← Book details Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 93

Sashe 66

Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Aunty Muhibbat ce tazo ta kama Zieyaderh inda kai tsaye suka wuce ɓangaren SOORAJ wanda aka sake ƙawatasa aka kuma zuba masa sababbin kayan funitures masu kyau da burgewa komai dake cikin falon kalan pitch and milk colour ne, sosai falon yayi kyau, daga gefe guda kuwa one bedroom ne kaɗai acikin falon wanda shima aka ƙawata cikinsa da furnitures light pink da fari,  sosai komai yayi kyau, akan haɗaɗɗen gadon dayaji lallausan katifa Aunty Muhibbat ta zaunar da ita,  inda ta sanya mayafi ta rufe mata gaɓa ɗaya jikinta,     nan itama tayi mata ɗan taƙaitaccen nasiha,  cikin dabara tace mata zataje ta ɗauko wayarta tana zuwa,  kai kawai Zieyaderh ta iya jinjina mata alaman to.
Aunty Muhibbat na fita daga cikin ɗakin ta saki murmushi, don wayo kawai tayiwa Zieyaderh babu wani wayarta da zata je ɗaukowa, tafaɗi hakane kawai don tabarta tatafi cikin salama. 

9:00 pm

Tun tana jiran dawowan Aunty Muhibbat harta gaji, sannu ahankali takejin wani irin bacci na fusgarta, yayinda agefe guda kuwa takejin wani amai da tashin zuciya na taso mata, wani irin luuuuu haka takejin kanta kamar wanda jiri ke shirin kaiwa ƙasa, lumshe idanunta tayi tama mejin wani abu me ɗumi daya fito ajikinta, da sauri ta yaye mayafinta tare da saƙƙowa daga kan gadon, banɗaki ta nufa, inda tana shiga ta sauƙe wani irin ajiyar zuciya don babu makawa tasan cewa period ɗinta ne yazo, mamakine ya cikata ganin cewa wannan karon mara da cikinta basuyi mata ciwo kamar yanda suka saba yi mata aduk lokacin zuwan period ɗinta ba,  tsabtace jikinta tayi tafito zuciyarta ɗauke da fargaba, don sam batasan yanda za'ayi ta samu pad ta sanya ajikinta ba,  tana fitowa daga cikin toilet ɗin ta jingina bayanta da jikin bango, idanunta ne ya sauƙa akan ƙatuwar trolly ɗinta, wani irin ajiyar zuciya ta sauƙe tare da ƙarasawa gaban trolly ɗin, tana zuge zip ɗin jakan tazaro pad ɗinta tare da komawa cikin bathroom ɗin da sauri,  tsabtace jikinta tayi tare da dawowa ta zauna aɗan bakin gadon, takure jikinta waje  ɗaya tayi tare da lumshe idanunta,   cikin ƴan mintunan da basu wuce 15 ba bacci ɓarawo ya ɗauketa..

11:00 pm.
Dai dai motarsa tashigo cikin harabar gidan, yana gama daidaita parking ɗin motar a parking lot, ya buɗe murfin motar ya fito tare da sawa motar tasa key, ahankali yake tafiya har ya shigo cikin babban falon gidan, duhune gaba ɗaya ya mamaye falon yayinda ko ina ya ɗauki shiru, kaitsaye ƙofar da zata sadashi da ɓangarensa ya buɗe ya shiga, direct bedroom ya nufa, ahankali ya tura ƙofar ɗakin ya shiga, yana shiga ya maida kofan ya rufe tare da murza mata key, yana juyowa idanunsa suka sauƙa akanta, kwance take tana bacci abaki bakin gado yayinda ta duƙunƙune jikinta waje ɗaya, dagani kai kasan bata shiryawa baccin ba ya ɗauketa, wani irin duka ƙirjinsa yayi ahankali ya lumshe idanunsa tare da jingina bayansa da jikin ƙofar ɗakin, wata irin ƙatuwar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ware idanunsa ahankali ya kuma sauƙesu akanta, sam yama manta da batun kawota ɗakinsa da Oummu tayi masa ɗazun, sama da minti goma ya ɗauka yana kallon yanda ta nannaɗe jikinta waje ɗaya, sake lumshe idanunsa wanda sukai ja yayi tare da ɗan cizon laɓɓansa, sam baiso ace ƙaddaransa ta shafeta ba, sai yanzu yafahimci dalilin dayasa wasu lokuta takan tsaya masa azuciyarsa, saiyanzu kuma yagane cewa zanen ƙaddaranta ne shumfuɗe azuciyarsa, maganganun da Oummu tayi masa ɗazunne suka shiga dawowa cikin kunnensa filla filla, ahankali ya raba bayansa da jikin ƙofan tare da ƙarasowa cikin ɗakin, kayan jikinsa ya soma ragewa yayinda ya cire rigar dake jikinsa, bathroom ya wuce inda ya sakarwa kansa shower, yajima atsaye ruwa na dukan jikinsa, ahankali wata irin nutsuwa ke sauƙar masa, yana gama wankan yayi alwala kana ya fito daga cikin toilet ɗin, kaitsaye gaban ƙaton sif ɗin kayansa ya nufa, wani dogon wandon jeans ya sanya, tare da barin murɗaɗɗiyar surar jikinsa awaje batare daya sanya riga ba, wani farin towel ya ɗauka yashiga goge kansa dake jiƙe da ruwa, yana kammalawa ya feshe gaba ɗaya jikinsa da daddaɗan turarensa mai sanya nutsuwa, kashe gaba ɗaya makunnan wutan ɗakin yayi, kan wata doguwar kujera dake cikin ɗakin ya nufa, kwanciya irinta ruf da ciki yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, gajiyayyun idanunsa ya lumshe yana me fitar da numfashi ahankali, kasancewar amatuƙar gajiye yake hakan yasa mintuna ƙalilan bacci ya ɗaukesa.

2:00 pm sosai take ta faman juyi akan gadon hannunta dafe da mararta dake tsananin ciwo, tamkar acikin mafarki haka takejin wani irin azababben ciwon mara na damunta, cikin tsananin wahala ta buɗe idanunta wanda lokaci ɗaya suka ƙanƙance saboda tsabar wahala, wani ɗan ƙara tasake sakamakon wani irin murɗawa da mararta tayi, lokaci guda ciwon ya tsananta fiye da wanda takeji acikin bacci, duk da sanyin ac'n da yacika gaba ɗaya ɗakin hakan bai hana jikinta fitar da gumin wahala ba, cikin matuƙar tsoro daya kamata da kuma zafin ciwo tasaki wani irin kuka, sosai jikinta ke karkarwa gashi ɗakin gaba ɗaya gauraye yake da duhu, wani irin murɗawa da mararta tayine yasanyata yin wani irin juyi, haka tafaɗo har ƙasa da ga kan gadon, wani irin sabon kuka tasanya yayinda ta dafe mararta da takejinta kamar zata tarwatse.

Ahankali sautin sheshsheƙan kuka ke ratsa cikin kunnuwansa, tun yanajin abun kamar amafarki har ya soma jiyosu raɗau acikin kunnuwansa, ahankali ya ware idanunsa dake cike da bacci, shiru yayi yana mejin sautin kukan nata na ratsa ko ina dake cikin ɗakin, cikin ɓacin rai ya rumtse idanunsa, sam shikam baisani ba ko aljanune da ita wanda ke sata kuka tsakiyan dare, don wannan bashine karo na farko da kukanta ke tashinsa abacci ba, cikin takaici yagyara kwanciyarsa tare da maida idanunsa ya rufe.
Ita kuwa Zieyaderh ciwon mararne ke sake cin ƙarfinta hakan yasa taci gaba da rera kukanta cikin fitar hayyaci, duk yanda yaso ya manta da ita yayi baccinsa hakan ya faskara domin kuwa jin kukannata yake har acikin ƙahon zuciyarsa, tsuka yayi tare da buɗe idanunsa, hannunsa yakai saman kujeran dayake kai, wani ɗan madanni ya danna take wani blue ɗin haske ya gauraye ɗakin, idanunsa ya sauƙe akanta, har yanzu kwance take aƙasa tana ta murƙususu, gaba ɗaya ta birkita kanta, tuni ɗan kwalin dake kanta ya kama gabansa, ahankali ya aje ƙafafunsa aƙasa tare da miƙewa tsaye, cikin takunsa mai ɗauke da nutsuwa ya ƙarasa gareta, tsayawa yayi akanta yana me kallon yanda take kuka tsakaninta da Allah hannunta dafe da mararta, ahankali yaɗan sunkuyo cikin ƙosawa daji kukan nata yace.
"Waike bakida lokacin yin kukane sai tsakiyar dare? zaki tashi daga ƙasannan ne ko saina ɓaɓɓala miki waƴannan siraran ƙafafunnaki?"
Chapter 66 · 0% Book details