Sashe 9
Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
da aka yi jiya." Abhi ya ce "To Allah i tsare, Allah i yi maka Albarka yaron kirki; kai Malam Hamza maza a je a zo min da Iyayen naku da sauran an uwa." Ya arasa maganar ya na duben inda Hamza yake. "To" Hamza ya ce sannan ya bi bayan Akhiee su ka yi hanyar fita. Cike da takaici ya ce "Amma kai anyi munafuki wallahi, ka iya arya kamar an duba, ka je ka yi kashe-kashe amma ka ce masa ka je gona." cikin acin rai Akhiee ya ce "Ba babban munafuki sama da kai da ka ke shirin fa a masa abinda zuciyarsa za ta buga, su fa iyaye kalamai masu da i ake gaya musu wanda hankalinsu zai kwanta, amma sabida ba ka san darajarsu ba za ka gaya masa abinda zai tashi hankalinsa, kuma na rantse da ubangijin Al'arshi idan aka samu wani ya gaya masa ainahin zahiriyyata har wani abu ya same shi sai na kashe kowaye ya fa a, ba alwashi bane al awari ne kuma zan cika indai an sa a min." Cikin acin rai gami da tsana Hamza ya ce "Banza mara kunya, sai ka kashe in in ran a hannunka yake" "To an masu da kunya, ni lokacin da aka raba kunyar ban zo duniya ba, idan ka damu da in yi kunyar sai ka ban taka" Hamza ya ce "Allah i sauwa e!" Akhiee ya ce "Zancen banza, da kunyar ba ta isheka ba kake tallar ta? ai da ta isheka sai ka eba min taka, gaso-rogo kawai" daga haka Bai bawa Hamza damar ara yin magana ba ya yi gaba cike da ba in ciki da takaicin irin yama da iyayyar da an uwan nasa suke nuna masa. IP Khalil na zaune kan kujerarsa ya kifa kai akan teburi ya na hucewa, kansa duk ya gama aukar zafi, wani mugun unci da damuwa yake ji kamar zai ha iyi zuciya ya mutu, Risslan ya gama aure masa jijiyoyin jikinsa, ya je ya yi kashe wancan ya kashe wancan gashi ya one motar ogansa, sai umarni yake samu daga sama na kawo arshen Risslan, babban tashin hankalinsa bai san menene raunin Risslan in ba bare ya yi masa illa, a yadda yake a rayuwarsa ba wani abu da ya zamo rauni a gareshi. Har baccin wahala ya fara aukarsa wayarsa ta tashe, ya ago idanunsa da su ka koma kalar ja ya zubawa wayar, ganin Hajiya Laure ce ya sa shi agawa don ya bata ha uri ma ta dena takura masa. a masife ta ce "Kai IP Khalil na gaji da gafara Sa ban ga aho ba, ina labarin wanda ya kashe mini Miji??" shiru ya yi mata don kuwa bai san me zai ce mata ba ya ji yau da bala'i ta hauro. "Tambayarka na ke yi fa??" Numfasawa ya yi sannan ya arta ya ce "Hajiya mun fi ki son mu ga mun yi aikinmu, amma ba mu da halin hakan, ki yi ha uri mu na nan mu na ara bincike akan lamarin, wanda mu ka kama kawai zargi ne ba mu da hujjoji warara, amma da yardar Allah komai zai yi daida...." "Dakata Ibrahim!!" Hajiya Laure ta fa a cikin tsawa, orawa ta yi da cewa "Na gaji da yaudarar nan da kake yi mini, yanzu na au haske na fahimci komai, ai bakinku aya da kai da makasan dama, to wallahi da kaina zan auki mataki, yanzu ba na bu atar temakonka, don me za ka ce ba ka da hujja bayan ka san wanda ya aikata har ka kama shi sabida bakinku aya sai ka sake shi, shine fa ya ba unci mijina a ranar da aka kashe shi, to in ba shi ba waye zai yi kisan?" IP Khalil zai yi magana ta katse shi da cewa "Kar ka gaya mini komai!! ba na son ji, na ha ura da temakonka ka je ka yi Allah na nan kuma ku in da na biyaka Allah ya isa, ni zan bi ta wata hanyar in auki fansar mijina, wallahi tallahi sai na jefa wannan yaro cikin bala'in da sai ya kashe kansa, kai kuma ta Allah ba taka ba munafukin banza" ta na kaiwa nan ta katse wayar ta na huci. IP Khalil ji yake tamkar ya yi ta bin layika da kwararo ya na zunduma ihu ko zuciyarsa za ta yi sanyi, nan take wani mugun zazza i da ciwon kai na wahala da tarin tunane-tunane su ka lullu e shi. Huci Hajiya Laure ke yi kamar bujimin sa ya ga wu ar yanka shi, Yazeed da ke zaune gefenta ya ce "Shima munafuki ne an sandan nan ko??" "Yo eh mana, in ba haka ba ta ya za ka kama mutum ka sake shi bayan ka san shi ya aikata, wallahi zan auki mataki akansa nan ba da da ewa ba, je ka fito mini da mota fita zan yi." Yazeed ya mi e ya na cewa "Amma da kin bari kin gama takaba sai ki yi ko me za ki yi." "Ubanka!! na ce ubanka kai da takabar! kamata ta yi ace ka fi ni damuwa da mutuwar ta shi amma sabida kai butulu ne duk wannan so da aunar da yake nuna maka sai ka ce in bari in gama takaba? to kai da takabar na ci buhun ubanku, an butar duma kai?" "Allah i bada ha uri" ya fa a cikin sanyi sannan ya fita domin gyara motar da za ta fitan. SHARE FISABILILLAH Na Ku i ne.... Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba. VIP 500 Posting Kullum. domin arin bayani 09079885632 INDO* [8/14, 8:18 PM] INDO: * SAHUN KEKE Ep 9