← Book details Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 93

Sashe 24

Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaye yake agaban drawer, dagashi sai dogon wando fari dake sanye ajikinsa, yayinda murɗaɗɗiyar surar jikinsa ta bayyana, gaba ɗaya shape ɗin bayansa abun burgewa ne.  Kayansa yake cirowa daga cikin drawer'n yana shiryawa acikin trolly bag ɗin dake aje kan gadonsa. yana gama shirya kayannasa ya ɗauki wata rubber t-shirt yasanya ajikinsa.   Wata jaka ya ɗauko irin wacce ake goyawa a baya, buɗe jakan yayi ya zuba wasu takardu aciki,  saida ya tabbatar daya haɗa komai nasa wanda yasan zai buƙata, sannan ya ɗauki wayarsa ya sanya acikin aljihunsa, direct falo ya nufa. Direct dinning area ya nufa, haɗa tea ɗinsa yayi, tare da dawowa cikin falon ya zauna.   Sipping tea ɗin yake ahankali, yayinda lokuta zuwa lokuta ya ke kai dubansa  ga agogon bangon dake cikin falon. 6 pm daidai jirginsu zai tashi.  5:40 ya kammala gaba ɗaya abubuwan da zaiyi,  ɗaukan troly ɗinsa yayi tare da rataya jakarsa akafaɗansa,   yana fitowa daga cikin ɗaki, dai dai lokacin ita kuma tana fitowa daga kitchine, sanye take da riga da wando na pakistan sai kuma hijab dake jikinta.   Idanunsu ne ya sarƙe acikin na juna.  Da sauri ya ɗauke kansa, ya nufi hanyar fita daga cikin  falon, bin bayansa tayi da kallo harya fice daga cikin falon. Samun kanta tayi da kasa ɗauke idanunta daga bakin ƙofar fita daga falon,  komai nasa abun burgewane,   wasu irin hawayene suka cika idanunta, sannan suka samu daman fitowa alokaci guda. Jingina bayanta tayi da jikin bango, tare da ɗan cije laɓɓanta, akullum rayuwarta ta baya, ta zame mata abun tunawa, tunanin babanta ne akullum yake damun zuciyarta,  tayi rayuwa cike da rashin gata da kuma ƴanci, ta taso cikin maraici, sam bata wani san menene daɗin mahaifiya ba, tun tana ƙarama mahaifiyarta ta rasu,  har i'yanzu tana buƙatar sanin wacece ita, gaba ɗaya rayuwar da tayi abaya cike take da duhu,  Maraici, Kaɗaici, da kuma Ƙunci su suka cika rayuwarta ta baya, babu wani wanda ya damu da ita, itake shanye damuwarta komai girmansa, ɗan zamewa tayi ta zauna daɓas akan tiles ɗin dake malale a wajen, lumshe kyawawan idanunta tayi, tare da soma murza ƴan yatsun hanunta.  Ƙamshin turarensa da taji yana shiga hancinta ne, yasanya ta buɗe idanunta da suke cike tab da ƙwalla, ganinshi tayi tsaye akanta ya zuba mata idanunsa masu matuƙar rikitata.  

Saurin ɗauke idanunsa yayi daga kanta, domin bazai taɓa iya juran kallon yanda ƙwayan idanunta ke cike da ƙwalla ba,  envelop ɗin dake hanunsa ya miƙo mata, hanunta na rawa haka ta amshi envelop ɗin, shikuma ya juya ya fita,  samun kanta tayi da kasa buɗe envelop ɗin jiki asanyaye ta koma ɗaki.

6:00 pm daidai jirginsu ya ɗaga zuwa sararin samaniya.  Jingina bayanshi yayi da jikin kujeran da yake zaune, tare da lumshe idanunsa,   wani tunani da yazo ranshi ne yasanyashi sakin murmushi, lokaci guda kuma ya haɗe fuskarsa tare da buɗe idanunsa da sukayi jajur dasu.

*** ***

Wasa wasa har sunyi sati ɗaya da  fara exam, a ɓangaren Ziyada kuwa sai dai muce Alhamdulillah, domin kuwa tana amsa tambayoyin jarabawan da iyakayi mata, da duka iya ƙoƙarinta.

Zaune take a inda aka tanadar musu don cin abinci, kasancewar yau ta riga su Nasmah fitowa daga ɗakin jarabawan, yasa take zaune ita kaɗai,  kanta ta kifa akan ɗan madaidaicin table ɗin dake gabanta wanda yake zagaye da kujeru.

Wani irin ƙamshin turarene yashiga kawowa hancinta Ziyara,    lumshe idanunta tayi tana mai shaƙan ƙamshin turaren batare da ta ɗago kannata ba.

Ahankali ya jawo kujeran dake fuskantar nata ya zauna.  Sexy eyes ɗinsa ya zuba wa ƴan yatsunta dake aje kan table ɗin.  Hakanan taji kamar akwai mutum akusa da ita, saboda hakane yasa ta ɗan ɗago kanta, waro idanunta tayi cike da mamaki, duk da cewa aƴan kwanakinnan yaɗan matsa mata, amma kuma sam bata tsammaci ganinsa a wannan lokacinba.  Murmushi yayi mata tare da ɗage giransa sama.   "Surprise!"  yafaɗa yana me sake ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo.   Kawar da kanta gefe tayi tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.

"Idan kina cikin yanayi na damuwa kinfi kyau, but even at that, i don't want to seeing you in this situation, ki ɗan saki fuskarki kinji ƴan mata na!"  Ya faɗi maganar yana mai langwaɓar da kansa gefe tamkar wani ƙaramin yaro.  Yanayin yanda yayi maganar shine abun daya sanya ta ɗan juyo ta kalleshi,  irin kallon daya keyi mata ne ya sanya taji jikinta yayi sanyi.    Yana shirin sake yi mata magana ne wayarsa ta soma ringing alaman shigowan ƙira.  Ɗaga wayan yayi tare da karawa akan kunnensa, baiwani jima yana wayanba ya kashe, tare da maida wayar cikin aljihunsa. Miƙewa tsaye yayi, tare da ɗan ranƙwafowa dai dai fuskarta.  in a silent voice yace. "Kina da kyau sosai, komai naki me kyau ne, zanyi baƙin ciki idan kika kasance saɓanin tunani na!!"  yana gama faɗin haka ya juya ya soma  tafiya, binsa tayi da kallo har ya ɓacewa ganinta. Dai dai lokacin su Nasmah suka ƙaraso.  Shukrah na zama ta kwashe da dariya.  "Har angama shan love ɗin?" Nasmah tafaɗi haka tana mai ƙoƙarin gumtse dariyarta.
"Love kuma?" Ziyada ta tambaya.
Dariya Shukrah da Nasmah suka sanya tare da tafawa, ganin haka yasa Ziyada ci gaba da sabgoginta, domin ta sansu abu mai sauƙi ne su fassarata da wata manufar.

*** ***
LAGOS NIGERIA.

SOORAJ!!!

1:00 am, ƙarfe ɗaya na dare, kwance yake akan makeken gadonsa, wanda yaji zanin gado na alfarma.  Sanye yake da white pencil jeans ajikinsa,  bai sanya riga ba hakan yasa  gaba ɗaya surar jikinsa take abayyane, musamman ma sick packs ɗinsa, wanda suka samu daman kwantawa raɗau akan fatar cikinsa, sama sama yake jiyo motsin mutane acikin kunnuwansa, ahankali ya buɗe idanunsa, aikuwa nan ya tabbatar da cewa ba karya kunnuwannasa keyi masa ba, tabbas motsin mutanene acikin gidansa, saƙƙowa yayi daga kan gadon tare da nufar ƙofan fita daga cikin ɗakin, ahankali ya murza handle ɗin ƙofar ya fita, taku uku kacal yayi ya samu kanshi a babban falon dake gidan, hanu yasanya akan makunnin ƙwan wutan dake falon ya kunna, kunnawansa yayi daidai da sakar masa bullet da akayi akan ƙirjinsa, wani ƙara yasanya sakamakon wani irin zafi da raɗaɗi da suka ratsa shi, tun daga ƙasan ƙafarsa harzuwa tsakiyar kansa, kafun yayi wani yunƙuri ansake sakar masa wani bullet ɗin akan hannunsa, wani irin azabane yaji yana huda jijiyoyin jikinsa, yana ratsawa ta ƙwaƙwalwarsa, take idanunsa suka soma rufewa, wani irin abu yaji acikin jikinsa wanda bai taɓa jin irinsa ba, take yafaɗi awajen baya ko motsi.

*(Kuyi haƙuri saida na gama typing ya goge gaba ɗaya, da ƙyar nasamu nayi wannan, nasan kuna fushi dani amma dan Allah kuyi haƙuri🙏🏻🙏🏻🙏🏻)*

     *Vote Me On Wattpad*🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

                *SOORAJ*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈Kainuwa Writers Association*
_{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain and motivate he mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

             *WATTPAD*
       @fatymasardauna

#romance

           *Chapter 21*

Jini ne ke fitowa daga jikinsa yana malala akan white tiles ɗin da ya mamaye gaba ɗaya falon.   Wasu ƙattin maza guda biyune suka fito daga maboyarsu, wato bayan labule kenan inda suka ɓoye, ko wannensu fuskarsa sanye take da mask, dukansu suna sanye da baƙaƙen kaya, sannan kuma kowannensu ahanunsa ɗauke take da bindiga, ɗan ranƙwafowa  ɗayan yayi tare da ɗaura hannunsa adai dai saitin hancin Sooraj, jin baya numfashine yasa ya kalli ɗayan ɗan uwannasa.  Alama yayi masa da ido akan su tafi aiki ya kammala,  babu wani ɓata lokaci, aƙagauce suka fice daga gidan..   10 minute da tafiyarsu saiga ƴan sanda har mota biyu.  Alhaji Ilyass (maƙocin Sooraj)  dake laɓe jikin gate ɗin gidansa, yana ganin ƴan sanda ya ƙaraso garesu haryana jin tuntuɓe, aruɗe yace.   "Yauwa ranka ya daɗe kun ƙaraso? Ni ne nan naƙiraku, tabbas naji ƙaran harbin bindiga awannan gidan har sau biyu, saboda haka duk yanda akayi babu lafiya!" yafaɗi haka yana me sharce gumin dake yankowa ta gaban goshinsa, gaba ɗaya atsorace yake, ƙiran ƴan sandan ma da yayi baƙaramin Jahadi yake ganin yayi ba, saboda tsorone cike fal aransa. 

Cike da rashin tsoro haka ƴan sandannan suka rarrabu, kowanne daga cikinsu ya saita kunamar bindigarsa, ƙiris sukejira su saki harsasai,  haka sukayi cikin gidan Sooraj,  ahankali suka tura ƙofar falon suka shiga, ganin bakowa acikin falon yasa suka shiga ƴan dube dube, yayinda wasu daga cikinsu suka nufi bedrooms ɗin dake cikin falon, ɗaya bayan ɗaya haka suka shiga suna dubawa, ɗaya daga cikin ƴan sandan ne idanunsa suka sauƙa akan jinin dake kwance ya daskare akan tiles, jawo ogansu yayi ya nuna masa jinin,  aikuwa suna leƙa bayan kujera sukaga mutum yashe aƙasa, gaba ɗaya jini ya ɓata jikinsa, aɗan razane sukayi kanshi, daidai lokacin sauran ƴan sandan suka dawo cikin falon.   "Sir gaba ɗaya fa mungama duba gidannan bakowa acikinsa" suka faɗa suna mai kallon Sooraj dake yashe aƙasa.   Shiru ogannasu yayi tare da ciro wayarshi acikin aljihunsa ya danna ƙiran asibiti.  Kallon sauran ƴan sandan yayi yace subi hanya duk wanda suka gani sukamashi.  hakan kuwa akayi duk suka watse yazama saura mutane ƴan ƙalilan.  Ƙarar jiniyan ambulance ne yacika gidan.    Ɗaukan Sooraj akayi aka sanyashi acikin ambulance ɗin, suka wuce asibiti.
Babban asibitin dake cikin garin Lagos suka wuce dashi, direct ɗakin bada taimakon gaggawa aka nufa dashi, duk da cewa basu da tabbacin cewa yana da rai ko bayidashi.   Dr. Femus shine mutumin daya fara cire handglobes ɗin dake hanunshi, kallon sauran abokan aikinnasa yayi yace.  "He is dead!"   Jikinsune gaba ɗaya yayi sanyi, saboda haka suma suka soma ƙoƙarin cire handglobes ɗin dake hanunsu.
Chapter 24 · 0% Book details