← Book details Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 93

Sashe 17

Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk yanda yaso bacci ya ɗaukesa abun yaci tura, kwance yake akan makeken Royal bed ɗinsa wanda yaji lallausan bedsheet.  Idanunsa dake alumshe ya buɗe haɗe da sanya hanu ya dafe kansa dake wani irin sara masa kamar zai faɗo ƙasa haka yakeji.  Gaba ɗaya duniyar bata yi mashi daɗi, ƙuna yakeji acikin zuciyarsa abubuwa da yawa ne suka haɗe masa,  hanunsa na dama ya sanya akan cikinsa wanda ke ɗauke da manya manyan 6 packs,  ahankali ya ke murza fatan cikinsa,  idanunsa gaba ɗaya sun kaɗa sunyi jajur dasu.  Cigaba yayi da murza fatar cikinsa da ɗan ƙarfi haɗe da cije laɓɓansa.  "Sai yaushe ne zai zama mutum me cikakken lafiya? sai yaushene zai san cewa shima Namiji ne? yaushe ne damuwarsa zata gushe? yaushe ne zaiyi bacci acikin farinciki da nishaɗi? yaushene zaiji abun da yake buri da fatan ji watarana? Abun tambayar aransa shine yaushe ne yazama haka? yaushe ne kuma zaici wannan jarabawar tasa mai wahala?"  waƴannan tambayoyin su yakeyiwa kansa akullum, sau tari yakan cire rai amma yasan Allah na sane dashi idan yana darai watarana zai dace,  amma kuma yaushene wannan ranan zata zo? shine abun da baisani ba,    tashi yayi ya zauna still hanunsa nakan fatar cikinsa yana murzawa. Ƙafafunsa ya zuro ƙasa tare da sauƙowa daga kan gadon,   gaban window ɗinsa ya nufa, tsayawa yayi ajikin window'n haɗe da sanya hanu ya yaye labulen window'n, buɗe glass ɗin window'n yayi  take wata iska mai daɗi ta bugi fuskarsa, lumshe idanunsa yayi haɗe da buɗesu alokaci guda, ɗaga kansa yayi yana kallon sararin samaniya, farin wata ne ya haske ko ina da ina.  Ahankali ya kejin nutsuwa na sauƙar masa, sosai yakejin daɗin ni'imar dake hurawa, yajima tsaye ajikin window'n kafun ya dawo cikin ɗakin.  Kwanciya yayi akan gado yayinda ƙafafunsa ke ƙasa, ahaka wani bacci ya ɗaukesa, dagani kasan bajin daɗin baccin yake ba.

** **

Tun 7 ta kammala duk wani shirinta,  saboda ta fahimci ba aso azo late a makarantar, duk yanda ta buga sammako wajen fita, amma bata iske shi afalo ba, saidai ta iske daddaɗan ƙamshinsa mai sanya nutsuwa, haka tashiga mota Kamalu driver yaja motar suka tafi batare da tayi tozali dashi ba.

Kamalu driver na tsaida motar ta  ɗauki jakanta haɗe da soma ƙoƙarin buɗe murfin motar.     "Ga wannan Oga yace abaki" Kamalu driver ya tsaidata tahanyar faɗan haka, yana mai ciro kuɗi acikin aljihunsa.

Kallon kuɗin tayi sannan ta kalli Kamalu driver.  "Ni kuma mai zanyi dasu to?" ta tambaya cike da mamaki.

"Haka dai yace abaki, hala ko kuɗin taran ki ne" Kamalu driver yafaɗi haka yana me ƙara miƙo mata kuɗin.

Cikin sanyin jiki tasa hannu ta amshi kuɗin, sannan tafice daga cikin motar aranta tana mai cewa da zaran takoma gida zata tambayeshi, hala ko wani abu ya keso tasayomasa da kuɗin. 

Yau ta riga Shukra da Nasmah zuwa saboda haka ita kaɗai ta zauna tayi jigum,  ba wani jimawa sosai sai gasu sunzo atare, ga mamakinta yau fuskar Shukra asake take babu tsumewa kamar na jiya,  Nasmah na ganinta ta saki murmushi haɗe da ƙarasowa ta zauna akusa da ita.   "Yau munyi late kin rigamu zuwa" Inji cewar Nasmah dake ƙoƙarin sauƙe jakarta dake kafaɗarta.

Ta buɗe baki zatayiwa Nasmah magana kenan malami ya shigo ajin. Sai bayan yafita ne suka ɗanyi taɗi da Nasmah.. Yau dai sosai Nasmah tasake jawota jikinta ko ina zasu tare suke zuwa kuma Shukra na biye dasu saidai bata cika yawan magana ba. Hatta sallah yau atare sukayi su duka ukun.   Ko da suka idar da sallan ma tare sukaci abinci wanda Shukrah ce tazo musu da jallop rice wacce taji ɗanyen kifi.

Yauma agajiye ta dawo daga school É—in tana idar da sallah ta soma bacci.

*** ***
Yau kimanin sati guda kenan tana zuwa makaranta, Alhamdulillah yanzu kam tana ɗan fahimtan wasu abubuwa musamman da Nasmah ta dage da koya mata,  acikin waƴannan kwanaki tayi sabo da Nasmah sosai, duk da cewa Shukra na shiga sha'aninta yanzu amma sunfi sabo da Nasmah,  aduk tsawon kwanakinnan bata taɓa ganinsa ba koda sau ɗaya ne,  saidai idan ta fito falo tana samun tsaraban ƙamshinsa dayake barmata akowacce rana.

(Wallahi yau ina busy sosai, tun jiya nagama typing amma bansamu daman yin update ba sai yanzu, . please kuyi manage da wannan banyi editing ba. Love you all and Son So.
Ku ƙaramin yawan Vote na ƙara muku yawan typing👌)
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
  
          *SOORAJ !!!*

   *Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Life (Sardauna)*

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION*
_{United we stand and succeed; Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}_
*https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation*

            *WATTPAD*
      @fatymasardauna

#romance

          *Chapter 16*

Saturday!

Kamar dai yanda kowa ya sani saturday ranar hutuce ga yawancin ɗaliban makarantar boko.   To haka ranar yau ta kasance saturday wato (Asabar).  Zaune take aƙasa ta tanƙwashe ƙafafunta, jakar makarantarta ne agabanta, sai kuma wani littafin English ɗin dake riƙe a hanunta,  lecture'n da akayi musu jiya take dubawa, so take karatun ya zauna akanta sosai, don taji malamin nacewa wani sati zai basu Assignment.  Tunda tayi sallah ta ke riƙe da littafi, gaba ɗaya hankali da nutsuwarta naga littafinta so take ta iya duk wani abu da aka koya musu,  a yanda ta ba da himma ne yasa ta fahimci wasu abubuwa da dama, wato shi karatu ɗan naci ne idan kanace masa da yardan Allah Zaka iya, sannan zaka gane komai sannu ahankali, yarda da wannan da tayi ne yasa abubuwa da yawa dake cikin karatun da take suka zauna akanta.    Yunwar da ta soma ƙwaƙulan cikinta ne yasa ta aje littafin haɗe da jingina bayanta da jikin gado, ajiyar zuciya ta sauƙe, tare da lumshe idanunta da suke cike da bacci, kasancewar daren jiya bata wani samu isashshen bacci ba, domin kuwa jiya ba tayi bacci da wuri ba, har sai wajen ƙarfe 12:30  na dare sannan ta kwanta, karatu tayi sosai, sannan gashi kuma yau tayi tashin sassafe sakamakon wani irin zazzaɓi dake ta sanɗanta tun jiya da rana, amma dayake zazzaɓin baiyi ƙarfi ajikinta ba hakan yasa bata jikkata ba.
***
Duk da cewa yau Asabar amma bayajin zai iya zaman gida, shi kansa yasan yana da buƙatar hutu amma kuma yasan ko ya zauna agida hutun nasa bazai samu yanda yakeso ba.  Fitowarsa awanka kenan yana ɗaure da towel a ƙugunsa, sannan kuma ga wani ɗan ƙaramin towel still dake riƙe a hanunsa, yana tsane ruwan dake kansa.   Yana gamawa ya ɗauko handryer, da shi yayi amfani wajen busar da gashin kansa, mayinsa mai ƙamshi ya shafa, sannan ya ɗauki comb ya shiga taje sumar dake kansa, mayukan gashi har kala uku ya shafawa kansa, take gashin kannasa ya ƙara bayyana sheƙi da kuma walwali.   Dogon wandon jeans wanda ke ɗauke da zane irin na kayan sojoji ya sanya, wandon irin mai yawan aljihunnan ne sannan ƙasan wandon atsuke yake da rubber,  wata farar t-shirt ya sanya ajikinsa,  take kyawunsa ya sake bayyana sosai kayan suka amshi jikinshi, kasancewarsa namiji mai murɗaɗɗiyar surar jiki,  gun ƴar ƙaramar drawer'n da yake aje drugs ɗinsa ya nufa, wani magani dake cikin sachet ya ciro, tare da ɓallan guda biyu ya watsa abakinsa, sannan yakora da ruwan swan. Hanunsa riƙe da goran swan ɗin ya nufi falo.

Yana shiga cikin falon ya soma bin ko ina dake cikin falon da kallo, ko alaman datti babu acikin falon, hakanne ya tabbatar masa da cewa tabbas gyara falon akayi, duk da cewa dama babu wani datti acikin falon, amma dai kallo É—aya zakayi kasan an gyara falon.

Kitchine ya wuce ya tafasa ruwan zafi acikin heater cup, yana gamawa ya juye a flask.   Zama yayi akan dinning tare da haɗa tea ɗinsa.  Sanya kofin tea ɗin yayi agaba ya kasa koda ɗauka ne yakai bakinsa, sai jujjuya spoon ɗin dake hanunsa yake acikin cup ɗin, yanayin yanda ya nutsu yayi shiru shine abun da zai baka tabbacin cewa tunani yakeyi. Tabbas kuwa tunanin yake, maganganun da mahaifinshi yayi mishi masu tsauri su suke damunshi, bai ɗauka fushin da mahaifannashi keyi dashi har yakai haka ba, bai taɓa tunanin suma zasuƙi fahimtarshi ba,  maganan da Abbanshi yayi mishi akan cewa  wai ya nemo matar aure ya aura, acikin ƴan ƙanƙanin lokaci idan ba haka ba kuma kada ya sake ƙiran wayanshi shine abun dake damunsa, tabbas hukuncin da Abbansa yayi mishi yayi tsauri da yawa, koda wasa baitaɓa tunanin zasu sake kawo mishi maganar aure nan kusa ba,  ya ɗauka zasu fahimceshi a wuce wannan stage ɗin, ashe abun ba haka yake ba.  Wayarsa dake gefensa ne tasoma ƙara alaman shigowan ƙira,  jikinsa a sanyaye ya ɗaga ƙiran tare da kara wayar akan kunnensa. 

Mas'oud dake zaune acikin motarsa yace
"Gaye na shigo Abuja fa yanzu"

Cike da É—an mamaki Sooraj yace

"Da gaske?"

"Bakayarda ba?"  murayar dake cikin wayar Sooraj ne ta bayyana raɗau acikin falon, da sauri Sooraj dake zaune akan dinning ya kalli ƙofar falon.

Mas'oud yagani yana murmushi.

Murmushin da iya kansa leɓe Sooraj yayi tare da kashe wayarsa. 
"Kai É—an rainin hankaline Mas'oud" Sooraj yafaÉ—i haka yana me kallon Mas'oud dake takowa zuwa garesa.

"Ni ne ɗan rainin hankali, ko kuma nida kai ne dukanmu ƴan rainin hankali?" Mas'oud ya faɗi haka yana mai ƙoƙarin jawo wata kujera dake fuskantar wacce Sooraj ke kai ya zauna.

Still ɗan guntun murmushinsa yayi, haɗe da ɗaukan kofin tea ɗinsa ya ɗanyi sipping kaɗan. 

"Sauƙar yaushe?"
ya tambayi Mas'oud.

"Banwuce 30 minute da sauƙa ba" Mas'oud yafaɗi haka yana mai ƙoƙarin ɗaukan wani cup zai haɗawa kanshi tea, duk da cewa bawani damuwa da tea din yayiba kawai don yanajin yunwa ne ya sanya zai sha.

ÆŠan sipping tea É—in kaÉ—an yayi, tare da kallon Sooraj da yaketa aikin juya tea da spoon É—in dake hanunsa, ya É—an karanci damuwa akan fuskar Sooraj É—in, amma da yake yasan kwanan zancen sai kawai ya share haÉ—e da cewa..
  "Ya maganan waƴannan kayanne? kasanfa yanzu babu kaya aƙasa"

Ajiyar zuciya Sooraj ya sauƙe haɗe da cewa "Next week zanje USA zan taho dasu"
Chapter 17 · 0% Book details