Sashe 80
Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Zaune ta samu Oummu acikin katafaren falon nata, fuska ɗauke da fari'a Oummu ta amsa mata sallaman da takeyi, cikin ladabi haɗi da biyayya ta ƙaraso har gaban Oummu, durƙusawa tayi tare da gaisheta, cikin sakin fuska Oummu ta amsa mata, tare da tambayanta ya take, cikin yanayi naɗanjin kunya Zieyaderh tayi ƙasa da kanta, haka Oummu ke ta janta da hira, itakuwa har cikin ranta kunyan Oummu takeji musamman idan ta tuna abun daya faru daren jia atsakaninta da Mr.Helper. Wayar Oummu dake aje bisa kan dinning table ne tasoma ruri alaman shigowar ƙira, Da sauri Zieyaderh ta tashi don ɗauko mata wayan, sam tamanta cewa agaban Oummu take hakan yasa take taka ƙafarta ahankali, duk dama bawani zafi takeji sosai acikin jikinnata ba.
Da kallo mai ɗauke da tsantsar nazari Oummu ta bita, wani tunani dayazo cikin ran Oummu ne yasanyata sakin murmushi mai ɗauke da tsananin jin daɗi, daidai lokacin Zieyaderh ta dawo hannunta ɗauke da wayar Oummu'n, cikin ladabi ta miƙawa Oummu wayar tare da dawowa ta zauna,  da sallama Oummu ta amsa wayar, saidai jin abun da ake faɗa mata acikin wayar yasanya ta miƙewa tsaye, cikin tsananin fargaba haɗi da tsoro tace.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!." Wayar dake saƙale akan kunnen nata ne ya sulale ya faɗi ƙasa, take idanunta suka cika tab da ƙwalla, cikin fargaba Ziryaderh ta kalli Oummu'n, ji tayi gabanta ya faɗi take wani irin tsoro ya shiga jikinta, hakanan tunaninsa ya faɗo mata arai, jikinta na rawa taƙaraso kusa da Oummu'n, kallonta Oummu tayi take kuma saitaji wasu irin hawaye mssu ɗumi sun gangaro daga cikin idanunta, wani irin matsanancin tausayin kansune ya kamata, ganin hawaye na fita daga cikin idanun Oummu yasanya taji faɗuwar gaban da takeji ya tsananta.
Hannu Oummu takai ta dafa kafaɗan Zieyaderh wacce itama idanunta sun cicciko da hawaye, duk da kasancewar ma batasan menene ke faruwa ba, daidai lokacin akaturo ƙofar falon aka shigo, Mas'oud ne ya shigo shima fuskarsa ɗauke da tsananin damuwa haɗi da tashin hankali, Oummu naganinsa taƙaraso garesa cikin sauri da ruɗewa takamo hannunsa, murya ɗauke da rauni tace.
"Mas'oud, SOORAJ!."
Idanu Mas'oud ya lumshe cike da tausayinsu, cikin son kwantar wa da Oummun hankali yasanya hannunsa ya share hawayenta,murya ƙasa ƙasa yace.
"Muje mu dubasa Oummu."
Da sauri Oummu tajuya ta haura sama don É—auko mayafinta.
Zieyaderh kuwa gaba É—aya kanta ya kulle, jin an ambaci sunan SOORAJ,yasanya jikinta ya É—auki rawa, sosai wani irin tsoro ya shigeta, bata fatan jin cewa wani mummunan abune ya sameshi, bazata iya jurewa ba, sam bazata iya jure abun da zai cutar mata dashi ba.
Oummu ce ta sauƙo daga kan mattakalan cikin sauri, ƙoƙarin yafa ƙaton mayafinta tayi, cikin kulawa ta dubi Zieyaderh dake zaune idanunta cike da ƙwalla, hannayen Zieyaderh'n ta kamo, duka suka ɗunguma sukayi waje, cikin motar Mas'oud suka shiga, dawani irin speed Mas'oud yaja motar, kai tsaye Nizamiyye hospital suka nufa.
Sosai likitoci suka duƙufa akansu wajen basu agaji da taimakon gaggawa,  sama da awa ɗaya likitotin nan suka share akansu suna ƙoƙarin ceto rayuwarsu, saidai kuma sunyi iyayinsu, amma abun naneman fin ƙarfinsu, duk da cewa Sooraj baiwani ji ciwo sosai ba, saidai buguwa daya samu ahanannu da kuma ƙafansa kawai, amma kuma yayi suman da har yanzu bai dawo cikin sense ɗinsa ba, shikuwa Pharouk sosai yasamu buguwa akansa, hannunsa da ƙafansa gaba ɗaya sun karye, gashi jikinsa gaba ɗaya ya kukkuje, sannan shi ne wanda yafara farfaɗowa kafun RAJ saidai kuma sam baya iya zuƙan numfashi da kansa, dole yasanya aka wuce dashi ICU domin ciwon nasa yayi tsanani, shikuwa Sooraj sun bashi duk wata taimako da zasu iya, daganan aka wuce dashi wani ɗakin hutu bayan sunyi masa wata allura mai ƙarfin gaske, wanda aƙalla zaiyi bacci na 5 hours kafun ya farka, suna kuma sa ran idan yafarka zai tashi lafiya ƙalau insha Allah.
Idanunta ne suka sake cika da hawaye ganin sun tsaya abakin ƙofar shiga asibitin, nanfa gabanta yafara dukan uku uku, take wani irin rauni ya cika zuciyarta.
Haka suka nufi cikin asibitin kowa da abun da yake saƙawa acikin rai da zuciyarsa.
Kaitsaye Mas'oud wajen wani babban likita me suna Dr.Anas wanda awajensa case din su Sooraj ɗin yake ya nufa, nan Dr.Anas ya ɗanyi musu ƙarin bayani tare da kwantar musu da hankali, sosai zuciyar Oummu dana Mas'oud suka ɗan samu salama jin cewar jikin Sooraj ɗin da sauƙi, har ma zai iya farfaɗowa zuwa anjima, ita kuwa Zieyaderh tuni zuciyarta tanarke da tsananin tausayin mijinta, take taji ba abun da take burin gani daji kamar sa.
Dr.Anas dakansa yayi musu jagora har zuwa ɗakin da Sooraj ɗin ke kwance, Dr.Anas ne ya dubesu tare da cewa idan suka shiga kar su cika surutu saboda zai iya affecting ɗinsa.
Haka suka shiga cikin ɗakin kowanne zuciyarsa ɗauke da fargaba, kwance suka iskesa flat fuskarsa na kallon sama, dagashi sai dogon wandon jeans a jikinsa, hannunsa na dama ɗaure yake da bandage haka ma ƙafarsa ɗaya itama an nannaɗeta da bandage, sannu ahankali ruwan da aka ɗaura masa ke ɗiga ajikinsa.
Jingina bayanta tayi da jikin ƙofar shigowar, lumshe idanunta tayi take saiga hawaye sun kwaranyo bisa kan ƙuncinta, hannunta tasanya ta dafe daidai saitin zuciarta da keyi mata zafi, ahankali su Oummu suka ƙarasa jikin gadon, hannu Oummu tasanya ta shafi lallausan sumar kansa, take kuma saiga hawaye zun kwaranyo daga cikin idanunta, Mas'oud ma ƙarasowa yayi yaɗan shafa kan SOORAJ ɗin,  Dr.Anas ne yayi musu alama akan subiyosa zuwa waje, babu musu dukansu suka bi bayansa, aɗan wani corridor ya tsaya dubansu yayi da kyau tare da cewa cikinsu su bar mutum ɗaya wanda zai kula da Sooraj ɗin, Oummu ne ta dubi Zieyaderh, cikin sanyin murya tace.
"Zieyaderh kibi Mas'oud ku koma gida ni zan zauna dashi kafun ya farka."
Da sauri Zieyaderh ta girgiza kanta so take tacewa Oummu A'a amma kuma bata da bakin musa mata, Dr.Anas ne ya dubi Oummu tare da cewa.
"Bashida mata ne?."
Ajiyar zuciya Oummu ta sauƙe, kana tace "Yana dashi."
Jinjina kai dr Anas yayi tare da yiwa Zieyaderh dake hawaye duban tsab, take jikinsa ya basa cewa itace matar Sooraj ɗin, duban Oummu ya kumayi cikin ɗan sakin fuska yace.
"Inaga kubar wannan sarauniyar hawayen ta zauna idan yaso sai ku ku koma, zaki iya kulawa dashi ae ko sarauniyar hawaye?." yaƙare maganan yana ɗan Murmushi.
Duk da yanayin da suke ciki saida Oummu da Mas'oud suka ɗan murmusa, maganar Dr.anas kuwa suka bi, inda Mas'oud ya maida Oummu gida don zataje tayi musu girki, nan akabar Zieyaderh.
Ahankali tatura ƙofar ɗakin ta shiga, cikin nutsuwa take takowa har zuwa inda yake kwance,  gab dashi ta ƙarasa, ahankali taɗan lumshe idanunta, wanda hakan ya bawa hawayen dake cikin idanun nata daman fitowa, hannunta ta ɗaura akan hannunsa wanda aka saƙala masa cannula, wata ƴar farar kujera dake gefe tajawo zuwa gaban gadon, zama tayi akan kujeran tare da ɗaura kanta ajikin gadon nasa, yayinda har yanzu hannunta ke riƙe da nasa, ahankali ta sauƙe idanunta akan kyakkyawar fuskarsa, komai nasa abun so da burgewa ne, sosai ƙawataccen sajen dake kwance akan fuskarsa ya kwanta lub bisa skin ɗinsa, ƴan ƙananan pink lips ɗinsa ta kalla masu kalan burgewa, kana ta dawo da kallonta ga kyawawan idanunsa wanda suke arufe ruf, sosai dogin eye lashes ɗinsa suka kwanta zara zara aƙasan idonnasa, ɗan lumshe idanunta tayi sannu ahankali takejin ƙarin zazzafar ƙaunarsa na ratsa gaba ɗaya jiki da jijiyanta.
Aje kanta tayi adai dai kafaɗunsa, ahankali take sauƙe ajiyar zuciya, sosai takejin tausayinsa na game gaba ɗaya jikinta, sannu ahankali wani irin bacci ke fusgarta, ɗaura kanta tayi akan hannunsa, cikin sanyin yanayi bacci ya ɗauketa.