← Book details Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 93

Sashe 59

Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau yakama saura kwana huÉ—u biki inda yaune kuma su Zieyaderh suka fara zana jarabawarsu na first term, wanda kuma ita bata samu daman zuwa ba, saidai kamar yanda Oummu ta faÉ—a ansamo wata É—aliba ta musamman tana zana mata jarrabawar.
Ɓangaren gyaran jikinta kuwa komai yana tafiya daidai, dok sosai gyaran da akayi mata ya bayyana ajikinta, duk inda ta zauna saita raba tsaraban ƙamshi,  baƙaramin sauyi takeji ajikinta ba, lokaci ɗaya ta zama wata babbar yarinya kuma cikakkiyar mace.
Kayanta take haɗawa acikin trolly ɗinta, kasancewar yau zata koma gida don sun kammala duk wani gyare gyaren su, wasu ingantattun magunguna haɗi da turaruka Hajiya Arabi ta bata, sannan musamman ta bata wasu turaruka kala biyu tace kada tayi amfani dasu sai bayan anɗaura auren tana shafasu idan zata kwanta, godiya tayi mata sosai, kana tayiwa su Nina da kuma Humaira sallama, kasancewar su ba aranar zasu tafi ba sai washe gari, inda suɗinma dukansu aure zasuyi, exchenging phone number sukayi, daganan ta ɗauki trollynta tafice daga cikin ɗakin.   Cikin nutsuwa tafito compound ɗin gidan tafiya takeyi me ɗaukar hankali yayinda take ta walwali tamkar wata tauraruwa.
duk atunaninta Kamalu ne zaizo ɗaukarta amma saitaga saɓanin haka don Almustapha ta tarar tsaye ajikin mota yana jiranta, tun fitowarta da yayi mata kallo ɗaya ya kau da kansa gefe, baƙaramin kyau da cika ta ƙara ba hakan yasa bazai iya jure kallonta ba, daddaɗan ƙamshin turarenta ne yafara kawowa hancinsa ziyara hakan ne yabashi daman gane cewa taƙaraso garesa, cikin zazzaƙan muryarta tace dashi.
"Ina wuni"
Kansa ya É—ago tare da sakin murmushi cikin kulawa yace "Lapia lau amaryata!"
Ƙasa ƙasa ta hararesa tare da murgaɗa masa baki,  dariya kawai yayi kana ya karɓi jakan hannunta, gidan baya ya buɗe ya ajiye jakannata ,  zagayawa yayi yashiga ɓangaren driver ita kuma tashiga gefen me zaman banza,  tafiya suke babu wanda yace da ɗan uwansa wani abu, gaba ɗaya hankalinta naga wayanta inda take chatting da Shukra wanda ketayi mata tsiya, shikuwa Almustapha gudu kawai yaketa shararawa akan babban titin, sosai ƙamshinta ke taɓasa hakanne ma yasanya yaketa sauri don yakaita gida, gudun kada daddaɗan ƙamshinta ya hautsina masa lissafi.  Ababban haraban gidan yayi parking motar, kamar dama jira take da sauri ta buɗe murfin motar ta fita, trolly ɗinta ta ɗauka kana ta shige cikin gida. Mutane tasamu sosai acikin babban falon na Oummu, kasancewar sunyi nisa acikin hidiman da sukeyi yasanya saɗaf saɗaf  ta haye sama, batare da kowa ya ganta ba, kaitsaye  ɗakin Oummu ta nufa,  da sallama ɗauke abakinta ta shiga cikin ɗakin nan ta iske Oummu da Aunty Muhibbat da kuma Aunty Laylerh,  cike da girmamawa ta gaidasu, cikin so da ƙauna suka amsa mata, inda dukansu suka yaba da gyaran Hajiya Arabi don sosai Zieyaderh taƙara kyau, daga ɗakin Oummu ɗakinta ta wuce, nan ta rage kayan jikinta ta kwanta wayarta ta ɗauka ta shiga IG kasancewar yana ɗebe mata kewa sosai.

Washegari.
Yau takama thursday  kuma yaune za'a gudanar da henna day, tun safe gidan yake ɗinke da ƴan uwan Oummu dana Abba, yayinda aka ɗauko ƙwararrun masu zanen lalle daga maiduguri wanda zasuyiwa Amarya Zieyaderh zanen lalle na musamman,  su Nasmah da Shukra ma sunzo wanda bayan sungama zana exam ɗinsu na yau ɗinne suka biyo ta gidan,  zuwansu yasanya damuwan da take ciki yaɗan gushe, don sun ɗebe mata kewa sosai,  har kusan ƙarfe 3 na yammaci sannan aka gamawa Amarya Zieyaderh zanen lallenta wanda ya matuƙar yiwa fatarta kyau, kasancewarta fara sosai hakan yasa jan lallen ya kama farar fatar jikinta ya zauna raɗau har wani maroon colour yayi,   masha Allah Zieyaderh tazama tamkar wata sarauniya banda walwali ba abun da takeyi,  sai wajen ƙarfe 6 na yammaci sannan su Shukra suka soma shirin tafiya gida, Oummu da kanta tasanya Kamalu driver ya maida kowaccensu gida.

Friday.
Tun ƙarfe 6 Aunty Muhibbat ta tasheta inda tanayin breakfast suka wuce shagon saloon,  gyaran gashi akayi mata mai kyau, daganan wani ƙaton mall suka wuce, Aunty Muhibbat ne tayi sayayya sannan suka dawo gida, kasancewar yau da yamma ƙarfe 4 za a gudanar da walima. Tun ƙarfe 2 Bilkh tazo don shirya amarya,  kafun ƙarfe uku tuni Bilkh ta tsantsara mata kwalliya akan fuskarta,  Aunty Muhibbat da kanta ta shiryata cikin wani irin tsadadden lace mai kalan fari da ratsin sky blue, wanda yaji ɗinkin riga da sket 12 pieces, sosai lace ɗin ya amshi jikinta,  wani haɗaɗɗen sky blue material sari Aunty Muhibbat ta naɗa mata akan kayan, wanda yaƙara bayyana kyawun kwalliyan nata, daga kan ɗan kunne zuwa dan ƙareren sarƙan dake wuyanta har izuwa awarwaro da zoben hannunta gaba ki ɗaya na gold ne, masha Allah Amarya Zieyaderh kam taji kyau harma tagaji da haɗuwa, kowa ya ganta sai yayi santin kyawun da tayi, haka Bilkh da Aunty Muhibbat suka dinga ɗaukarta hotuna, Bilkh kuwa har ma da vedio tayi mata ta ɗaura akan shafinta na Instagram.  Ƙarfe huɗu daidai aka soma ƙoƙarin tafiya da ita wajen walima, adai dai lokacin su Nasmah suka ƙaraso sun sha kyau ita da Shukra inda sukayi ado cikin wasu tsadaddun dogayen riguna masu kyau.   Tsala tsalan motoci aka tanada na musamman don zuwa walima, cikin wata haɗaɗɗiyar mota ƙiran ferarri aka sanya amarya ita da su Shukra tare da Aunty Muhibbat.  Ajere motocin da suka cimma guda talatin kebin dogon titin suna tafiya cikin nutsuwa ahaka har suka ƙarasa babban katafaren hall ɗin da za'a gudanar da waliman, Aunty Muhibbat da Shukra ne suka riƙo amarya aka shigo da ita cikin taron jama'an, nan fa kowa yafara ambatan masha Allah, don dayawansu basu san amaryar ba sai aranan, kowa ya yaba da tsananin kyawunta.
Walima aka gabatar mai rai da lafiya yayinda aka gudanar da wa'azi mai ratsa jiki da zuciya akan zaman aure, sosai wa'azin ya ratsa zuciyar Zieyaderh har batasan sanda hawaye suka fito daga cikin idanunta ba, wanda ita kanta batasan mene dalilin fitar hawayen ba, anci ansha sosai awajen waliman yayinda aka raba kyaututtuka, duk wanda yazo waliman sai da yasamu kyautar Sallaya da kuma al'ƙur'ani izu sittin,  bayan an kammala walima ne kuma aka shiga ɗaukan hoto,   abu dai yayi daɗi saidai ace masha.
Tun ahanyar dawowansu gida wani irin zazzaɓi ya rufe Zieyaderh, wanda har saida Aunty Muhibbat ta lura da hakan,  koda suka koma gida Aunty Muhibbat da kanta ta haɗa mata ruwan wanka,  tana fitowa awanka ta zura wata riga marar nauyi, sallah tayi sannan ta kwanta bayan tasha maganin da Aunty Muhibbat takawo mata, lulluɓa tayi da blanket tare da matse jikinta waje ɗaya.

6:00 pm daidai jirginsu ya sauƙa ababban airport ɗin dake cikin garin abuja Nnmdi Azikwe International Airport.
Ahankali yake sauƙowa daga kan matattakalan jirgin, sanye yake  da white pencil  jeans and white t-shirt, sai kuma wata jibgegiyar rigan sanyi daya ɗaura akan rigannasa wanda take da kalan maroon, white facing cap ne akansa wanda hakan yasanya ba a iya ganin fuskarsa sosai,   yana gama sauƙowa daga kan step ɗin cikin sauri Kamalu driver ya ƙaraso tare da karɓan ƴar ƙaraman jakan dake hannunsa, tare da yi masa sannu da dawowa..    Kaitsaye gidansa ya wuce, don bayason kowa yasan da dawowarsa,  yana shiga cikin tamfatsetsen ɗakinsa ya kashe wuta, tare da cire kayan jikinsa dogon wandonsa kawai ya bari, kwanciya yayi luf akan gadonsa tare da lulluɓa da blanket, awahalce yake maida numfashi yana me ƙara takure kansa waje ɗaya, sannu ahankali zafin zazzaɓin dake jikinsa ke ƙara hauhawa.

1:00 am daidai awannan lokacin cikin kaso 90 na mutane suna bacci, kasancewar dare yakasance mahutar bawa, saidai saɓanin haka ne yakasance daga ɓangarenta don kuwa sam bacci ƴaƙi zuwa idanunta awannan dare, kuka take ƙasa ƙasa hadda sheshsheƙa wanda hakan ya haifarmata da ciwon kai, zafin zazzaɓin jikintane ya ƙara hawa hakan yasa gaba ɗaya jikinta ya ɗauki masassara, kuka take sosai, wani irin faɗuwar gaba takeji na musamman idan ta tuna da cewa gobe za'a ɗaura mata aure, tanaji ajikinta tamkar wani abu zai faru da ita. Haka takwana acikin matsanancin zazzaɓi da ciwon kai sai wajen ƙarfe huɗu na asuba sannan tasamu bacci ɓarawo ya ɗauketa. 

Wayewar garin yau yakasance rana ta musamman awajen ahalin Sooraj don kuwa yau tun safe suke cike da farin ciki, yayinda gidan kota ina ke cike da ƴan uwa da kuma abokan arziki. 
Ƙarfe takwas daidai tasoma yunƙurin buɗe gajiyayyun idanunta ahankali, har yanzu akwai zazzaɓi ajikinta, cikin dauriya ta jingina bayanta da saman gadon tare da rumtse idanunta, Aunty Muhibbat ce taturo ƙofar ɗakin  tashigo, ganin Zieyaderh'n da tayi azaune yasa ta ƙaraso da sauri cikeda kulawa tace.
"Kintashi ya jikin naki?"

"Da sauƙi!" tafaɗa asanyaye tana me karyar da kanta gefe,   Hannu Aunty Muhibbat takai ta taɓa wuyanta, zafi zau taji hakan yasa tace "Subahanallahi har yanzu zazzaɓin bai sauƙa ba, muje kiyi wanka sai kiyi break kisha magani!" 
Da taimakon Aunty Muhibbat ta sauƙo daga kan gadon, har toilet Aunty Muhibbat ta kaita tare da haɗa mata ruwan wanka. 

9:30 am tuni ƙofar gidan ya ɗinke da mutane manya manyan ƴan siyasa da masu muƙami harma da masu sarauta da ƴan kasuwa, kowa kagani fuskarsa ɗauke take da murmushi, Abba wanda yake cikin tawagarsa kallo ɗaya zakayi masa kafahimci cewa yana cikin farinciki,  can na hango Almustapha wanda yasha ado cikin wata blue ɗin shadda riga da wando tare da babban riga, sosai yayi kyau shima fuskarsa ƙunshe take da murmushi, duk bayan minti ɗaya yake kai dubansa zuwa ga agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa.
Chapter 59 · 0% Book details