← Book details Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 93

Sashe 37

Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zieyaderh kuwa tana shiga cikin ɗaki ta soma rage kayan jikinta,  towel ta ɗaura aƙirjinta tare da shigewa bathroom,  da ruwa me ɗan ɗumi tayi wanka, take taji gajiyan dake  nannaɗe a muscles ɗinta sun soma warwarewa,   Ko body lotion bata shafa ajikinta ba ta zura wata slim net gown red colour ajikinta, wanda take da guntun hannu, sosai rigan tayi mata kyau,  hasken fatanta yasake bayyana sosai, wani mayafi me shara shara ta ɗauka tayane kanta zuwa ƙirjinta dashi,    ko bedroom slippers bata sanya ba haka ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice,  wani irin yunwane ke ƙwaƙulan cikinta,  kaitsaye dinning area ta nufa, food flask ne masu kyaun gaske jere a kan babban royal table ɗin,  kulan farko data buɗe white rice ne aciki wanda yaji carrot da piece, ɗayan kulan kuwa chicken soup ne wanda za aci shinkafan dashi, su kaɗai ma sun wadaceta hakan yasa bata bubbuɗe sauran food flask ɗin ba,   ɗiban abincin tayi ta sanya a plate, direct kitchine ta wuce don ɗaukan ruwa,   sam bata taɓa tunanin zata tarar da wani acikin kitchine ɗinba kasancewar yanda taji gidan ya ɗauki shiru alamun banda Ummu da ita babu kowa acikin gidan,  bata damu da gyalenta daya zame daga kanta har yayi sanadiyar fito da tsefeffen gashin kanta ba, kasancewar gyalen yana da santsi shiyasa yaketa zamewa ajikinta.  

Tanashiga kitchine ɗin taga baki ɗaya wutan kitchine ɗin akashe suke, abun da bata taɓa gani ba kenan, gashi garin yasoma yin duhu hakan yasa bakomai dake cikin kitchine ɗin take iya gani ba, dayake tasan wajen da makunnan wutan suke sai kawai ta ƙarisa ta kunna wutan, take haske ya mamaye gaba ɗaya kitchine ɗin, bata damu data waiga bayanta ba ta nufi wajen fridge,  buɗe murfin tayi ta ciro bottle water me ɗan sanyi.  Tana juyawa idanunta suka faɗa cikin nashi, take ta sake goran dake  hanunta ya faɗi ƙasa,  buɗe manya manyan idanunta tayi cike da mamaki taɗan kalleshi,   zaune yake akan saman wata ƴar madaidaiciyar drawer, dagashi sai long jeans ba shida ko riga ajikinsa, fresh naked skin ɗinsa sai shining take, wani cup ne riƙe ahanunsa wanda cikinsa ke ɗauke da black coffee, tun shigowarta cikin kitchine ɗin yake kallonta, harzuwa yanzu kuwa bai ɗauke idanunsa akanta ba,  wani irin bugawa taji heart ɗinta nayi amma saita ɗan daure, tsugunawa tayi ta ɗauki goran ruwan tare da miƙewa tsaye, gaba ɗaya a tsarge takejin kanta,      Ahankali ta juya ta nufi hanyar fita daga kitchine ɗin.

Cikin husky voice ɗinsa yace da ita.  "Zoki bani ruwa"

Cak ta tsaya da tafiyan da takeyi tare da juyowa taɗan saci kallonsa, har yanzu bai ɗauke idanunsa  akanta ba,  zuwa tayi ta buɗe firjin tare da ɗauko masa bottle water me sanyi, cikin yanayi naɗan rusunawa ta miƙa masa, idanunsa ne suka sauƙa akan ƙirjinta, da sauri yakawar da kansa gefe tare da taɓe baki, cikin rashin kulawa yace "Ajiye" agefe dashi ta ajiye, cikin sanyin jiki ta juya zata fice daga cikin kitchine ɗin.

"Waye kika ajiye da zai kashe miki wutan da kika kunna?"  ƴajefo mata tambayar yana me jujjuya spoon ɗin dake hanunsa.

Tsayawa tayi daga tafiyan da takeyi tare da juyowa,  jiki asanyaye ta ƙarasa ta kashe makunnin wutan,  tana fita daga cikin kitchine ɗin ta saki wani wawan ajiyan zuciya, tare da ɗaukan plate ɗin abincinta da sauri ta haura sama.    Shikuwa coffee ɗinsa ya cigaba da sha, sam duhun dake cikin kitchine ɗin bai damesa ba, sometimes yafison zama acikin duhu fiye da zama acikin haske.

Aƙasa ta zauna tare da tanƙwashe ƙafafunta, har yanzu ƙirjinta be daina bugawa da ƙarfi ba, hannu tasanya acikin plate ɗin, saidai takasa kai koda loma ɗaya ne na abincin cikin bakinta, gaba ɗaya tayi losing nutsuwarta, ganinsa da tayi yanzu ya matuƙar hautsina tunaninta, ba komai ke ruɗar da ita ba kamar zallan kyau da kwarjininsa, sosai takejin wani iri aduk sanda tayi gamo dashi,  lumshe  kyawawan idanunta tayi tare da jingina bayanta da jikin gado, shock ɗin da ta shiga lokacin da idanunsa ke yawo ajikinta tane, ya shiga yadawo cikin brain ɗinta.
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

           *SOORAJ!!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

             *WATTPAD*
       @fatymasardauna

*Chapter 30*

Haka ta daure ta cuccusa abincin wa cikinta zuciyarta cike da tarin tunani, tana kammalawa tayi sallan magriba, bayan tayi sallan isha ne tabi lafiyan gado, da yake agajiye takejin kanta take bacci ɓarawo ya ɗauketa.

_SOORAJ_

Yana gama sipping black coffee tea ɗinsa, ya aje cup ɗin tare da miƙewa tsaye ya fice daga cikin kitchine ɗin,  direct ɗakinsa ya wuce, toilet yafara shiga yayi wanka sannan ya ɗauro alwala,  wata blue t-shirt ya sanya kana ya wuce masallaci. 
Bashi yadawo gidan ba sai ten pm dai dai,  wanka ya sakeyi sannan yafito ɗaure da towel a weast ɗinshi,       ɗan ƙaramin towel ya ɗauka agaban dressing mirror ya shiga goge kansa,  duk da cewa bai shafa turare ba amma gaba ɗaya ƙamshin sabulun da yayi wanka dashi ya cika ɗakin,   wani body lotion wanda baya kama jiki sosai ya shafa ajikinsa,  turarensa me sanyin ƙamshi  ya ɗauka tare da fesawa,  cumb ya ɗauka ya  taje kwantacciyar sajen dake kan fuskarsa,  ɗan kallon kansa yayi amadubi lokaci guda kuma ya kawar da kansa gefe, pink lips ɗinsa ya ɗan ciza, wani tunanine yazo ransa hakan yasanyashi sakin murmushin daya bayyana zallan Kyawunsa, shi kansa baisan da yayi murmushin ba,  direct gaban drawer ɗinsa ya nufa tare da zaro kayan dazai sa, riga da wando  na black jeans ya sanya ajikinsa wanda sukayi matuƙar yi masa kyau,   White kambas masu kyau yasanya aƙafafunsa, tare da ɗaura hulan white facing cap akansa, sosae da sosae yayi kyau harma baka iya tantance kammaninsa saboda yanda hulan ta ɓoye fuskarsa,  wayoyinsa ya ɗauka tare da ɗaukan car key ɗinsa,  yana fita daga cikin ɗakin ya murzawa ƙofar key tare da tura key din cikin aljihun wandonsa,   koda ya fito ko ina dake cikin gidan ya ɗauki shiru, direct parking space ya nufa,  mota ƙiran kia  yashiga tare dayi mata key,   koda ya iso bakin gate taradda Maigadi yayi yana ta zuba gyangyaɗi, wani silent horn ya danna, take maigadi yatashi a zabure, cikin daburcewa ya wangale masa gate ɗin,   ba ɓata lokaci Sooraj ya cilla hancin motar sa waje,    kasancewar dare ne hakan yasa babu wani hayaniya sosai akan tituna, tuƙi yake cike da nutsuwa yayinda ya saƙala earpiece akunnensa. 
Duk da sanyin AC'n dake tashi acikin motar hakan bai hanasa sauƙe glass ɗin window ba, wani irin ni'imtaccen sanyine ke ratsa jikinsa wanda har ma yafi na AC daɗi. 
    
TRANSCOP HILTON.

Wangale masa makeken gate ɗin akayi, asukwane ya tura hancin motarsa cikin ƙawataccen compound ɗin hotel ɗin,   ababban parking space ɗin hotel ɗin yayi parking motarsa.  

Ahankali ya zuro da ƙafafunsa waje, cikin takunsa me ɗauke da nutsuwa haka ya nufi cikin hotel ɗin, direct babban ɗakin da zasu gudanar dawani important meeting ya nufa,  gaba ɗaya kowa da kowa sun hallara shi kaɗai kawai ake jira, kasancewar shine jagoran meeting ɗin shiyasa basu fara ba dole saida suka jira yazo,  aƙalla sun ɗauki sama da 1 hour suna tattauna maganganu wanda gaba ɗaya su yasu suke abunsu, Sooraj kam maganarsa bata wuce "Eh" ko "A'a" Ko kaɗan basu wani damuba domin dama acikinsu babu wanda baisan halinsa ba, 11:30 pm daidai suka kammala meeting ɗin, kowa ya kama gabansa,  koda ya baro Transcop Hilton baikoma gidansu ba, direct gidansa ya wuce kasancewar gobe zai koma bakin aikinsa na Bank.

Washegari.

Kamar koda yaushe 7:15 daidai take kammala shirinta na zuwa makaranta, yauma hakance ta kasance domin tuni ta shirya kanta cikin uniform ɗinta,  school bag ɗinta ta ɗauka agurguje tafice daga cikin ɗakin,  bata tarar da kowa acikin falonba gashi har 7:30 takusa sam kuma bataso tamakara,  buɗe ƙofar falon tayi ta fice,  Kamalu driver ta iske tsaye yana jiranta, tana shiga cikin motar yaja suka tafi.
***
Tun 7 daidai yagama shirya kansa cikin wani tsadadden maroon colour suit and white long sleeve shirt, sosai yayi kyau acikin suit ɗin, wani dark maroon toms ƙiran company'n Italy yasanya aƙafafunsa, sosai kwalliyan nasa ya sake ƙawata. Agogon rolex ne ɗaure a tsintsiyar hanunsa, gaba ɗaya gashin kansa sai shining yake yana ɗauke ido, saboda sosai yasha gyara,   kamar wanda akawa ɓarin turare ajiki haka yake tashin ƙamshi,  sabuwar   black car ɗinsa mercedes benz yashiga,  direct bank ɗinsu ya nufa,   tun fitowarsa daga cikin mota mutane keta kawo masa gaisuwa, sama sama yake amsasu yana wucewa,   koda yakai office ɗinsa ya samu komai nead, dama kowa yasan bayason ƙazanta shiyasa always ake tsabtace masa office ɗinsa, sosai yatarar da aiki na jiransa saboda haka tunda yaje bai wani huta ba aiki kawai yaketayi a computer.

_Zieyaderh_

Tun fitowansu break take jin kanta wani iri, ga wani amai da tashin zuciya dake damunta, haka dae tayi break adaddafe suka koma class, duk su Nasmah na lure da ita, saboda ko magana sosai yau din batayi,   ƙarfe 1 daidai aka fito dasu sallah, zuwa lokacin abun yasoma fin ƙarfin tunanin Zieyaderh, saboda ciwon sosai ya tsananta, gawani irin zazzaɓi daya rufeta, koda ta idar da sallah  cusa kanta tayi tsakankanun cinyoyinta ta saki kuka me sauti, don bazata iya jurewa ba, sosai mararta ke murɗawa, gawani sabon ciwon ciki me tsananin azaba da takeji,  ganin irin yanda take kuka yasa Nasma da Shukra kamata suka fice daga cikin masallacin, aƙasan wata bishiya suka zauna su dukansu, cike da kulawa haɗi da damuwa Nasmah ta dubi Shukhra wacce idanunta sukayi raurau alaman itama kuka takesonyi. "Ki kula da ita Shukhra banaje na faɗawa discipline master, nasan zai faɗawa principal!"   kae kawai Shukhra ta iya kaɗa mata alamar taji, saboda itama zuciyarta cike take da rauni haɗi da tausayin halin da Zieyaderh ke ciki, don zuwa yanzu numfashinta har seizing yake kamar zai ɗauke,

Sauri Nasmah keyi don taga ta isa office ɗin discipline master, kamar daga sama taji anƙira sunanta.
Chapter 37 · 0% Book details