Sashe 36
Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta dinga kiwon Mommy da Amadu. Ta na samun dama kuwa ta zumbu a Hijab ta fice, kai tsaye ta nufi Makaranta duk da cewar da ar tazara tsakanin yankinsu da yankin makarantar amma yau ba ta bu atar a kaita a Mota don ta san Direban nata zai hanata fita. Ta na cikin tafiya Tankar Ya i da Tawagarta su ka sha gabanta. Ta na sanye da wani mugun amammen wandon Jeans blue wanda aka tsatstsaga wajen guiwarsa sabida tsabar gayu, rigar kuwa ta ciki fara ce sol itama ta mugun kama jikinta sai jacket da ta ora ita ma ta jeans, sai farar bandana wadda iyakacinta goshi, tsefaffen gashinta wanda ke ta zuba yalli ya yi watsa-watsa kowanne ya kama gabansa, hannunta aya a Aljihun riga ayan kuma ya na kusa da bakinta ta na zu ar Wiwi ta na busawa. Wani irin taku ta ke yi me cike da izza, zarra, jin kai, asaita, tamkar ita ce Queen Elizabeth. Husnee ta kallesu aya bayan aya ta ga zaratan arti sai zaro mata na mujiya su ke yi su na huro mata hancika tamkar bujimayen shanu, Zuciyarta ce ta fara tsallle tsoro da razani da firgici ha i da tashin hankali su ka kawo mata ziyarar bazata. JanKai ne ya kalli shugabar ta shi cike da agarar aiwatar da mugun aiki akan Husnee ya ce "Ya kika ce Zinaru! mu hau kanta ne ko kuwa??" Jin haka ya ara aga hankalin Husnee idanun nan nata kamar an danne tinkiya za'a yanka sun firfito waje tsuru-tsuru, Tankar Ya i ta busa haya i a asaice ta ce "Saurin me ka ke yi, ku kawo mini ita nan." Ta na fa en haka su ka nufi inda Husnee take dama a tsakiya su ka sata, ba tare da tunanin ita mace ce su maza ba haka su ka cicci eta ta na ihu ta na komai su ka direta a gaban Tankar Ya Zabgegiyar wu arta me kama da Adda ta kar a a hannun Jankai ta goge ta sannan ta zubawa Husnee idanunta da su ka koma launin ja, cikin murya me unshe da manufofi da dama ta ce................................. Akhiee, an-Bakwai ne ya mi o masa wayarsa da take ta tsuwwa, ya kar a bayan ya aga kiran ya sa a saman kunnensa, a aya angaren me kiran ya ce "Ni ne dai Abokin gabarka Inspector Khalil, ina zarginka da aikata kisan kai na wasu an Yara guda biyu bayan ka yi musu Fya e kai da yaranka, ba wanda zai aikata hakan sai kai." Cikin Nutsuwa Akhiee ya ce "Aikin ne ka rasa da za ka biyo ta bayan gida kuma?? Ka san ina yin arna da yawa, ko za ka iya yi mini arin bayani?" "Sunan aya Zakiyya aya kuma Farhana, an tsinci gawarsu kuma bincike ya nuna sai da aka yi lalata da su sannan aka kashe su, aya a ciki ma har da ule mata ido, Ba wani kwalo-kwalo da za ka yi mini na san kai ne ka aikata, kuma mu na nan mu na ara bincike akanka." Akhiee ya ja tsaki kafin ya ce "Shashashan banza". A fusace IP Khalil ya ce "I'm Police fa ni zaka gayawa maganar banza? wallahi ka guji shigowa hannuna sai ka gane kurenka wallahi, har ni za ka cewa shashasha?? I will arrest you wallahi" i da Hausa" Akhiee ya fa a cikin salon rainin hankali, ai kuwa IP ya ara haurowa da Masifa da fa e-fa e ta inda yake shiga ba ta nan ya ke fita ba. Sai da ya gaji ya yi low sannan Akhiee ya ce "In kun shirya kamani in ina jiranku da kai da iyayen gidan naka, in ka tashi zuwa ka tawo da IG ma." daga haka ya katse wayar ya na mamakim Sharri irin na an-adam, an kashe masa Mutanen sannan za a ora masa sharrin aikatawa. Waya ya auka ya kira Rahma don jin Halin da Farhana ta ke ciki don ya san in su ka gane ta na raye ma wata sabuwar gwaramar ce. Rahma ta na agawa cikin Muryar kuka ta ce "Dama yanzu na ke son kiranka an Manya" ''Why" Cikin dauriya ta ce "Ita ma Farhana Allah ya yi mata rasuwa". "What?? Farha is dead??" ya fa a cikin ka uwa da razani. Sake fashewa ta yi da kuka ta na cewa "Yes! kuma na yi imani da Allah ita ma ha a baki aka yi da Likitoci su ka kasheta................ LAST FREE PAGES (Mutanen Akhiee da na Husnee zan gani ko zan iya idaya adadin aunar da za ku nuna musu ta hanyar jin labarinsu har arshe ARSHEN FEJIN KYAUTA Na Ku i ne.... Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba. VIP 500 Posting Kullum. domin arin bayani 09079885632 LAST FREE PAGE INDO* [9/5, 5:29 PM] INDO: * Ep 21 Shiru ne ya ratsa tsakani na an lokaci kafin ya numfasa, cikin tattausar murya wadda ba ta bawa me saurarenta damar fahimtar halin da yake ciki ya ce "Shi kenan Zulaihart ki dena damun kanki, ko ma waye Allah ya na kallonsa, ko da ba mu yi masa komai ba Allah zai hukuntashi a bisa laifinsa" an tsagaitawa ya yi kafin ya ci daba da ce "Ba lallai na samu halartar Jana'izarta ba; ki Fa awa Inna ba na so ananun Yaran nan su san abinda ke faruwa." Zulaihart ta amsa da "To" gami da ci gaba da kukanta. Ajiye wayar ya yi ya na ci gaba da tunane-tunane, ji yake kamar kansa zai yi tsawa ya tarwatse sabida tsabar ru anin da ya shiga. Wata muguwar bugawa Zuciyarsa ta shiga yi, wadda ke tabbar masa ba lafiya ba, karaf Husnee ta fa o masa a rai, idanunsa ne su ka ara girma sabida razani. Daidai lokacin aya daga cikin Dakarun Aljanunsu ya araso wajen bayan ya gaishe shi ya sanar masa halin da Husnee take ciki. Rai ace Akhiee ya nufi wajen Tare da Dakare Adnanu. "Yau zan kasheki in huta da acin ranki!!! Shishshigin naki har ya wuce yi masa magana sabida ke mayya ce sai da kika sa ya aureki; yau taki ta are sai dai in na kasheki nima ya kasheni" Tankar Ya i ta fa a ta na zazzarowa Husnee garadan idanunta da su ka ci kwalli kamar a ciki aka ha ashi, Fuskarta sam babu alamun wasa. Zuciyar sai bugun sama da asa take tamkar za ta zillo ta fa asa, sake fashewa ta yi da wani irin kuka me cike da tsoro razani da rashin sanin abin yi ga uwa uba nadamar kuskuren da ta yi na fitowa. Jikinta duk ya auki karkawa kamar ana ka awa an tauri gangi, magiya ta shiga yi mata gami da ban ha uri akan kar ta kasheta, ita kuwa tamkar shai aniya haka ta yi kunnen uwar shegu da ita, Zuciyarta ta riga ta ashe sam ba ta jin wani umi- umin imani bare tausayi. "Rufe mini baki kafin na soka miki wu ar nan a ciki!" ta fa a cike da tsanar Husnee. a memakon ta yi shirun sai ta ara arke baki ta na cewa "Wallahi ba zan kuma fitowa ba don Allah kar ki kasheni ki yaleni ba zan kuma ba." Tasss!!!!! ta wanketa da wani bahagon mari wanda ya sa kukan nata da maganar da takeyi su ka auke a lokaci aya, gabaki aya wutar kanta ta tsaya cak!!, ba ta gama dawowa hayyacinta ba ta ara wanketa da wani zazzafan marin. Husnee ta dur ushe kan guiwoyinta ta na girgiza kanta da ke wata muguwa hajijiya, a take gefen bakinta ya fashe, fuskarta kuwa ta yi kozai-kozai shatin yatsu sun fito ra a-ra a kamar sa yi magana. Cikin rashin imani ta aga wu ar hannunta gami da kaiwa Husnee suka a gefen wuyanta. Husnee ta rintse ido da arfi gabaki aya ta sadda ar, cikin Zuciyarta kuwa Kalmar Shahada take maimaitawa. Caraf!!! ta ji an ri e hannun nata katamau sabida azabar matsar da aka yi masa tamkar ashinta zai tsage. Wata aramar ara ta yi gami da sakin wu ar ta fa Juyowa ta yi a zafafe don ganin wanda ya ri eta, rass! Zuciyarta ta buga yayin da idanunta su ka yi alaragab da na Rislan. Yaranta kuwa su na ganinsa su ka fara gudun ceton rai sai waigawa ta yi ta ga babu su ba alamunsu. Ta rasa yadda za ta yi don haka ta fashe da kuka ta na cewa "Wallahi indai ba ka Aureni ba sai na kasheta na kashe kowa nima na kashe kaina." A fusace ya watsar da ita can gefe ta zube kamar kayan banza, Ko kallon inda take bai kuma yi ba, Jiki na tsuma ya matsa inda Husnee ke dur ushe ta na wani marayan kuka. Cikin zafin nama ya finciko hannunta ta kusa fa uwa amma da yake azamin ri o ya yiwa hannunta sai ta tirje. tatass!! tass!!!!! ya watsa mata wasu lafiyayyun maruka har guda biyu a jere, cikin mugun acin rai da zafin Zuciya ya ce "Ban ce kar ki sake ki fitowa ba?? Na rantse da Allah ko me ya sameki sai ya samu Danginki, na rantse da Ubangijin da ya halicci Duniya akan danginki zan auki Fansa; kuma indai ba za ki ji magana ba to za ki gamu da acin raina." Ido kawai take zarewa domin kuwa zuwa yanzu azaba da tashin hankalin da su ka mamayeta ba za su barta ta yi kukan ba. Jan hannunta ya yi gami da cewa "Mu je na mayar da ke gidan; kin san Allah kika ara fitowa sai ranki ya yi mummunan aci, kuma ni fa ar zan yi nake yi, ba na shan Alwashi, indai na ce zan yi to zan aikata ." ba ta iya amsawa ba shima daga haka bai ara magana ba ya shiga janta kamar kara, sauri take yi iya yinta amma duk da haka sai tuntu e take yi kamar za ta fa i sabida ya fi ta zafin nama. Bai damu da ana kallonsu ba haka ya dinga ratsa layika da ita har su ka dawo ofar gidansu sannan ya tsaya. Idanu ya zuba mata tamkar me yi mata kallon arshe