari ba.

MONDAY

Cikin yanayi naɗan sauri sauri yake tafiya, don 8 daidai jirginsu zai ɗaga zuwa garin Lagos.  Sanye yake da black and white suit wanda suka matuƙar yi masa kyau, black cover shoe ne ƙiran kamfanin Gucci sanye aƙafansa me tsadan gaske. ƙamshi kawai yaketa zubawa, yayinda gashin kansa keta shinning na mayukan da aka shafa masa,  yau kam masha Allah Yayi kyau har ya gaji da haɗuwa. 

Manta biology text book  ɗinta da tayi, yasanya ta taho cikin sauri don komawa ta ɗauka, sam bata kulaba saiji tayi sunyi karo da juna,  wanda hakan yajawo zubewan documents ɗin dake  hannunsa.  Da sauri taja da baya ƙirjinta na bugu da ƙarfi, idanunsu ne suka faɗa cikin na juna, hakan yasanya taji tamkar an jona mata shocking,      kallonta yayi sannan ya kalli ƙasa inda documents ɗinsa suka zube,  da sauri ta durƙusa ƙasa hannunta har rawa yake wajen harhaɗa documents ɗin waje ɗaya.    Agogon hannunsa ya kalla yaga 7:30 kuma sai ya biya ta office kafun ya wuce airport, gashi duk gani yake kamar bata sauri wajen tattara documents ɗin.  Itakuwa bakomai ke cinta ba face tsoro hakan yasa gaba ɗaya bata sauri, ƙamshin mayen turarensa dake zautar da ita ne, ya daki hancinta sosai, hakan yasa ta ɗan ɗago da kanta, daidai lokacin shi kuma ya ɗan ranƙwafo don tattare documents ɗin, kanta ne ya bugi haɓanshi wanda hakan yasashi rumtse ido, ahankali yace "Auchhhh!!"  dan ya ɗanji zafi sosai.
Sakin documents ɗin tayi tare da sanya hannuwanta ta rufe bakinta, wani sabon tsoro ne  yasake kamata, baki na rawa tace "Kayi haƙuri Wallahi bansaniba ne!!"

Baikulata ba haka yasanya hannu ya shiga tattara papers ɗinsa da suka watse.  ganin haka yasa itama tashiga tayasa tattarewa,  gaba ɗaya ƙamshinsa ya jefata acikin wani irin yanayi, jin kanta take cikin wani  baƙon yanayi, har wani iska ne ke shiga jikinta.   Idanunta ne yakai kan wani papers da iska ke shirin kaɗasa wani wajen, da sauri takai hannunta zata kamo paper'n,  shima hannunsa yakai batare

da yayi zato ba yaji hannunsa ya sauƙa akan nata, atare sukaji wani shock da sauri yajanye hannunsa daga kan nata tare da ɗaukan paper'n ya miƙe tsaye, baijira komai ba ya nufi wajen motarsa wanda tuni dama driver na jiransa, yana shiga gidan baya driver yayiwa motar key suka fice daga cikin gidan.   Saida taji alamun fitansu sannan ta iya miƙewa tsaye daga tsugunnen da take,  batare da ta saniba wani murmushi ya bayyana akan fuskarta take kuma saiga hawaye sun ziraro daga cikin idanunta, Wallahi ko za akasheta bazata iya fassara abun da takeji dangane dashi ba, tausayi ne? rauni ne? Ita duk takasa ganewa, tasan koma menene tabbas abun da takeji akanshi na musammanne,  idanunsa kaɗai da ta kalla ya sanya taji wani iri ajikinta, tabbas da zata samu mai bata amsar abun da takeji dangane dashi da taso hakan fiye da komai, watarana idan tagansa sai taji kamar tasanya masa kuka, watarana kuwa jitake kamar taje da gudu ta shige jikinsa tayi kuka sosai, wataƙila hakan zai ɗan sama mata salaman abun dake ranta.    Sam tama manta da cewa text book zata ɗauko sai kawai ta koma tashiga mota.
Luf tayi ajikin kujeran motar,  ƙamshinsa da har yanzu takejinsa acikin hancinta shiyayi fatali da duk wata nutsuwarta, sam tarasa me yasa takejin ƙamshin nasa har yanzu duk da cewa baya tare da ita,  hannunta takai tashafi fuskarta, sai alokacin ta gano daga inda ƙamshin ke fitowa, sake kai hannunta kan hancinta tayi tare da shunshunawa, tabbas hannunta da ya taɓa ne ke ƙamshin, wani irin sanyi taji acikin zuciyarta, ɗaura hannun tayi akan fuskarta tare da lumshe idanu, ahaka har suka iso cikin school ɗin.  Yau kam tayi late duk da cewa bahaka tasoba, don sunada biology, kuma shine first period, bakuma taso tayi missing lecture ɗin biology ko kaɗan,     ai kuwa tana zuwa bakin class ta iske malami aciki, da ƙyar ya barta tashiga cikin ajin, tana zama akan chair ta sauƙe ajiyar zuciya, hannu Nasmah tasanya ta ƙasa ta muntsineta akan cinyarta,   ƙasa ƙasa tayi dariya tare da rumtse ido alaman taji zafin muntsinin, hakan da tayi kuma sai ya tuna mata da MR.HELPER ɗinta, yanayin yanda ya rumtse idanunsa da kuma yanda yace "Auchhh!!" Baƙaramin kyau yanayin yayi masa ba, musamman yanda pink lips ɗinsa suka motsa abun saiya ɗauki hankalinta, sai ayanzu moment ɗin kedawowa cikin brain ɗinta da kyau, wani murmushi tasake tare da lumshe idanunta.
"Kenan shima yanajin zafi idan abu yasameshi?" A zuciyarta ta tambayi kanta, wani murmushin ta sakeyi alokacin da ta tuna da kyawun idanunsa, a iya tsawon rayuwarta itakam bataga irinsa ba, bata kuma tunanin zata taɓa ganin wani irinsa.    Ataƙaice dai  har biology teacher'n yafita, bata tsinci komai daga cikin darasin daya koyar ba,  gaba ɗaya hankali da tunaninta yau akan Mr.Helper yake. 
Su Shukra da kansu yau sun fuskanci cewa tana cikin farinciki, don koda aka fita break zagewa tayi tayita zuba musu surutu. 

7:59 AM

Gyara zama yayi tare da ɗaura sit belt ajikinsa, bayansa ya jingina ajikin luntsumemiyar kujeran dake cikin jirgin, 8:00 daidai jirginnasu ya ɗaga zuwa sararin samaniya,  tafin hannunsa yakai ya rufe fuskarsa, ko hakan zaisa yaɗan rage stress ɗin dayake ciki, ahankali yaji wani baƙon ƙamshi na ratsa cikin hancinsa yana me cakuɗa da numfashinsa, mamakine yakamasa don sam baisan daga ina ƙamshin ke fitowa ba, ɗan waigawa bayansa yayi,  dayake  ɓangaren business class ne kowa sha'aninsa kawai yake, babu kowa kuma akusa dashi dasai yace na kusa dashine ke ƙamshin.  Sake shunshuna hannunsa yayi, sai alokacin ya tabbatar da cewa tabbas hannunsa ne ke ƙamshin, bawani turarene me ƙarfi ba, irin dai turaren nanne da idan mutum yasa saima ka matso kusa dashi kafun kajiyo ƙamshin.   "Itace!" yafaɗa in a silent voice ɗinsa, sake kai hannun kan hancinsa yayi tare da ɗan taɓe lips ɗinsa.   Azuciyarsa yace.
"Su ƙamshi manya"   Jarida ya ɗauka yashiga karantawa tare da watsar da duk wani tunani dake ransa.

Hadari ne sosai ya haɗu agarin kasancewar anacikin yanayi na damuna,  3:30 pm, fitowarsu sallan La'asar kenan.
Tana idar da sallan ta fito daga cikin masallacin, sosai take matuƙar son yanayi irin wan
Chapter 44 · 0% Book details