← Book details Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 93

Sashe 33

Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Tafaɗa abayyane cikin wata irin murya me sanyi. "Ko abacci ma kyau yakeyi, shi komai nasa me kyau ne!!!"  Tasake faɗa  tana me murza ƴan yatsun hanunta, itakanta batasan maganganun da take faɗa suna fitowa fili ba, gaba ɗaya ashagalce take,   fararen ƙafafunta ta zuro ƙasa tare da tashi tsaye, direct wajen window ta nufa,  ɗan yaye labulen window'n tayi tare da soma bin ko ina dake cikin compound ɗin gidan da kallo,   idanunta ta tsayar asetin ƙofar shiga garden ɗin, dai dai lokacin yafito daga cikin garden ɗin hanunsa riƙe da wani green apple,   tafiya yake kansa tsaye yayinda skin ɗinsa keta walwali kallo ɗaya zaka masa kasan hutu da kudi sun zauna masa,  tundaga wajen da take tana iya hango yanda tarin suman dake kansa ke sheƙi, gashi ya kwanta luf luf tamkar sajen dake kwance akan fuskarsa,   bata taɓa ganin wani irinsa ba, shi na dabanne ko acikin maza, hannunta takai ta dafa glass din dake jikin window'n,  fuskarsa kawai take kallo,  akullum tana mamakin yanda yake rayuwarsa babu annuri akan fuskarsa, koda yaushe haka yake baka taɓa ganin dariyarsa, kafun kaji  maganarsa ma wahala ne, shi komai nasa is difference,   Maganan aurensa ne ya faɗo mata lokaci guda ta marerece fuska tare da ɗan taɓe soft lips ɗinta.    "Wace zata aureshi?" tambayar da tayiwa kanta kenan azuci, amma sam batasani ba har sautin maganan yafito fili.  Soft lip ɗinta na ƙasa taɗan tsotsa tare da soma karyar da yatsun hanunta, idanunta ne sukayi raurau kamar wacce zatayi kuka, ɗago kanta tasakeyi da niyan kallonsa, amma kuma saitaga kome kama dashi babu awajen, sake labulen tayi tare dakomawa kan gado ta zauna.  "Mene nawa? Meyasa nake tambayar kaina abubuwan da basu shafeni ba? No wannan ba halina bane kawai sharrin zuciya ne!"  Tafaɗi haka cike da tuhuman kanta, domin sam tasan tunanin rayuwarsa ba huruminta bane. Remote taɗauka tare da kunna ɗan madaidaicin tv plasman dake ɗakin, tashar MBC Bollywood takamo inda tasamu suna nuna film ɗin Sushant Singh  da Kriti Sanon wato Raabta, yanayin film din sosai yaɗauki hankalinta musamman yanda taga suna wata kalan rayuwa a daji, sam saita manta da tunanin komai ta bada hankalinta ga kallo.

_RAJ_
Koda yabar garden direct babban falon gidan ya nufa, babu kowa afalon kamar koda yaushe hakan yasa kaitsaye yawuce ɓangarensa,  yana shiga ya murzawa ƙofarsa key, gaba ɗaya zaman gidan ya ishesa, ayanzu bayason damuwar kowa ta dameshi, saboda haka  yaciro wani tablet dake jikin bedside drawer ɗinshi, ɓare maganin yayi ya jefa abakinsa sannan yabi da ruwa,  toilet ya wuce ya ɗauro alwala domin alokacin har ansoma ƙiraye ƙirayen sallan Magriba,  direct masallaci ya wuce, tunda yayi Sallah Magriba bai tashi ba har saida ya sallame isha yayi azkar,  yana fitowa daga cikin masallacin yasoma jin jiri na ƙoƙarin kadashi, lokaci guda kansa yayi masa nauyi, idanunsa sukayi luhu luhu, cikin dauriya yake tafiya ahaka har ya isa gida,  yana shiga cikin bedroom ɗinsa ya soma rage kayan jikinsa, dagashi sai long jeans haka ya faɗa   kan royal bed ɗinsa tare da jawo pillow ya ɗaura kansa akai, wani irin duhu yake gani a idanunsa, har takai ma da ƙyar  yake iya buɗesu mintuna kaɗan wani irin nannauyan bacci ya ɗaukesa,  daga yanayin yanda yake baccin idan ka gani kasan bana lafiya ba....

Washegari.

Tun da safe Ummu da Ziyadah keta ƙoƙarin haɗa breakfast a kitchine kasancewar yau Abba zai koma KD, jirgin ƙarfe 9 zaibi shiasa Ummu keta ɗawainiya tanason yayi break kafun yatafi, don ita tace dawowarta ba yanzuba saboda Sooraj.   Ba abun da Abba yakeso kamar Tuwo hakan yasa yauma Ummu tuwo takeyi masa da moringa soup wanda yaji cow meat da biscuit bone,  ƙarfe takwas daidai suka kammala gaba ɗaya aikinsu, Ziyadah ce ta jere komai akan dinning table,   Koda Ummu tagama serving ɗin Abba kujera taja ta zauna, har Abba yafara cin abincin ya ɗago ya kalli Ziyada wacce tayi shiru kamar me tunani.  "Jeki ƙiramin yayanki" Abba yafaɗa yana me duban tsadadden  agogon dake ɗaure a hanunsa,   cike da ladabi tamiƙe tare da nufar inda zai sadata da ɗakinsa, duk da cewa ƙirjinta dukan uku uku yake, amma haka ta daure, tana tura kanta acikin corridor ɗin da direct zai kaika ɗakinsa ta shaƙi daddaɗan ƙamshinsa wanda yake matuƙar hautsina tunaninta, wani irin sanyi taji yana busata cikin sanyin jiki taƙarasa jikin ƙofar ɗakinnasa, hanunta na rawa tayi knocking amma shiru ba'a amsa taba, cike da tsoro tasakeyin wani knocking ɗin nanma shiru babu amsa,  ɗan jim tayi tare da juyawa zata koma, tunani tayi idan takoma me zata faɗawa Abba tace tayi knocking ba a buɗeba ko me? hakan yasa tayi karambani'n  murɗa handle ɗin ƙofar, kamar da wasa kuwa taji ƙofan ta buɗe, wani daddaɗan ƙamshi tare da sanyin AC ne suka daki fuskarta har saida ta lumshe idanunta.  Ahankali taɗan kutsa kanta cikin ɗakin,   kwance yake akan bed yayi irin kwanciyarnan ta ruf da ciki, dagashi sai dogon wando gaba ɗaya gadon a hargitse yake tamkar wanda akayi kokuwa akansa, kallonsa tayi tundaga ƙasa har sama, gaba ɗaya kwanciyanma baiyita a dai dai ba, domin kusan rabin ƙafafunsa suna lilo suba a sama ba suba a ƙasa ba, gangarjikinsa ne kawai ke kan gadon,   idanunta ne suka sauƙa akan bayansa inda fresh white skin ɗinsa ke shining  yana fidda ƙyallin zufa, mamakine yakamata ganin jikinsa na fidda gumi, domin kuwa sanyin ac ne keta tashi acikin ɗakin, hatta tiles ɗin dake malale aƙasan ɗakin yaɗauki sanyi sosai,   sam takasa sanin bacci yake ko kuwa idanunsa biu,  cikin yanayi naɗan tsoro ta ɗan tako zuwa tsakiyan ɗakin,   muryarta akarye tace   "Yaa..." kasa ƙarasawa tayi, ɗan cije laɓɓanta tayi tare da rumtse idanunta, gaba ɗaya jarumtarta ta tattaro tace "Ya--yah!"    Jin shiru bai amsa ba yasanya tace  "Dama Abbane yace naƙiraka!"   shima dai shiru babu amsa hakan yasa taɗan matsa kusa dashi, jin zuciarta take kamar zata fashe saboda fargaba, da ace zai juyo ya kalleta alokacin to tabbas abu me sauƙine ta sume masa awajen.    "Ya--Yah katashi!" Ta sake faɗa tana ɗan leƙa fuskarsa, domin yanzukam taga alamun cewa bacci yakeyi.    Ko motsi baiyiba balle tasaran zai bude idanunsa har yatashi kamar yanda take ɓuƙata,  cike da karanbani taɗan sanya hanu ta bugi katifan da yake  kai,  tun tana ɗan bugawa ahankali harta gaji taɗan buga da ƙarfi, still ko motsawa baiyi ba, hakan yasa tasa hanu tashiga jan bedsheet ɗin dayake kai cikin shagwaɓan da batasan ta iyaba tace.
"Please Ya--yah wake up!"   cikin bazata taga ya mirgino tare da juyowa hartana iya kallon fuskarsa saidai kuma bai buɗe idanunsa ba,  da sauri taɗauke idanunta daga kan faffaɗan chest ɗinshi,   cike da ƙosawa taɗan bubbuga ƙafafunta aƙasa murya agajiye tace "Nidai dan Allah katashi aikoni fa akayi!"   Bawai baitashi bane duk abubuwan da takeyi masa yana jinsune tamkar amafarki, sam ƙarfin maganin baccin da yasha baigama sakeshi ba, ko sallan asuba daƙyar ya iya tashi yayi nanma agida yayi baije masjid ba, ƙasa ƙasa yaɗan buɗe sexy eyes ɗinshi wanda sukayi masa matuƙar nauyi, dishi dishi haka yake ganinta hakan yasa ya maida idanunsa ya kulle, sam batama lura da cewar ya ɗan buɗe idanunsa ba, blanket ɗin dayake kai taja da ƙarfi waiko zai tashi amma sam ko sake motsawa baiyi ba,  hawayene suka cika idanunta sai kawai ta juya tabar masa ɗakin.  Tana shigowa cikin falon tasamu Abba da Ummu tsaye harsun kammala cin abincinsu.    "Ya haka naganki ke ɗaya ina Sooraj ɗin?" Ummu ta tambaya tana me ƙarewa Ziyada'n kallo, domin kuwa baƙaramin jimawa tayi aɗakin Sooraj ɗin ba. 

Sunkuyar dakai ƙasa tayi cikin muryarta me sanyi tace. "Bacci yakeyi, tun ɗazu nake tashinsa kuma baitashi ba!"

"Bacci?" Ummu ta tambaya cike da mamaki.

Kai Ziyada ta É—aga mata alamar "Eh"

"Badamuwa ku barshi idan yatashi zamuyi waya, yanzuma haka nakusa makara!" Abba yafaɗi haka yana me nufar hanyar barin falon, Ummu ce ta rufa masa baya, ita kuwa Ziyada  ɗakinta ta wuce domin kuwa lokacin da MBC Bollywood zasu fara haska series ɗin Ishqmeinmarjawan  *(حب خادع)*  ya kusa kuma bataso tayi missing saboda sosai series ɗin keyi  mata daɗi.
Chapter 33 · 0% Book details