Sashe 63
Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Cikin kulawa ta gyara zamanta tare da cewa.
"Duk da wannan bashine karo na farko da muka fara yi maka aure ba, amma inaso kasancewa wannan auren daban yake da sauran, bandamu ba koda zakaji cewa hakan da mukayi rashin kyautawa ne agareka, saidai inason kasan cewa ban taÉ“ajin ina yimaka sha'awar rayuwar aure da wata mace ba kamar Zieyaderh,Â
kamar yanda kaine ka kawota kakuma riƙeta tunkan musan da ita, ayanzuma haka nakeso kacigaba da riƙeta, kai ba ƙaramin yaro bane Sooraj, kamar yanda na gargaɗeka abaya akan sakin aure, to awannan karon ma zan gargaɗeka, Wallahi! Wallahi!! Sooraj idan har ka saki yarinyar nan Zieyaderh kamar yanda kake sakin sauran matan da muke aura ma to tabbas saina tsinemaka!!"
Amatuƙar razane Sooraj yaɗago kansa da idanunsa wanda sukayi jajur ya kalli mahaifiyar tasa, gani yayi sam babu alamar wasa akan fuskarta, sake gyara zama Oummu tayi tare da cewa.
"Kada kaɗauki maganata amazaunin wasa, idan kuma kace bahaka ba lallai zan shayar dakai ruwan mamaki"
Miƙewa tsaye tayi tare da ɗan soma tattakawa har takai bakin steps taɗan tsaya tare da juyowa, dubansa tayi kana tace.
"Bazan baka Æ´ar mutane katafi da ita gidanka ba, dole anan zaku zauna, saboda haka anjima za'a kai maka amaryarka, cikin part É—inka dake gidannan, sannan kuma Wallahi idan ka cutar da ita ban yafe maka ba!"Â Tana gama faÉ—in haka ta juya tare da soma haura steps É—in.
Ahankali Sooraj yaɗago idanunsa wanda suka zama tamkar garwashin wuta yabi bayan mahaifiyar tasa da kallo, ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe tare da lumshe kyawawan idanunsa, jiki asaluɓe haka ya tashi ya bar cikin falon.
Wani irin haɗaɗɗen lace purpule colour mai taushi wanda yaji ɗinkin riga da sket ta sanya, sosai kayan ya zauna ɗas ajikinta, inda farar fatarta ta sake bayyana acikin purpule colour lace ɗin, tsayawa ajikin madubi tayi tare da duban kanta, wani irin kunyane ya kamata sakamakon ganin yanda gaba ɗaya rabin ƙirjinta ya bayyana ta saman wuyar rigar, rumtse idanunta tayi ayayinda taji tsikar jikinta na tashi, sakamakon tunowa da yanda hannayensa suka sauƙa akan naked skin ɗinta da tayi, da sauri ta sanya hannu ta rufe fuskarta, wani irin haushi da kunyan kanta takeji, turo ƙofar ɗakin da akayine ya sanyata shiga cikin nutsuwarta.
Aunty Muhibbat da Bilkh ne suka shigo, ganin yanda tsadadden leshin ya zauna ajikin Zieyaderh yayi mata kyau, yasanya Aunty Muhibbat sakin murmushi tare da cewa.
"Masha Allah!"
Zama tayi akan stull ɗin mirror yayinda Bilkh tashiga aikin tsantsara mata kwalliya akan kyakkyawan fuskarta, duk da cewa bawani uban kwalliya sosai akayi mata ba, amma sosai
tayi kyau, ɗauri mai kyau Bilkh tayi mata tare da yafa mata wani babban mayafi ajikinta wanda yake purpule colour marar nauyi,  sosai Zieyaderh tayi kyau irin mai É—aukar hankalin nan, yayinda oil lipstick É—in da aka shafa mata akan lips É—inta keta shinning.Â
Sooraj kuwa yana fita daga cikin falon na Oummu kai tsaye gaba É—aya gidan ya bari inda ya wuce night club, can yaje suka haÉ—e da Mas'oud.
Ƙarfe 8 daidai Aunty Muhibbat ta kamo hannun Zieyaderh inda ta ƙarasa da ita har gaban Oummu da ke zaune akan kujera.
Hannun Zieyaderh Oummu ta kamo cike da ƙaunar biyayya irin na yarinyar tace.
"Haƙiƙa kamar ƴata dana haifa ta cikina haka nakejinki Zieyaderh, saboda haka zanyi miki duk wani abu irin wanda uwa mahaifiya keyiwa ƴarta".
ÆŠan numfasawa Oummu tayi haÉ—e da cigaba da cewa.
"Idan akace miki zaman aure ba'ana nufin zaman wasa bane, zaman aure bayana nufin zamane da zaki zauna kiyi abun da kikeso ko kuma kiyi duk abun da kikaga dama ba, aduk sanda mace tayi aure to tana zaune ne aƙarƙashin mijinta akuma ƙasan ikonsa, haƙiƙa aure wani babban sinadarin rufin asirine ga kowacce ƴa mace, aure yana ƙarawa mace ƙima da daraja sosai, sannan kuma idan kikaji ance miki zaman aure bawai yana nufin kullum zaman daɗi akeyi ba, kamar yanda harshe da haƙori suke saɓawa awasu lokutan haka ma mata da miji ke saɓawa, wani lokaci harma fiye da haka, saboda haka dole saikinyi haƙuri kin kuma jure daɗi da rashinsa kafun zaman aurenki yayi kyau, sannanne kuma zakici riba, Mijinki tamkar Uba yake agareki saboda haka koda wasa karkiyi ƙoƙarin taka maganarsa, idan yace kiyi koda bakyaso kiyi matuƙar bai saɓawa addini ba, kada ki taɓa tunanin ɗaga muryarki sama akan ta mijinki, sannan kada kitaɓa sanya masa baki idan yana magana, mace tagari mai nutsuwa,hankali, da kuma ilimi bata taɓa ɗaga muryarta sama akan muryar mijinta, sannan kuma bata taɓa tanka masa idan yana magana harsai ya gama, sannan macen da tasan kanta itace macen da ako yaushe take tausasa zuciyar mijinta, idan yana fushi ta rarrashesa, idan tayi masa laifi ta basa haƙuri, haka kuma koda shine yayi mata laifi amma idanunsa suka rufe yake ganin kamar laifinta ne takan kwantar da kanta ƙasa ta bashi haƙuri,  zanji daɗi matuƙa idan kika zamo mace tagari acikin gidan aurenki"
Ajiyar zuciya Oummu ta sauƙe tare da dafa kafaɗan Zieyaderh wacce ke aikin zubar da hawaye, cikin kulawa ta sake cewa.
"Nasan babu soyayya atsakaninki da Sooraj amma har acikin raina ina fata da kwaɗayin ganin ɗorewar zamanku, kada kice don bakyasonshi zaki ƙuntata masa, haka kuma kada kice don baya sonki zaki ƙuntata masa, kada kice don bakwason juna komai ya umarceki da yi bazakiyi ba, kisani dun wani abu dazakiyi masa wanda yakasance ba daidai ba to Allah Bazai barki ba saiya kamaki da laifi, sannan mala'iku zasu rubutamiki zunubi akan duk abun da kika aikata masa wanda yake ba daidai ba, kiyi haƙuri kizauna dashi da daɗi ko babu, sannan kiriƙe muku sirrinku koda wasa kada kitaɓa barin wani yaji sirrinku, kizama mai haƙuri akullum akuma koda yaushe insha Allah Allah Zai zama gatanki ako ina!"
Kuka me ƙarfine ya ƙwacewa Zieyaderh hakan yasa ta kifa kanta ajikin Oummu tashiga rera kukanta, itama Oummu hawayene suka cika idanunta amma saita shanye tare da sakin murmushi, hannu tasanya ta ɗago Zieyaderh tare da share mata hawaye, cikin son ƙarfafa mata guiwa tace.
"Allah yamiki Albarka kema yabaki Æ´aÆ´a masu biyayya!"
Aunty Muhibbat ce tazo ta kama Zieyaderh inda kai tsaye suka wuce ɓangaren SOORAJ wanda aka sake ƙawatasa aka kuma zuba masa sababbin kayan funitures masu kyau da burgewa komai dake cikin falon kalan pitch and milk colour ne, sosai falon yayi kyau, daga gefe guda kuwa one bedroom ne kaɗai acikin falon wanda shima aka ƙawata cikinsa da furnitures light pink da fari, sosai komai yayi kyau, akan haɗaɗɗen gadon dayaji lallausan katifa Aunty Muhibbat ta zaunar da ita, inda ta sanya mayafi ta rufe mata gaɓa ɗaya jikinta,   nan itama tayi mata ɗan taƙaitaccen nasiha, cikin dabara tace mata zataje ta ɗauko wayarta tana zuwa, kai kawai Zieyaderh ta iya jinjina mata alaman to.
Aunty Muhibbat na fita daga cikin É—akin ta saki murmushi, don wayo kawai tayiwa Zieyaderh babu wani wayarta da zata je É—aukowa, tafaÉ—i hakane kawai don tabarta tatafi cikin salama.Â
9:00 pm
Tun tana jiran dawowan Aunty Muhibbat harta gaji, sannu ahankali takejin wani irin bacci na fusgarta, yayinda agefe guda kuwa takejin wani amai da tashin zuciya na taso mata, wani irin luuuuu haka takejin kanta kamar wanda jiri ke shirin kaiwa ƙasa, lumshe idanunta tayi tama mejin wani abu me ɗumi daya fito ajikinta, da sauri ta yaye mayafinta tare da saƙƙowa daga kan gadon, banɗaki ta nufa, inda tana shiga ta sauƙe wani irin ajiyar zuciya don babu makawa tasan cewa period ɗinta ne yazo, mamakine ya cikata ganin cewa wannan karon mara da cikinta basuyi mata ciwo kamar yanda suka saba yi mata aduk lokacin zuwan period ɗinta ba, tsabtace jikinta tayi tafito zuciyarta ɗauke da fargaba, don sam batasan yanda za'ayi ta samu pad ta sanya ajikinta ba, tana fitowa daga cikin toilet ɗin ta jingina bayanta da jikin bango, idanunta ne ya sauƙa akan ƙatuwar trolly ɗinta, wani irin ajiyar zuciya ta sauƙe tare da ƙarasawa gaban trolly ɗin, tana zuge zip ɗin jakan tazaro pad ɗinta tare da komawa cikin bathroom ɗin da sauri, tsabtace jikinta tayi tare da dawowa ta zauna aɗan bakin gadon, takure jikinta waje ɗaya tayi tare da lumshe idanunta,  cikin ƴan mintunan da basu wuce 15 ba bacci ɓarawo ya ɗauketa..