← Book details Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 93

Sashe 46

Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Nagode ma"  Tafaɗa tana me gimtse dariyan dake bakinta, gaba ɗaya yasata nishaɗi don yanayin yanda yayi abun sai yazama tamkar wani small babyyy. 
Daga haka babu wanda yasake ce da ɗan uwansa wani abu har suka iso gida.    ƙoƙarin buɗe murfin motar take  muryarsa ya dakatar da ita, inda yake cewa tashiga da kayan da suka sayo ciki,   gidan baya inda aka sanya kayan ta buɗe tare da ciro ledodin ta wuce cikin gidan da su.  Bata samu kowa afalon ba hakan yasa kai tsaye ta wuce  sama,  tsayawa tayi ajikin ƙofar ɗakin Oummu tare dayin  knocking.     "Yes,Come in!" Oummu dake ciki ta bada amsa ataƙaice.  Tura ƙofar tayi ta shiga bakinta ɗauke da sallama.  "Oummu naganinta ta saki murmushi tare da cewa.
"Ƴan makaranta andawo kenan?"

Murmushi itama tayi cike da girmamawa tace "Eh nadawo, Oummu sannu da gida!"

"WaÆ´annan ledodinfa na menene?" Oummu ta tambaya fuska É—auke da mamaki.

"Ummmm dama Ya Almustapha ne yace nashigo dashi ciki!" tafaÉ—a cikin sanyin murya tana me aje ledodin.

Murmushi kawai Oummu tayi tare da cewa  "Aini nace yaje ya ɗaukoki, kasancewar naga anyi ruwa garin duk yaɗau ki sanyi, gashi Kamalu ma bayanan, ki cire uniform ɗin sai kici abinci ko!"

Kai ta kaÉ—a alamar "To" sannan ta juya ta fice daga cikin É—akin.

Tana shiga ɗaki ta soma cire uniform ɗin, gaba ɗaya wani irin sanyi takeji, ruwan daya daketa baƙaramin shiga jikinta sanyinsa yayi ba, gashi harwani ciwo ciwo takejin kanta nayi.  Da ruwan ɗumi tayi wanka kana ta sanya wata doguwar riga me kauri, rigan irin jallabiyannan ne na mata, amma tana da kauri sosai, sannan kuma haɗe take da hula, hulan ta sanya ta rufe kanta.  Saida tayi sallan Magriba sannan ta buɗe ƙofar ɗakin ta fito don samawa cikinta abinci.   Ahankali take sauƙowa daga kan matattakalan falon, tunkafun ta gama sauƙowa, ƙamshin turaren daya zame mata abunso ya daki hancinta, lumshe idanunta tayi tare da waresu alokaci guda,  mamakine yakamata na rashin ganinsa afalon, don tasan tabbas indai taji ƙamshinsa to yana wajenne.  Harta gama sauƙowa daga kan steps ɗin bata iske kowa acikin falon ba, kai tsaye kitchine ta wuce, kasancewar  yau ba a haɗa abinci akan dinning ba.   Fried cous cous and egg sauce aka dafa, kaɗan ta ɗiba don bata wani cika cin abinci da yawa ba, buɗe ɗayan food flask ɗin tayi, nan taga pepper soup ne na chicken's aciki, rufewa tayi don wannan ɗinma kaɗai ya isheta.  fridge ta bude ta ɗauko ruwa, daidai lokacin Oummu tashigo cikin kitchine ɗin,  ganin Zieyaderh a kitchine ɗin yasanya ta cewa.
"Yauwa Zieyaderh zoki kaiwa Sooraj coffee yana É—akinsa"

Wani irin ƙululuuuuu haka ƴaƴan  cikinta suka hautsina, ambatonsa ba ƙaramin faɗar mata da gaba yake yi ba, batasan mene dalili ba koda zancensa ake sai taji gabanta ya faɗi, ko kuma taji zuciyarta ta tsinke, ganinsa kuwa baƙaramin je fata acikin wani irin Yanayi yake ba.   Bata gama idar da tunanin nata ba, Oummu ta miƙo mata wani tray me ɗan faɗi, wanda samansa ke ɗauke da kayan haɗin coffee da kuma ɗan madaidaicin cup me kyaun gaske, sai kuma small flask.  "Idan kinje ki haɗa masa, ai dai kinga yanda na haɗa masa ranan ko?" Oummu ta tambaya tana me miƙa mata tray ɗin.  Kamar wadda aka zarewa laka ajiki haka ta amshi tray ɗin tare da cewa "Eh nagani"   Ficewa tayi daga cikin kitchine ɗin, yayinda zuciya da ƙirjinta keta bada wani irin sauti.

Dawowarsa daga Lagos kenan, dama baije don ya kwana ba,  socks ɗin dake ƙafansa ya cire sannan ya zare suit ɗin dake jikinsa, maɓallan long sleve ɗinsa yashiga cirewa,  yana kammalawa ya cire rigar tare da zare white singlet ɗin dake jikinsa, belt ɗin wandon shi ya zare  yana me ƙoƙarin zame wandon ƙasa yaji ana knocking ƙofarsa, bai kula ba ya cigaba da cire kayansa, jin still ana knocking ɗinne yasanya shi ɗaukan wani 3 guater jeans ya sanya,  ko gama zuge zip ɗin wandon baiyi ba, ya nufi wajen ƙofar ransa aɓace, ko damuwa da yanda saman maranshi ta bayyana baiyi ba.  Itakuwa  Zieyaderh dake tsaye gaba ɗaya atsorace take, harta gama yanke shawaran cewa zata koma kawai tace da Oummu ƙofar a kulle take.  Da wani irin fushi ya buɗe ƙofar, idanunsu suka faɗa cikin na juna, kallonta yayi from head to toe sai kawai yasaki wata tsuka me sauti tare da komawa cikin ɗakin, ganin haka yasa jikinta ya shiga ƙyarma ba shiri ta bi bayansa, hannunta har rawa yake wajen aje tray ɗin, ƙoƙarin haɗa masa coffee ɗin take ya juyo tare da soma tahowa inda take, cak ta tsaya daga haɗa coffee ɗin da take,  tare da sunkuyar da kanta ƙasa, tabbas kunnuwanta  sautin takunsa suke jiye mata, wanda ke ɗauke da alaman cewa gareta yake zuwa, hakan yasa wani uban tsoro ya lalluɓeta, wanda har ya kaita ga kasa ɗaga kai ta kalleshi.  Taku biyu kacal ya rage atsakaninsu yace.      "Ke!!"

Da sauri ta ɗago kanta aɗan daburce tace "Umm!"  sake matsowa kusa da ita yayi wanda hakan yasa gaba ɗaya takusa ficewa hayyacinta, gab da ita yazo har suna iya jiyo hucin numfashin juna, sosai ta ruɗe sakamakon ganinsa agabanta, baƙaramin cika mata idanu yayi ba, gaba ɗaya ba ta iya ganin komai don yacika mata gaba da faffaɗan chest ɗinshi, haka ta zama wata ƴar cukula agabansa, gaba ɗaya jikinta ɓari yake.. Cikin wani irin husky voice ɗinsa yace. "Ke baki da hankali ko? Haka aka koyar dake  bugun ƙofa?"

Yanzu kam ba iya gangar jikinta bane  ke rawa,  harma da laɓɓan bakinta, cikin daburcewa tayi ƙasa da idanunta don bazata iya kallonsa ba, idanunta ne suka sauƙa akan waist ɗinshi wanda har saman mararsa ta bayyana, kasancewar har yanzu bai ƙarasa jan zip ɗin wandon nasa ba, wasu jijiyoyine kwance akan maran nasa wanda suka mimmiƙe, ga wani irin murɗewa da  cikinsa yayi, da sauri ta rumtse idanunta, tana me ƙara ƙanƙame jikinta.  "Badake nake magana ba!!" Yafaɗa atsawace.  Baƙaramin tsorata ta wannan tsawan yayi ba, har batasan lokacin da ta ƙanƙame jikinta sosai ba, bakinta na rawa tace "Dan Allah kayi haƙuri, Allah Bazan sake ba!"

Kallon fuskarta yayi tare da ɗan cizan laɓɓansa, hannayensa ɗaure akan waist ɗinsa yace.       "Buɗe idanunki!"
Kasa buɗe idanunnata tayi saima rawan jiki data ƙara, tare da kullesu ƙam.

"I say open your eyes!!!" Yafaɗa murya akausashe.  Tun kafun ya gama idar da zancen, ta buɗe idanunta tare da sauƙesu akansa. Sarƙewar idanunsu waje guda yasanya idanunta sukayi wani irin juyawa, take suka wani irin lumshewa luuuuu  kamar  zata sume.  Cikin tsawa yace "Wallahi idan kika sumemin saina wanka miki mari stupid girl!!"  ae kuwa tamkar wanda ya watsawa ruwan sanyi saigata ta tsaya cak akan ƙafafunta,  tare da sake maida idanunta ta rufe, saidai ya kasheta amma tabbas bazata iya kallon cikin ƙwayan idanunsa ba, musamman ma ayau, idan kuwa tace zata sake kallonsa to tabbas  sumewa zatayi koda kuwa kasheta zaiyi bayan ta farfaɗo.

Tsaki yayi tare da nuna mata hanyar ƙofa murya akausashe yace.  "Out!"

Ae kamar jira take haka ta tattari ƙasan riganta aguje ta fice, baki ya buɗe yana mamakin yanda tasa gudu kamar wacce aka turowa dodo.  "Wannan yarinyar anya tana da lafiya kuwa?" Tambayar daya yiwa kansa kenan cike da mamaki, ƙofarsa ya rufe tare da murza mata key,  bathroom ya shige tare da sakarwa kansa shower.

Aguje ta haura steps ɗin dake cikin falon, tana kaiwa ɗakinta ta shige tare da rufo ƙafar, kan gado ta faɗa tare da lumshe idanunta, har yanzu jikinta baiwani gama daina ɓari ba,  saida ta ɗauki kusan  8  minute tana maida numfashi, kafun tasamu daman dawowa cikin nutsuwarta.   Shiru tayi tare da cusa kanta acikin pillow, yau kam gaba ɗaya brain ɗinta ta cushe, yayinda tunaninta kuwa gaba ɗaya ya gudu.

Ruwan shower ne ke dukan lafiyayyar fatan jikinsa, yayinda hannunsa ɗaya ke dafe da bango,   akasalance ya buɗe idanunsa, kasancewar yajima tsaye ruwa na dukansa, hakan yasa idanunnasa suka ɗanyi ja.  So yake ya goge wannan tunanin daga cikin ransa, so yake wannan idanun su fice daga cikin nasa idanun, so yake duk wani abu dake cikin zuciyarsa ya goge, baishirya ɗaukan wannan ƙalubalen ba, bakuma yajin zai shirya har abada,  hannu yasa ahankali ya kashe shower'n, tare da ɗaukan wani nead towel ya ɗaura akan waist ɗinshi. Haka ya fito daga cikin bathroom ɗin jikinsa na ɗigan ruwa,   wani ɗan ƙaramin towel ya ɗauka ya shiga goge jikinsa,  sama sama ya shafa mai ajikinsa, sannan ya sanya long jeans, shida kansa ya haɗa coffee ɗin yasha, jin ana ƙiraye ƙirayen sallan Isha ne yasanyashi miƙewa, wata farar rigar Dolce and Gabbana mai kamar na sanyi ya sanya, kasancewar ana yanayin sanyi hakan yasa ya jawo hulan  dake jikin rigan ya rufe kansa dashi.  Yana fitowa ya haɗu da Almustapha shima masallacin zaije saboda haka atare suka wuce. 

Washegari.
Chapter 46 · 0% Book details