Sashe 34
Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ayeesha Abdulkareem INDO *Wannan shine Last Free Pages* LAST FREE PAGE Da sauri ta ago ta zuba masa blue eyes inta ta na murmushi me matu ara mata kyawu da jan hankalin me kallonta, cikin sassanyar muryar da ke ara sa shi fita daga hayyacinsa ta ce "Indai da gaske ka ke ka yi min Al awarin za ka kasance tare da ni har abada, kuma za ka rabu da wadda ka Aura." idanunsa ne su ka ara girma, tamkar aradu ta rikito masa aka haka ya ji saukar kalaman nata, la ansa har karkarwa su ke yi wajen cewa "Impossible! Razia idan ki ka rabani da Asma'u tamkar kin rabani da garkuwar rayuwata ne, ban na son rabuwa da ita kuma ba na so ta cutu, akanta na shiryawa komai ko da mutuwa ce, ta na da muhimmanci a rayuwata kuma kema ki na da shi, zan so ku rayu a ashin inuwa aya ba tare da cuta da cutarwa ba." "Ba zan iya ha a Mijina da kowace iya ba, kuma ma ka rasa wadda za ka ha ani kishi da ita sai Bil-adam, ba ka nemi zaman lafiya ba, kuma ka na ji ka na gani zan kasheta ko kuma na nakastata!!" Ta yi maganar a fusace. zafi da una kawai Zuciyaraa ke yi, ture ta ya yi daga jikinsa gami da juya mata baya cikin acin rai ya ce "Tinda na fahimtar da ke kin kasa fahimta zan auki tsatstsauran mataki akanki da zarar kin cutar da ita, ko meye ya sameta ki sani zan ninka shi akanki, ko kasheta ki ka yi sai na yi miki azabar da za ki gwammace ke ma mutuwa ki ka yi, tinda na gaya miki gaskiya kin kasa fahimta." Ta na shirin yin magana Russlan ya diro a wajen, ransa a matu ace, ya na sauka ba tare da wani tunani ba ya ame kwari-da-bakar hannunsa ya na shirin harbawa Razia, wani gwauron tashi Akhiee ya yi ya dira a kansa ya bangajeshi su ka fa i can gefe su ka fara mulmulawa kamar wallo, cikin sa'a Akhiee ya yi nasarar wace kwari-da-bakar ya yi wurgi da ita zuwa gefe, rai a ace ya ce "Me ta yi maka?" Russlan ya tunku eshi gefe sannan ya mi e ya na cewa "Sabida ta raina mutane a dinga fa a mata magana amma ita kamar shai aniya? yanzu gashi ta sa Uban Dawa sai fa a ya ke yi mini a ganinsa ko me ta yi laifina ne, gwara kawai na harbeta mu je mu yi jinya da wannan fitinar ta-ta." Dogon tsaki Risslan ya ja kafin ya ce "Amma ai Matata ce ko? kuma wurina ta zo ba wani wurin ta tafi ba." "Waye ya bata izinin fita to? kawai ka yaleta ta kar i hukuncin abinda ta yi, ka riga ka san halinta kaima. "Ba fa zan bari ka cutar da ita ba, laifi na yi mata kuma ta na da right in da za ta nuna acin ranta, ka je kawai zan dawo da ita da kaina." Cikin takaici Russlan ya ce "Sai ka amsa Kiran Father kai ma nemanka ake yi." Daga haka ya tashi sama ya basu wuri. Akhiee ya maida kallonsa kan Razia da ke dur ushe ta na kuka magashiyyan, a hankali ya taka zuwa gabanta ya dur usa, tausayinta ya cika masa Zucuya taf, cikin tattausar murya ya ce "Razia! gardamarki ce ta sa ki ke fuskantar acin rai a kodayaushe, ba kya jin magana gashi ba kya aikata abu me kyau, Lokacin da za'a antaki ya kusa amma a bisa wannan laifin da ki ka yi na san dole Uban Dawa Zai ara miki lokaci, ba kya kiyaye acin rai, ba kya aukar shawara, ni a yanzu ba zan iya yin komai a kai ba don nima hankalina ya fi kwanciya idan aka killace ki, fitinarki ta yi yawa musamman a yanzu da ki ka ara burkicewa, ki tashi mu je." Ba ta iya cewa komai ba sai kuka, Zuciyarta tamkar ta tarwatse, ji take da Allah zai ha ata da Husnee a yanzu ba abinda zai hana ta kasheta in yaso sai ayi mata auri me dalili. Hannunta ya kama su ka ace daga wurin. A Fadar Uban Dawa su ka sauka, yayinda Da yawa daga cikin ahalinsu sun taru a wurin su ka ai ake jira. Russlan da Arsalaan da Hidaya da sauran yara su na dur ushe a gaban Tafkeken gadon Sarauta na Uban Dawa, anan Razia da Risslan su ka dur usa su na mi a gaisuwarsu. Sai da lokaci ya an ja sannan Uban Dawa ya yi gyaran murya ya fara da cewa ''Risslan Labari ya iso mana na cewar ka Auri wata ar Bil-adam ba tare da iyayenta sun Amince ba, meye dalili?" Da sauri ya ago kansa cike da tsoron ta yadda Father zai Kar i Abin, Mother ya kalla cike da son warin guiwa daga gareta, ta sakar masa sassanyan murmushinta gami da lumshe idanunta . ar ajiyar Zuciya ya sauke gami da yin asa da kai ya ce "Sabida ta na sona ne, kuma idan ba na tare da ita komai zai iya faruwa da ita, shi yasa na yi hakan, a gafarceni Father." Uban Dawa ya jinjina kai cikin dattako gami da manyance ya ce "Ba ka yi tunanin hakan akwai kuskure ba?" "Ba na tunanin akwai kuskure a ciki, amma ban sani ba ko kun hango abinda ni ban hango ba." Father ya yi murmushi hakan ya sa duk sauran na wajen su ka murmusa, cike da auna da kulawa ya ce "Kar ka sake wani ya rabaka da Ita, nima zan so ganinku tare." Da sauri Razia ta ago rinannun idanunta ta zubawa Uban Dawa gami da cewa "Father!!" cikin ka uwa da tashin hankali. Oum Razia ce ta yi saurin tarar numfashinta da cewa "Kul!! kar ki ara sako baki cikin maganar manya." Uban Dawa ya ce "Razia ba sai kin neme ni ba ni zan nemeki da kaina domin kin yi mini laifi, indai fa ba za ki koyi jin magana ba to ba za ki dena kar ar hukunci ba, Yanzu kin ninkawa kanki Shekaru a ashin Hukunci, Arsalan maza a maida ita." ya arasa maganar ya na kallon inda Arsalaan ya ke Razia ta ara rushewa da wani azababben kuka ta na magiya gami da bada ha uri, amma ba wanda ya ce uffan har shi wanda ya yanke hukuncin, Akhiee kuwa rintse ido kurum ya yi don kuwa sam ba ya jin da in kukan nata. Cikin sanyin jiki Mother ta ce "Father! don Allah a yiwa Razia afwa, wani lokacin Zuciya ce take ru arta da aikata abinda ba daidai ba." "Idan ba a nuna mata kuskurenta kuma ta yaya za ta fahimci yadda rayuwa take??, idan ta gama hankalta babu me ara hukuntata; idan akwai wanda zai yi magana ana saurarensa." ewa Akhiee ya yi gami da cewa "Ni kam zan fita ana nemana." Da kai kowa ya amsa masa, sannan ya fice. Hajiya Laure Yau har agara ta yi gari ya waye Sabida mafarkin Boka Barore da ta ke yi, ko ta farka da zarar ta koma sai ta ci gaba. Tin arfe bakwai na safe ta auki waya ta turawa Hajiya Saudah kira, a angaren Hajiya Saudah ma wayar ta na hannunta ta na shirin kiran Hajiya Laure ta sanar mata, cikin sauri ta auki kiran gami da kara wayar a kunnenta ta na cewa "Hajiya Laure kema kin yi mafarkin ne?" Hajiya Laure ta ce "Hmm! na yi manaaa,, ba me da i ba ma kuwa, ai ni gaskiya mu shirya tin wuri mu je mu ji abinda zai ce don wallahi a tsorace nake." "To ai nima dai hakan take a nawa angaren, har na ji ma ina tsoron zuwa wallahi don mafarkan da na yi ba kyau" Hajiya Saudah ta fa a murya asa- asa, da sauri Hajiya Laure ta ce "A'ahh! da ke mu ka je da ke za mu koma, ni kinsan ba sanin kan abinsa na yi ba, ko hanyar ba lallai in gane ba, kar kuma mu i komawa ya yi mana wani mugun abin, don na lura azzalumi ne" ta arasa maganar cikin nuna tsoronta a sarari. ulululu!!!! cikin Hajiya Saudah ya ara juyawa, jiki na ari ta ce "Kuma fa haka ne, to ki shirya mu je da wuri." Da sauri Hajiya Laure ta ce "Ai tuni na shirya dama ke ka ai na ke jira, na fa cika da tsoro wallahi. Hajiya Saudah ta kasa cewa komai sai ma katse wayar da ta yi ta na sauke wani gwauron nishi, yau aya dai ta yi danasanin raka wani wajen Boka Barore. Dolenta ta shirya, Hajiya Laure ta zo ta zabareta su ka yi gaba, cikin su biyun ba a bambance wadda ta fi shiga tsoro da firgici. Muddassir na cikin driving kamar an tsunkuleshi ya gangare Motar gefe ya tsaya, wayarsa ya zaro ya lallatsa ya tura kira: Sai da na farko ya katse wani ya shiga sannan aka auka, Bakinsa har karkarwa ya ke yi wajen cewa "Oga Dazginabu ina cikin tsaka me wuya fa". aya angaren Dazginabu ya yi magana cikin kakkausar muryarsa wadda ta ke nuni da rashin imani da tausayi da bushewar Zuciyarsa, "Me ya faru??" "Sahun Keke ya auri anwata, kuma wadda na fi auna, ban san yadda zan yi ba wallahi" "Hhhhhhhh!!" ya shiga ala dariya irin ta mugayen mutane, Maddassir dai ya na saurarensa har ya yi me isarsa sannan ya tsagaita ya ce "Kar ka damu Mafaraucina, wannan dama ce ta zo mana wadda za mu ara wasa walwarsa, za mu dinga yi masa abinda bai yi tsammani ba kuma ba zai ta a zarginka ba, yanzu ko me mu ka yi masa ruwa ta sha, zai dinga kallonka a matsayin yayan Matarsa, yayin da mu kuma za mu dinga cin dunduniyarsa, ka ga ranar nan ya kashe jama'ata to yanzu tinda haka ta faru ka ci gaba daga inda ka tsaya ni kuma zan dinga tura masa wasu domin kawar da hankalimsa daga kanka." an tsagaitawa ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Ina Fatan kisan da aka yiwa yaran