Sashe 79
Sooraj Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Sannu ahankali yake murza steering motar, zuciyarsa ɗauke take da tunaninta mai tarin yawa, sosai yakejin wani abu na musamman agame da ita na game gaba ɗaya jikinsa, da tunani kala kala acikin ransa yaƙaraso haraban babban asibitin.
Cikin nutsuwa yake tafiya yayinda ya nufi hanyar da zata sadashi da office É—in Dr.Waleey.
Amna sakateriar Dr.Waleey na ganinsa ta miƙe da sauri cikin mayen sonsa da tajima tanayi taɗan ƙaraso da sauri, cikin ƙasa da murya tace.
"Ranka ya daÉ—e barka da zuwa."
Kansa kawai ya ɗaga mata batare daya ce da ita komai ba, ganin fuskarsa atsuke kamar koda yaushe yasanya ta juya da sauri ta nufi office ɗin na Dr.Waleey, bawani jimawa tafito inda tanuna masa ƙofan office ɗin alaman ya shiga, baiko kalli inda take ba ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shige ciki.
Dr.Waleey naganinsa ya saki murmushi tare da tasowa ya bawa SOORAJ É—in hannu suka gaisa, kujera ya nunawa Sooraj É—in, bayan Sooraj ya zauna ne yajawo kujeran dake facing na Sooraj din shima ya zauna.
Cikin rashin sabo da yawan magana Sooraj yaɗan ɓata fuska, cike da aji yasanarwa Dr.Waleey irin zazzafan zazzaɓin dake damun jikinsa, sannan yaƙara da sanar masa yanda kansa ke masa bala'in ciwo kamar zai rabe gida biyu.
Murmushin tsananin jin daÉ—i Dr.Waleey yayi don aÉ—an bayanin da Sooraj É—in yayi masa tuni yagano abun dake damunsa, cikin jin daÉ—i da kuma son kwantar masa da hankali Dr. Waleey yayi ajiyar zuciya, tare da gyara zama, kana yace.
"Ƙwarai naji daɗin wannan labarin SOORAJ, tabbas alamomin zazzaɓi da ciwon kannan da kakeji alamane dake nuna cewa kaima yanzu kazama cikakken Namiji mai lafiya, dama cutarka ba da ita aka haifeka ba, sannan kuma ba sihiri ko shafar aljanu bane, cuta ce da Allah Kan iya sawa kowani bawa, Allah Shi ya ɗaura ma kuma gashi ayanzu shi ya yayema, tabbas wannan yana daga cikin ƘADDARANKA dama ita Jarabawa takanzowa bawa ta inda baizata ba, sannan idan tayi tsanani Allah yakan sauƙaƙata, kada kayi mamakin samun lafiyarka SOORAJ saboda cuta da kuma sauƙi duk na Allah Ne, Allah Ne kaɗai kan iya bayar da lafiya ga bawa aduk lokacin dayaso."
Ɗan numfasawa Dr.Waleey yayi tare da ɗaukan wata farar takarda yaɗanyi rubutu kaɗan akai, miƙawa Sooraj paper ɗin yayi cikin kulawa yace.
"Ga wannan idan kafita sai kasaya a babban pharmacy, magungunane da zasu sauƙaƙa wajen hana zafin zazzaɓin yin ƙarfi, bare har yakai ga ya dameka, kuma sannan zazzaɓin ya shigeka ne saboda yanayin yanda ka sarrafa jikinka batare daka saba ba, Insha Allah Nanda wani lokaci komai zai dawo normal, sannan ayanzu zakanajin wani irin feeling na tasomaka sosai, kada kace zaka jure abunda kakeji, ka ƙoƙarta yin sex akai akai zai taimaka ƙwarai wajen dawo maka da cikakkiyar lafiyarka."
Amsan papern Sooraj yayi tare da miƙewa tsaye, jin surutan da Dr.Waleey'n keyi, har yasanya kansa ya fara yi masa ciwo, hannu ya bawa Dr.Waleey inda sukayi musabaha daga nan yayi masa sallama, koda ya fito daga cikin office ɗin na Dr.Waleey haka Amna tabisa da wani irin mayataccen kallo harya ɓacewa ganinta, sosai yake tsananin burgeta, kama daga yanda yake dressing da kuma yanda yake aiwatar da komansa cikin nutsuwa, haka kuma sosai MISKILANCI nsa ke burgeta, duk da cewa miskilancinnasa ya zarce misali amma ahaka take kwaɗayin rayuwa dashi, saidai kuma tasan kamar yanda wutsiyar raƙumi tayi nesa da ƙasa, haka shima yayi nesa da ita, don yazama kamar wutsiyar raƙumi itakuwa tazama tamkar ƙasa, dama ance hanyar jirgi daban hakama na mota daban.
Yana isa compound É—in asibitin direct inda motarsa take ya nufa, yana shiga yabata wuta.
Gudu sosai yake shararawa akan babban titin dazai sadashi da unguwar ta Maitama, sanye yake da baƙaƙen kaya ajikinsa yayinda yasanya wata baƙar mask ya rufe gaba ɗaya fuskarsa, idanunsa kawai zaka iya hangowa, ayanda yakejin zucia da ransa na tafasa yanajin komai ma zai iya aikatawa, ayau bayajin zai iya haƙuri yashanye ɓacin ran da SOORAJ ke ɗura masa, SOORAJ ya ƙwace masa komai, a sanadin sa yarasa abubuwa da dama, asanadin SOORAJ yarasa babban matsayin dayake kai, sanadin SOORAJ company'nsa wanda yake matuƙar ji dashi ya durƙushe, akodayaushe sunan companyn ƙera abayas na SOORAJ dake Dubai ne ke yawo ƙasashe ƙasashe ba nasa ba kamar yanda yakeso, SOORAJ yasashi ya rasa abubuwa da yawa, ciki kuwa harda yarinyar dayake fatan kashe ƙishin ruwansa akanta, saboda haka baya tunanin zai iya barin SOORAJ ya rayu cikin duniya.
SOORAJ kuwa ganin ya kusa shigowa cikin unguwar tasu ta maitama ne yasanyashi ɗan ƙara gudun motar, daidai zaisha wata kwana batare da ya kula ba wata mota tayiyo kansa da gudun gaske, shima batare daya taka birkin motar tasa ba yayi kan motar, wani irin karo da sukayine yasanya gaba ɗaya motocin nasu tashi sama, alokaci guda kuma suka faɗo ƙasa, cikin ƴan mintuna ƙalilan gaba ɗaya motocin suka fara fitar da hayaƙi.
ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
     *SOORAJ!!!*
   *Written By*
Phatymasardauna
*Dedicated To My Life (Sardauna)*
          *Wattpad*
      @fatymasardauna
#romance.
*(Gabaki É—ayan wannan fejin sadaukarwa ne agareka HAMEED, ina maka fatan farinciki me É—orewa a iya ka tsawon rayuwarka.!â£ï¸)*
       *Chapter 53*
Sosae duka motoci biyun ke fitar da hayaƙi, kasancewar ba kaɗan ba motocin sukayi mummunan buguwa, hayaƙi ne ke cigaba da fita sosai ajikin motar kowannensu,  cikin matsanancin sauri, haɗi da gaggawa, ƴan sandan dake gadin area'n, suka taho domin bawa waƴanda ke cikin motar taimakon gaggawa, domin kuwa nanda wasu lokuta idan wani bai taimaka ba, lallai gaba ɗaya motocin zasu iya kamawa da wuta, cikin sauri da dabara haka ƴan sandan nan suka shiga ƙoƙarin fito da kowannensu daga cikin motar, gaba ɗayansu babu wani wanda yake da alaman numfashi ajikinsa, gaba ɗaya jini ya ɓata fuskokinsu, har takai ga baka iya tantance kamanninsu,  Ambulance ƴan sandan suka ƙira take cikin ƴan mintuna ƙalilan aka zo aka kwashesu dukansu, Kaitsaye babban privet hospital ɗin dake cikin garin Abuja wato Nizamiyye Hospital aka nufa dasu.
Direct Emergency aka wuce dasu, lokaci É—aya aka soma basu taimakon gaggawa.
Zaune take akan stool ɗin dake aje gaban dressing mirror, sanye take da towel ajikinta, yayinda jikinta ke ɗauke da danshin ruwa, da dukkan alamu fitowarta daga wanka kenan,  ahankali take murza sassanyan body lotion ɗinsa mai daɗin ƙamshi ajikinta, harwani ɗan lumshe idanu takeyi, saboda sosai ƙamshin body lotion ɗin keyi mata daɗi, har takai tanajin batason daina goga maiɗin ajikinta, koda ta kammala sama sama ta shafa powder akan kyakkyawar fuskarta, wani ɗan light pink lipstick ta goga akan ƴan madaidaitan laɓɓanta, black eye pencil ta ɗan goga acikin idanunta, mascara tasanya taɗan taje eyelashes ɗinta, take suka ƙara mimmiƙewa sukayi zara zara dasu.
Kallon kanta tayi amadubi naɗan wasu sakanni kana ta lumshe idanunta, moment ɗinsu na ɗazu ne kawai ke yawo acikin brain ɗinta, sosai takejin daɗin kasancewa dashi, domin aduk sanda take tare dashi takanji wani abu na musamman na yawo cikin jikinta.
Ahankali ta tashi daga kan stool ɗin inda ta nufi gaban babban drawer ɗinsu, ɓangaren kayanta ta buɗe inda ta zuba musu ido, tunanin wanda zata saka take, nan dai ta zaro wata doguwar rigar atamfan ABC, wanda take da kalan blue wato shuɗi, sosai zanin keda kyau, yayinda aka shumfuɗa mata wata haɗaɗɗiyar straight gown me kyaun gaske, rigar irin doguwar nance, sosai kuma aka fitar da shape ɗin ta, yayinda gefe da gefen rigar dama da hagu suka kasance atsage, tun daga ƙasa har gefe da gefen cikinta abuɗe suke, wani dogon pencil crazy jeans ta sanya, tare da ɗaura tsagaggen doguwar rigan akai, sosai tayi kyau, musamman yanda haɗaɗɗen shape ɗinta ya bayyana ta cikin tsagun rigar, dayake jeans ɗin yakama jikinta sosai, parking dogon gashin kanta tayi yayinda ta naɗeshi a tsakiyar kanta, wani ɗan madaidaicin blue vail ta yafa akanta, wanda ya kawo har kan cikinta, sosai tayi kyau cikin shigarta ta, ƙarasawa gaban mirror tayi tare da ɗaukan body spray ɗinsa mai daɗin ƙamshi, wanda akullum ƙamshinsa ke ƙara zautar da ita ta fesa ajikinta, wani flat shoe tasanya aƙafanta, cikin nutsuwa ta murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ta fice, kaitsaye ɗakin da zai sadata da babban falon na Oummu ta nufa, taku biyu ya rage mata taƙarasa zuwa cikin falon taɗan tsaya, daidaita nutsuwa haɗi da tafiyarta tayi, sannan ahankali tatura ƙofar falon ta shiga bakinta ɗauke da sallama.