Sashe 31
Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ayeesha Abdulkareem INDO *M.W.A Cikin tausasawa ya ce "Kwantar da hankali Mukhtar! Lokacinta ne ya yi ba yadda za mu yi dole sai mun rasata ko ba ta wannan hanyar ba, bai kamata ka yi kuka ba; kamata ta yi ka rarrashi annenka, kai fa Namiji ne, ba na son ara ganin hawayenka, ka bar komai a hannuna kuma ka manta da abinda ya faru ina so komai ya wuce." Mukhtar ya ja numfashi ya sauke kafin ya ce "Amma ba yadda za mu yi haka za su dinga yi mana?" "Ta ya kake tunanin wani aramin abu zai dawwama a Duniya?? lokaci juyawa ya ke yi, Ka kula da annenka a shirya jana'izar Zakiyya kafin na iso." Daga haka ya katse wayar ya yi wurgi da ita ta fa i can gefe, safa da marwa ya shiga yi a wajen ya kai mari ya kai gwauro, duk iya nazarinsa ya kasa gane kowaye yake yi masa wannan zagon asan, kuma ya na bu atar sani tin kafin tafiyar ta yi nisa. Ya da e cikin yanayin tunane-tunane kafin ya shirya domin zuwa wajen Jana'izar Zakiyya. Husnee jiki a sa ule ta sauke wayar daga kan kunnenta ta na kallon Amadu kallon da ya ke nuni da cewar bai barta ba, Ya kalli Ahajiji Me Gadi ya ce "Ahaf!!! Allah na tuba Shu'umin Mutum irin wannan Yaron ne zai bar matarsa ta dinga yawo a gari? ai shi yasa na yi azancin cewa ta Tambayi Mijinta." Alhajiji ya ce "A'ah iko sai Allah, to ni na kasa gane me kuke nufi ai, ba ku ga tin azu na ke kallonku aya -bayan- aya ba Ni ai a sanina Husnee ba ta da Miji." Amadu ya ce "Na shafa maka lafiya to yanzu Matar Aure ce, ga shi dai a gabanka ai ta tambayi mijin nata fita ya hanata" "Matar Aure??? Mijinta kuma?? ita Husnee in???" Mommy da ta iso wurin ba tare da sun sani ba ta jefo musu tambayoyin a jere. Rassss Gaban Husnee ya yanke ya fa i har asa, jikinta ya fara karkarwa ta zazzaro fararen idanunta akan Mommy wadda ta ke kallonsu ita da Amadu aya-bayan- aya kallo me cike da tuhuma gami da mamaki da acin rai. Amadu ya ji tamkar Motar Gingimari ta hau kansa lokacin da ya ji tambayar Mommy. Lokaci guda duk su ka shiga firgici da tashin hankali. a ladabce Alhajiji ya ce "Hajjaju Makkatu ikon Allah barka da fitowa." Mommy ta ce "Ba ka ji tambayar da na yi ba ne? shine ka ke kawo mini taka idea?" Ya rissina gami da cewa "Ayi ha uri, wallahi Hajiya nima yanzu na ke tambayarsu yaushe ne ta yi aure ban sani ba, Allah i sanya Alkairi." Cikin tsawa Mommy ta ce "Husna!!! Dan Ubanki ba kya jina ne???? yaushe ki ka zama Matar wani????" zamewa ta yi ta dur ushe a wajen gami da fashewa da wani marayan kuka wanda sautinsa ma ya ba ya fita sosai, ta na so ta magantu amma ta kasa. Jiki na tsuma Amadu ya ce "Ina zuwa Hajiya" cikin Mota ya nufa ya auko ku in Sadakinta wanda ke nanna e a cikin hankicif, ya dawo gaban Mommy ya dur usa jiki na ari ya ce "Hajiya Allah ya baku ha uri, Ga wannan" cikin mugun mamaki ta sa hannu ta kar a ta na arewa hankicif in kallo, Amadu ya ci gaba da magana murya na rawa "Hajiya wa annan ku i su ne Sadakin Husnee, Jiya Wanda take so ya aureta, Hajiya ba laifina ba ne, Tilasta mini ya yi akan cewar ni zan kar i Aurenta, mun aura Auren a Masallacin wani Malami, Malam Kabiru" iya abinda aka yi a gabansa ya kwashe ya gaya mata. Kallon Husnee ta ke yi cikin tsananin mamaki da al'ajabi, ta na yi ta na jinjina ku in hannunta. Cikin murya me nuna tsantsar acin rai ta ce "Husnee? har kin yi girman da za ki iya bin wani an iska ya aureki? Ashe duk burin Mahaifinki na ki yi karatu me zurfi ba ya cikin tunaninki?" Girgiza kai ta ke yi ta na wani irin kuka wanda ke fitowa tin daga asan Zuciyarta, murya a dishe ta ce " addara ce Mommy don Allah kar ki zargeni sam ba laifina ba ne, nima ban zata abinda zai yi kenan ba." Amadu ya ce "Gaskiya ne haka ne Hajiya ita ma ba ta zata ba, sama taka ya aikata hakan" "To wai shin waye shi ? Su waye iyayensa a asar nan da har zai aure mini a ba tare da Sahalewata ba??" Amadu ya ce "Ranar wanka ba a oyon cibi Hajiya, Sunansa Muhammad Risslan Sheikh Muhammad Risslan, a ne ga babban Malamin nan na duk Hotoro da kewaye, kuma shi in Babban Tantiri ne na kaf Nigeria, wasu na kiransa SAR A wasu na kiransa SAHUN KEKE, kowa ma da irin sunan da yake gaya masa, ko kwanakin baya an kamw shi da laifin kisa amma sai aka sako shi domin ya fi gaban nan, wannan shi ne ka ai abinda zan iya fa e a kansa." Duhu-duhu Mommy ta fara gani nan take jiri ya fara ibarta ta tafi luuuu!!! za ta fa i Husnee ta yi kanta da gudu da nufin tareta, kafin ta arasa Muddassir ya rigata, ya rungumota a jikinsa ya na tambayar lafiya. Hawaye ne su ka shiga tsiyaya akan kumatunta, da kyar ta ce "Husnee ce!!! mu na zaune a gida ashe ta je ta Auri wani bayan mun yi wa Zaheer Al awarin aurenta, wai yanzu har ta yi girman da za ta iya zuwa ta Auri wani Namiji ba tare da sanin iyayenta ba?? har yaushe ta fara zuwa makarantar da ya hure mata kunne haka?" Muddassir ya zubawa Husnee ido ya na binta da kallon tuhuma, a masife ya ce "Ashe ba ki da hankali? me ya sa za ki aikata haka? akwai wanda ya fiye miki iyayenki ne duk son da ki ke yi masa? Kwantar da hankalinki Mommy kowaye sai ya saketa ni zan je in yi magana da shi, mu ba za a yi haka da mu ba, ba ma son tantiranci." Mommy ta ce "Shi in Tantirin gaske ne kuwa, kuma Shai ani wai Sunansa Sahun Keke" dimm!!!!!!! Zuciyar Muddassir ta yi wata muguwar bugawa wadda ta sa numfashinsa aukewa na wucin gadi. "SAHUN KEKE!!!!!!" Ya maimaita kalmar cikin ka uwa gami da tashin hankali da firgici. idanunsa na kan Husnee wadda take wani irin galabaitaccen kuka, a hankali ya ce "Mommy shiga ciki ina zuwa." Mommy ta ja jikinta da kyar da kyar ta shige cikin gida ta na kuka ta na fa in "Ai ko waye shi, Allah i sa Iblis ne sabida hatsabibancinsa sai mun yi shari'a da shi sai ya saketa, ba za ta ta a zama da an Ta'adda ba." A ki ime Muddassir ya matsa kusa da ita ya dur usa a gabanta su na fuskantar juna, cike da son tabbatar da abinda kunnensa ya jiye masa ya ce "Da gaske ne Kin zama Matar Sahun Keke???" cikin shashshekar kuka ta ce "Amma ba laifina ba ne don Allah ku yi ha uri kar ku yi fushi da ni!!" jinjina kai ya yi cikin wani irin yanayi na tashin hankali da ya riske shi, "Husnee ki na nufin Sahun Keke ya na sonki ne ko kuma ya yi hakan ne kawai don wata manufar? ke ma ki na son shi ne? a ina ki ka ha u da shi??" A jere ya zubo mata tambayoyin cikin ki ima. ba tare da ta dena kukan ba ta ce "Ba don wata manufa ya yi ba, sabida ina son shi ne ya sa shi yin hakan, don Allah Yaya kar ku rabani da shi ni ina son shi a haka duk da irin halayensa." Muddassir tamkar zai fashe da kuka ya ce "Duk fa in Duniya Husnee ki rasa wanda za ki so sai wanda bai auki ran Mutum a bakin komai ba?? anya kuwa kin yi tunani? yanzu an da za ki haifa ya sunansu?? ki temaka mana ki temakawa kanki ki rabu da shi." kai tsaye ta ce "Ba zan iya ba Yaya!!! ba yin kaina ba ne Allah ne ya jarrabeni da son shi, so me tsanani wanda na ke jin tamkar shine bugun Zuciyata Yaya!!!" ewa ya yi ya na bubbugar kansa da ya gama hautsinewa gami da juyewa, yarfa hannunsa ya yi ya na cewa "Kaih!!! Impossible ta ya-ya zan bari ya auri anwata??" No ba zai yuwu ba!" ya yi maganar tamkar wanda ya fara zaucewa, kamar an tsikare shi ya zabga da gudu zuwa cikin gidan. Husnee ta mi e ta na ingisa afa da yar fa yar ta bi bayansa. Ya na shiga ya Zauna kusa da Mommy ya na cewa "Mommy ta ya-ya kenan? Ta ya Auren Husnee zai halatta ga wannan an ta'addan, ya zama dole mu auki mataki!!" Mommy ta sa an hankicif inta ta fyace hanci sannan ta ce "Ai na kira kowa da kowa na sanar musu abinda ya faru, kwantar da hankalinka dole ne a raba Auren nan indai da gaske ne an aura shi." Da sauri Muddassir ya ce "Yess ta yuwu ma ba a aura ba, ba ri in je in tambayo wanda ya aura in ko arya su ka yi mana." Bai jira ta ce komai ba ya fice da gudu kamar aramin yaro, Amadu ya tambaya bayanan wanda ya aura Auren Amadu ya gaya masa komai, nan ya zabare shi da sunan ya raka shi wajen Malam Kabiru. Husnee na tsugunne gaban Mommy ta na kuka ta na neman yafiyarta amma sam ta i ko da kallonta, Wayar Mommyn ce ta fara ruri Ta auka gami da sa hands free yadda Husnee za ta ji ko me za a ce, Daddy ne ko sallama bai yi ba ya fara surfa fa a ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, da Mommy ta gaji sai ta ce masa ga Husnee in ta mi a mata wayar ta tashi ta bar musu Parlorn. Ba Irin kuka da magiyar da Husnee ba ta yiwa Daddy ba amma ya kanne