Sashe 60
Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Cikin tsananin damuwa Mas'oud ke kallon SOORAJ wanda ke zaune agaban dressing mirror yana shafawa jikinsa mai, zallan damuwa Mas'oud ya hango kwance akan fuskar Sooraj, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da duban agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa 9:40 cikin ɗan zaƙuwa yace "9:40 fa RAJ kayi sauri kada mu makara"
Harara Sooraj ya watsa masa tare da cewa "Bayan ka matsamin akan cewa saina bika yanzu kuma mene zaka dameni"
Murmushi kawai Mas'oud yayi tare da cewa "Naji koma me kayi sauri."
Baki Sooraj ya buɗe daniyar yin magana sai kuma tari ya sarƙesa da sauri yasanya handkerchief ya toshe bakinsa gudun kada Mas'oud ya ji sautin tarin har ya lura da jinin dake fita daga bakinsa,  ganin kamar hankalin Mas'oud baya garesa hakan yasa ya goge bakinsa tare da komawa toilet ya wanke bakinsa, da kallo kawai Mas'oud ya bisa don yaga sanda Sooraj yayi saurin goge jinin dake fita a bakinsa, yanasane yayi kamar baigani ba, wani irin tausayin abokinnasa ne yasake lulluɓe zuciyarsa.
Cikin dauriya da danne ciwon dayakeji yasanya tsadaddiyar shaddan da Mas'oud ya kawo masa, riga da wando ne ɗinkin half jumper, sai kuma gare wanda yasha aiki sosai, yana gama sanya kayan ya zura baƙaƙen takalmansa na kamfanin gucci aƙafansa wanda suke da matuƙar tsada, hulansa mai ratsin white and blue yasanya, kasancewar shaddan jikinsa white ce aikinta kuma ya kasance blue, sosai da sosai yayi kyau, yayinda gold wrist watch ɗinsa keta shinning yana ɗauke ido, baƙaramin kyau Sooraj yayi ba, duk da cewa ciwon dake cinsa arai yaɗan bayyana rama kaɗan ajikinsa, saidai kuma ya ƙara fari sosai, sannan kuma ƙawataccen sajen dake kwance akan fuskarsa ya ƙara kwantawa luf akan fuskarsa, Mas'oud da kansa saida ya yaba irin kyawun da Sooraj yayi, wayoyinsa ya ɗauka ya zuba acikin aljihun rigarsa, batare dayacewa Mas'oud ƙalaba ya murɗa handle ɗin ƙofar ya fita. Ganin haka yasanya Mas'oud rufa masa baya.
Cikin wata haɗaɗɗiyar motar SOORAJ ƙiran Buggati suka nufi unguwar Maitama inda anan za'a ɗaura auren.
Haɗaɗɗiyar motartasu ce ta ƙaraso ƙofar gidan yayinda ta ratsa cikin yawan jama'an dake cike a wajen, Mas'oud ne ya fara buɗe murfin motar ya fita, yayinda Kamalu wanda shike driving motar ya zagayo da sauri ya buɗewa Sooraj ƙofar motar, yana fitowa kallo ya dawo kansa domin sosai yayi kyau.  Sam baidamu da kallon da jama'an wajen keyi masa ba, yanufi inda Abbansa yake, kan wata lallausan darduma ya zauna, fuskarsa ɗauke da mamaki yake bin ƴan tsirarun abokansa da yagani awajen da kallo, Mas'oud ne ya zauna akusa dashi tare da dafashi, ɗago da kansa yayi ya kalli Mas'oud, murmushi Mas'oud yayi masa tare da kashe masa ido, sanin iskancin Mas'oud nada yawa yasanyashi kawar da kansa gefe, yanayin hayaniyan da akeyi awajen yasanya har aka gama ɗaurin auren baisani ba, wayarsa dake ta faman ruri ya ciro daga aljihunsa, baikai gayin picking call ɗinba yaji ana shelan cewa an ɗaura auren *SOORAJ MANSOOR MAINASARA da Amaryarsa ZIEYADERH ABUBAKAR* akan sadaki naira dubu ɗari.
ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
Sooraj !!!
Written By
Phatymasardauna
ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
       *SOORAJ !!!*
   *Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
       *WATTPAD*
    @fatymasardauna
#romance
      *Chapter 44*
Ahankali ta buɗe idanunta da sukayi mata matuƙar nauyi ta sauƙesu akan Aunty Muhibbat. Cikin tsananin kulawa Aunty Muhibbat tace "Sannu Zieyaderh tashi kisa kaya sai muje asibiti ko, naji jikin naki yayi zafi sosai!"
Oummu ce tashigo cikin ɗakin fuskarta ɗauke da damuwa, ƙarasowa gaban gadon da Zieyaderh'n ke kwance tayi cike da tausayin Zieyaderh'n tasanya hannunta ta taɓa wuyanta, jin zafi zau ajikinta, yasanya Oummu cikin damuwa sosai tace "Muhibbat sanya mata kaya naƙira Dr.Bashir yana hanya!"
"To" kawai Aunty Muhibbat tace tare da ɗauko wani lallausan arebian gown wanda aka tsara ado me ɗaukar hankali ajikinsa, miƙawa Zieyaderh rigan tayi tare da cewa ta sanya, cikin ɗan kuzarin daya rage mata tasanya rigan wanda yabi gaba ɗaya surar jikinta ya lafe, komawa tayi ta kwanta tana me maida numfashi ahankali, jin kanta take kamar zai rabe biyu.
Blanket Aunty Muhibbat ta rufa mata, inda tabi bayan Oummu suka fice daga cikin É—akin.
Wani irin shock ne yaji ya kama gaba ɗaya illahirin jikinsa, take yaji komai ya tsaya masa cak, yayinda maganan maroƙin ke ƙara yawo acikin kunnuwansa yana me hautsina ƙwaƙwalwa da tunaninsa, dummmm haka yaji acikin kunnuwansa yayinda yaji tamkar an buga masa guduma atsakar kansa, tunani gami da nutsuwarsa ne suka ɗauke gaba ɗaya, haka yazama tamkar wani statue, cikin tsananin farinciki da jin daɗi Mas'oud ya dafa kafaɗunsa tare da cewa.
"Ina matuƙar tayaka murna da farincikin samun Zieyaderh amatsayin mata, Allah ya tayaka riƙo!" Mas'oud ya faɗi maganar yana me ɗan bubbuga kafaɗan SOORAJ wanda har yanzu ya kasa ƙyafta koda idanunsa ne,  fuska ɗauke da tsananin farinciki Almustapha ya ƙaraso inda Sooraj din ke zaune, hug ya basa tare da cewa.
"Happy Married life my brother, am very happy to day!"
Sai alokacin Sooraj ya motsa idanunsa inda yakeyiwa Almustapha wani irin kallo me É—auke da tarin tambayoyi haÉ—i da ma'anoni daban daban.
Ƴan tsirarun abokansa da suka samu daman halartar ɗaurin auren ne suka ƙaraso inda yake, kowanne daga cikinsu bakinsa ɗauke da fatan alkhairi, shidai SOORAJ tamkar wani gunki haka yake binsu da idanu, wani irin gumi ne ke tsatstsafowa ta goshinsa, lokaci guda jikinsa ya soma karkarwa tamkar wanda aka watsawa ruwan sanyi, lura da hakanne yasanya Mas'oud kamo hannunsa suka fice daga cikin taron jama'an dake wajen, kai tsaye mota Mas'oud ya nufa dashi inda ya buɗe gidan baya ya tura Sooraj ɗin aciki kana yamaida murfin ya rufe.
Da Æ™arfi ya rumtse idanunsa yana mejin zuciyarsa na bugawa da Æ™arfi kamar zata faso Æ™irjinshi, wani irin sarawa kansa keyi, yayinda numfashinsa ke seizing yana me Æ™oÆ™arin É—aukewa, hannunsa yakai kan Æ™irjinsa dake masa wani irin Æ™una, idanunsa ne suka kaÉ—a sukai jajur, da Æ™yar ya iya haÉ—iye wani yawu me É—aci wanda ya tsaya amaÆ™oshinsa, jiyake kamar ana watsa masa ruwan zafi akan fatarsa, yanajin kamar yata kurma ihu ko zai samu nutsuwa da salama acikin zuciyarsa, jingina bayansa yayi da jikin kujeran motar tare da cije laɓɓansa, idanunsa da suka kaÉ—a sukai ja kamar garwashin wuta ya lumshe tare da sanya hannuwansa duka biyu ya toshe kunnuwansa dake ta faman amsa masa amo.Â
Cikin mintunan da basu wuce 20 ba Dr.Basheer yasamu daman ƙarasowa cikin gidan, kai tsaye Aunty Muhibbat ce tayi masa jagora zuwa ɗakin Zieyaderh, saboda Oummu na fama da jama'arta.
Akan bedsite Dr.Bashir ya zauna tare da ciro kayan aikinsa ya soma kwada yanayin jikinnata, yana kammalawa ya haɗa wasu allurai guda biyu wanda zaiyi mata, drip ya shiga ƙoƙarin ɗaura mata don ya lura sosai take buƙatan ruwa,  ganin manyan alluran dayake ƙoƙarin yi mata ne yasanya ta rumtse idanunta, cikin fitar hayyaci tare da sambatu irin na zafin zazzaɓi daya sauƙar mata lokaci guda tace. "Banason Allura, wayyo Yaya kazo kafaɗa masa banason allura, banason komai kai kawai nakeso!"
Baki buÉ—e Aunty Muhibbat ta kalli Dr.Bashir,
murmushi Dr.Bashir yayi mata tare da girgiza kansa cikin nutsuwa yace. "Karki damu zafin zazzaɓi ne yasanyata haka amma nanda 1 hour insha Allah zata ji sauƙi!"
Kuka Zieyaderh keyi sosai haka Dr.Bashir yayi mata allura, har ya gama yi mata alluran kuwa bata daina kuka ba,  tun baigama haɗa kayan aikinsa ba wani irin fitinannen bacci ya soma fusgar ta, kasancewar manyan allurai yayi mata masu ƙarfi hakan yasa dole zasu sata bacci, lumshe idanunta wanda sukayi luhu luhu tayi, gaba ɗaya yanayin idanunnata sun sauya, yayinda suka koma kamar na wata wacce ke cikin tsananin maye.
Wata farar takarda Dr.Bashir yabawa Aunty Muhibbat inda yace anemamata magungunan idan tatashi sai abata tasha insha Allah Zata warke, godiya Aunty Muhibbat tayi masa inda daganan yayi musu sallama ya tafi, mintuna 5 kacal da tafiyan Dr.Bashir nannauyan bacci ya ɗauki Zieyaderh, ganin haka yasa Aunty Muhibbat gyara mata kwanciya tare da rufa mata blanket, rage mata gusun a.c tayi kana ta jawo mata ƙofar ɗakin ta fice,  koda ta gayawa Oummu yanda sukayi da Dr.Bashir ƙiran Almustapha Oummu tayi tabashi takardan tare da gaya masa halin da Zieyaderh'n ke ciki.
Idanu Almustapha ya zaro waje cikin damuwa yace "Badai aurenta da SOORAJ ne matsalan ba?"
Kai Oummu ta girgiza masa tare da cewa "Bashi bane, don har yanzun bata sani ba, tunjiya dai take fama da zazzaɓin"
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.
"Allah ya bata lafiya"
Da "Ameen" su duka suka amsa kana ya fice don siyawa Zieyaderh magani.
Acan waje kuwa sannu ahankali jama'a keta watsewa inda kowa ke kama gabansa, Alhaji Mansur ne ya dubi Malam Garba wanda yazo ɗaurin auren dashi da ƴan tsirarun abokansa, cikin kulawa yayi musu iso zuwa cikin katafaren falonsa, shidai Malam Garba gaba ɗaya jinsa yake wani iri, burinsa shine yayi ido huɗu da angon ƴartasa don ya damƙa masa amanarta, saidai kuma yawan jama'an dake wajen yasanya sam baiga angon ba yadaiji wasu nacewa angon yanacikin mota amma dai bai ganshi ba.