← Book details Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 93

Sashe 64

Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

11:00 pm.
Dai dai motarsa tashigo cikin harabar gidan, yana gama daidaita parking ɗin motar a parking lot, ya buɗe murfin motar ya fito tare da sawa motar tasa key, ahankali yake tafiya har ya shigo cikin babban falon gidan, duhune gaba ɗaya ya mamaye falon yayinda ko ina ya ɗauki shiru, kaitsaye ƙofar da zata sadashi da ɓangarensa ya buɗe ya shiga, direct bedroom ya nufa, ahankali ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, yana shiga ya maida kofan ya rufe tare da murza mata key, yana juyowa idanunsa suka sauƙa akanta, kwance take tana bacci abaki bakin gado yayinda ta duƙunƙune jikinta waje ɗaya, dagani kai kasan bata shiryawa baccin ba ya ɗauketa, wani irin duka ƙirjinsa yayi ahankali ya lumshe idanunsa tare da jingina bayansa da jikin ƙofar ɗakin, wata irin ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ware idanunsa ahankali ya kuma sauƙesu akanta, sam yama manta da batun kawota ɗakinsa da Oummu tayi masa ɗazun, sama da minti goma ya ɗauka yana kallon yanda ta nannaɗe jikinta waje ɗaya, sake lumshe idanunsa wanda sukai ja yayi tare da ɗan cizon laɓɓansa, sam baiso ace ƙaddaransa ta shafeta ba, sai yanzu yafahimci dalilin dayasa wasu lokuta takan tsaya masa azuciyarsa, saiyanzu kuma yagane cewa zanen ƙaddaranta ne shumfuɗe azuciyarsa, maganganun da Oummu tayi masa ɗazunne suka shiga dawowa cikin kunnensa filla filla, ahankali ya raba bayansa da jikin ƙofan tare da ƙarasowa cikin ɗakin, kayan jikinsa ya soma ragewa yayinda ya cire rigar dake jikinsa, bathroom ya wuce inda ya sakarwa kansa shower, yajima atsaye ruwa na dukan jikinsa, ahankali wata irin nutsuwa ke sauƙar masa, yana gama wankan yayi alwala kana ya fito daga cikin toilet ɗin, kaitsaye gaban ƙaton sif ɗin kayansa ya nufa, wani dogon wandon jeans ya sanya, tare da barin murɗaɗɗiyar surar jikinsa awaje batare daya sanya riga ba, wani farin towel ya ɗauka yashiga goge kansa dake jiƙe da ruwa, yana kammalawa ya feshe gaba ɗaya jikinsa da daddaɗan turarensa mai sanya nutsuwa, kashe gaba ɗaya makunnan wutan ɗakin yayi, kan wata doguwar kujera dake cikin ɗakin ya nufa, kwanciya irinta ruf da ciki yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, gajiyayyun idanunsa ya lumshe yana me fitar da numfashi ahankali, kasancewar amatuƙar gajiye yake hakan yasa mintuna ƙalilan bacci ya ɗaukesa.

2:00 pm sosai take ta faman juyi akan gadon hannunta dafe da mararta dake tsananin ciwo, tamkar acikin mafarki haka takejin wani irin azababben ciwon mara na damunta, cikin tsananin wahala ta buɗe idanunta wanda lokaci ɗaya suka ƙanƙance saboda tsabar wahala, wani ɗan ƙara tasake sakamakon wani irin murɗawa da mararta tayi, lokaci guda ciwon ya tsananta fiye da wanda takeji acikin bacci, duk da sanyin ac'n da yacika gaba ɗaya ɗakin hakan bai hana jikinta fitar da gumin wahala ba, cikin matuƙar tsoro daya kamata da kuma zafin ciwo tasaki wani irin kuka, sosai jikinta ke karkarwa gashi ɗakin gaba ɗaya gauraye yake da duhu, wani irin murɗawa da mararta tayine yasanyata yin wani irin juyi, haka tafaɗo har ƙasa da ga kan gadon, wani irin sabon kuka tasanya yayinda ta dafe mararta da takejinta kamar zata tarwatse.

Ahankali sautin sheshsheƙan kuka ke ratsa cikin kunnuwansa, tun yanajin abun kamar amafarki har ya soma jiyosu raɗau acikin kunnuwansa, ahankali ya ware idanunsa dake cike da bacci, shiru yayi yana mejin sautin kukan nata na ratsa ko ina dake cikin ɗakin, cikin ɓacin rai ya rumtse idanunsa, sam shikam baisani ba ko aljanune da ita wanda ke sata kuka tsakiyan dare, don wannan bashine karo na farko da kukanta ke tashinsa abacci ba, cikin takaici yagyara kwanciyarsa tare da maida idanunsa ya rufe.
Ita kuwa Zieyaderh ciwon mararne ke sake cin ƙarfinta hakan yasa taci gaba da rera kukanta cikin fitar hayyaci, duk yanda yaso ya manta da ita yayi baccinsa hakan ya faskara domin kuwa jin kukannata yake har acikin ƙahon zuciyarsa, tsuka yayi tare da buɗe idanunsa, hannunsa yakai saman kujeran dayake kai, wani ɗan madanni ya danna take wani blue ɗin haske ya gauraye ɗakin, idanunsa ya sauƙe akanta, har yanzu kwance take aƙasa tana ta murƙususu, gaba ɗaya ta birkita kanta, tuni ɗan kwalin dake kanta ya kama gabansa, ahankali ya aje ƙafafunsa aƙasa tare da miƙewa tsaye, cikin takunsa mai ɗauke da nutsuwa ya ƙarasa gareta, tsayawa yayi akanta yana me kallon yanda take kuka tsakaninta da Allah hannunta dafe da mararta, ahankali yaɗan sunkuyo cikin ƙosawa daji kukan nata yace.
"Waike bakida lokacin yin kukane sai tsakiyar dare? zaki tashi daga ƙasannan ne ko saina ɓaɓɓala miki waƴannan siraran ƙafafunnaki?"

Cikin tsananin ciwon dake addabarta taji muryarsa na ratsa kunnuwanta, saidai ko kaɗan taba fahimci abun dayake faɗa ba, don zuwa yanzu tafara fita hayyacinta, ganin yanda taketa faman neman shigewa ƙarƙashin gado yasanyashi sanya hannayensa ya riƙe waist ɗinsa, idanunsa ya tsura mata tare da ɗan cije laɓɓansa, itakuwa Zieyaderh sam batasan metakeyi ba, hakan yasa taketa ƙara shigewa cikin lungun gadon tana sakin wani irin gurnanin kuka, ahankali ya durƙusa agabanta tare da sanya hannunsa ya kamo arm ɗinta, jin shi akusa da ita yasanyata kai hannunta ta kamo damtsen hannunsa cikin tsananin azaban da takeji tashiga yaƙushinsa akan murɗaɗɗun muscles ɗinsa, rumtse idanunsa yayi yana mejin zafin yanda take yaƙushin fatar jikinsa, hannayensa yakai ya tattara gaba ɗaya gashinta dake watse kan tiles, ɗagota jikinsa yayi tare da matseta aƙirjinsa, saboda ya lura sosai zafin ciwon ke ƙoƙarin gusar da nutsuwarta, duk da cewa bata cikin hayyacinta amma hakan baihanata sauƙe ajiyar zuciya ba alokacin da taji sauƙar kanta acikin ƙirjinsa,kuka take sosai tana ƙara shigewa jikinsa, yayinda tasake riƙesa ƙamƙam tana me jujjuya kanta acikin faffaɗan ƙirjinsa, wani iri yakeji acikin zuciyarsa, sam bayason jin kukanta, cikin dauriya da jarumtar daya arowa kansa yakai hannunsa dake rawa kan bayanta, ahankali ya ɗanyi ƙasa da zip ɗin rigar dake jikinta, still hannunsa na rawa haka ya taɓa naked skin ɗinta, rumtse idanunsa yayi ƙam kana yasoma yawo da hannun nasa akan fatar bayanta, ahankali yake shafa skin ɗinta, sama da mintuna 20 suka ɗauka ahaka harzuwa wannan lokacin baidaina shafa fatar bayanta ba, sannan kuma harzuwa wannan lokacin bai buɗe idanunsa da suke kulle ƙam ba, ahankali sautin kukannata ke raguwa sai sheshsheƙanta dake tashi kaɗan kaɗan, kukannata ne ya ɗauke gaba ɗaya alokacin da tasamu relief daga menstrual pain ɗin dake damunta, cikin tsananin galabaita da tayi, ta ƙara gyara kwanciyarta akan faffaɗan jikinsa, karo nafarko kenan arayuwarta data fara ajiye kanta acikin ƙirjin wani ɗa namiji, haka shima karo nafarko arayuwarsa daya fara ajiye wata mace acikin jikinsa, sannu ahankali numfashinta ya daidaita yayinda wani irin bacci me daɗin gaske yasoma ƙoƙarin fusganta, hucin numfashinta dake sauƙa akan ƙirjinsa shine abundaya sanyashi buɗe idanunsa ahankali, wata irin ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ɗan matsawa ya jingina bayansa da jikin gado inda ya tanƙwashe ƙafafunsa, ahankali yasoma ƙoƙarin cireta daga jikinsa, cikin magagin baccinta da baiyi nisa ba tabuɗe baki tare da sakin wani sabon kuka, duk wannan abun da takeyi sam bata cikin nutsuwarta don batasan metakeyi ba, sake ƙanƙamesa tayi ƙam tare da cusa fuskarta acikin ƙirjinsa hartakai tausassun laɓɓanta na gogan kan nipple ɗinsa, lumshe idanunsa yayi tare da ɗan jingina kansa da gadon, wani irin sarawa yakejin kansa nayi masa, yayinda yakejin wani irin bacci na fusgar idanunsa, sannu ahankali gaba ɗaya jikinta ya jiƙe da wani irin gumi, duk da cewa sanyin ac ya wadata ɗakin, cikin yanayi na gajiyawa haɗi da bacci ya sanya hannayensa yaƙarisa zuge mata zip ɗin rigar dake jikinta, kansa ya ɗaura adaidai kafaɗanta wanda hakan yasata sauƙe wani irin ajiyar zuciya badon komai ba saidon sauƙar da lallausan sajen sa da yayi akan fatar wuyanta, ahankali yake hura mata iskan bakinsa akan wuyanta, sakamakon haka wani irin sanyi ne taji na ratsa gaba ɗaya ilahirin jikinta, sannu ahankali jikinta ya sake alaman baccinta yayi nisa, yanda numfashinta ke sauƙa akan chest ɗinsa yasanya shi lumshe idanunsa wanda suke cike da bacci, 10 minute kacal bacci ɓarawo ya ɗaukesa yana me zaune akan ƙafafunsa yayinda ita kuma Zieyaderh ke kwance ajikinsa.

(Naji wasu sunacewa har yanzun waisu basusan mene ke damun SOORAJ ba, nayi mamaki ƙwarai don dai nasan tun a pages ɗin baya da suka wuce nafaɗi matsalarsa, nafaɗi matsalan RAJ ne acikin hikima tayanda duk wanda yake nazartan labarin to cikin sauƙi zai iya gano menene matsalarsa, amma wasu sam sun kasa fahimta, to kamar yanda kukeson ji shine SOORAJ namijine amma bashida cikakikkiyar lafiya idan nace bashida cikakkiyar lafiya bawai ina nufin fever ko headache ne ke damunsa ba, a'a ina nufin shiba cikakken namiji bane kamar yanda wasu maza suke, sam shi bayajin sha'awa kamar yanda wasu daga cikin mutane keji, haka kuma bashi da ingantaccen lafiyar da zai iyayin sex da mace, saura kuma wasu suƙara cemin basu san mene matsalan SOORAJ ba🙄)

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

           *SOORAJ !!!*

    *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

             *WATTPAD*
        @fatymasardauna
#romance

             *Chapter 45*
Chapter 64 · 0% Book details