← Book details Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 47

Sashe 40

Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nema kenan sai dai ba ta da me bata. Cikin wannan yanayin bacci me nauyi ya yi awon gaba da ita. Washegari jirgin su Abhie da Jaafar ya sauka kuma yau ne ranar komawa Kotu. Tinda ya iso ya fara tambayar Akhiee, su Yasayyadi Usman masu jiran ka an suka fara rattaba masa abinda ke faruwa, ga mamakinsu sai su ka ga sam abin bai ata masa rai ba sai ma albarka da yake sawa Auren jin haka ya sa suka ja bakinsu su ka tsuke. Kamar dai ranar nan kowane angare sun halarci Zaman, kowa da nashi Burin a Zuci, duk da sun yi tarayya ta wajen son raba Auren sai dai daga cikin Dangin Akhiee akwai masu son ganin wani mummunan abun ya faru da shi bayan haka. Abinda ya matu aure musu kai, bayan gabatar da an Hujjoji da alabusai d aga bakin Lauyan da ke Kare masu ara kai tsaye Mai Shari'a ya ce "Bincike ya tabbatar da cewar Wannan Aure ya auru, yanzu Husna Matar Muhammad ce shi yake da hurumin sakinta, har sai ya Amince sannan Saki ya yuwu." Turusss! suka yi kowa ya kasa wani kyakkyawan motsi, duk a tunaninsu Kotu za ta raba auren ta arfin tsiya. Ko da aka tambayi Akhiee bu ar bakinsa ya ce "Ni a karan-kaina ba zan iya rabuwa da Matata ba, amma indai ta ce in saketa zan saketa." daga haka ya ja bakinsa ya tsuke. Asma'u kuwa ya jefata a wahala, ta shiga tsitstsilla ido ta na kallonsa ta na kallon Mommy da Daddy har ma da su Muneeb da suke ta yi mata muzurai, wasu zafafan hawaye ne suka shiga tsere akan fuskarta, ta zubawa Akhiee ido tamkar ba za ta ara ganinsa a Dunyar ba............. INDO* [9/7, 8:15 PM] INDO: * Ep 23 Ta da e ta na kallonsa shi kuwa ya i bata damar su ha a ido sai ya yi tamkar bai ganta ba, rintse ido ta yi da arfi kafin ta fara magana cikin rawar murya "Ina son shi! da shi nake so na rayu har lokacin mutuwata, sai da na riga na za eshi a matsayin abokin rayuwata kafin ya Aureni, don Allah kar ku rabamu. Mai Shari'a ya numfasa ya gyara gilashin dake kan idanunsa sannan ya ce "A barwa me Mata Matarsa itama yarinya a Bar mata Mijinta, Kotu ta Amince da Auren Husna da Muhammad, a bisa shara i na ci da sha tufatarwa da sauke ha in iyali duk ya rataya a wuyansa, Kotu ba ta Amince wani daga angaren Miji ko angaren Mata ya tayar da wata hatsaniya akan Hukuncin da ta yanke ba. Daga haka ya bubbuga ar gudumarsa Kotu ta tashi. Cikin asaitaccen takunsa ya fito daga inda yake tsaye, kai tsaye wurinta ya nufa ya kama hannunta ba tare da ya bi takan kowa ba ya nufi hanyar fita daga Kotun, ita dai ta bishi da ido sai azga kuka take yi. Suna fita suka yi karo da cincirindon jama'a har da an Jarida, an zo kallo da samun labarai masu waya na auka su ma an Jarida su na auka. Wani daga cikin an Jaridar ne ya bugi irji ya matsa kusa da Akhiee ya na cewa "Ranka-yada e Minti aya don Allah ka amsa mana tambayoyinmu." Tamkar da dutse yake magana haka Akhiee ya yi masa banza, sai ma wucewa da yayi wajen wata lintsumemiyar Mota me Numfashi, da ka ganta ka san ta manya ce ba ananu ba, nan ma mutane su ka bisu riiiiii don kar a yi ba su. Cikin rawar murya gami da fargaba ta ce "Ina za mu je Akhiee!??" ata ya yi da jikin Motar ya yi mata rumfa ya na zuba mata idanunsa da ke ta she i da walwali, cikin wata sirrintacciyar murya ya ce "Yau tare da ni za ki kwana, ba zan bari ki ara nesanta da ni ba". da Sauri ta ago idanunta da su ka kukkumbura sabida kuka ta jefasu cikin nasa tare da cewa "Akhie...." saurin rufe bakinta ta yi ganin ya rintse idanunsa gami da kamo gefen le ensa ya cije shi da arfin gaske, "Tell me!" ya fa a a ta aice bayan shu ewar an sakanni, asa ta yi da kai kafin ta ce "Ban yi sallama da iyayena da an uwana ba, na san su na fushi da ni, ina bu atar na nemi yafiyarsu, kuma su ya kamata su rakani akina!!" ta arasa maganar gami da sauke wata zazzafar ajiyar Zuciya. a hankali ya bu e idanun nasa ya zuba mata sannan ya ce "Yanzu ni kike bu ata ba su." sharr!! hawaye su ka ci gaba da zubowa kamar dama jira suke ya yi magana, ta bu e baki za ta yi magana ya dakatar da ita ta hanyar yi mata alama da idanunsa wanda zuwa yanzu ta fara karantar Yarensu. Janyeta ya yi gefe sannan ya bu e Motar, cikin sassanyar muryarsa ya ce "Look! she's my small Mommy." Sai da ta goge walla sannan ta iya zazzaro ido ta na kallon cikin Motar, wata ha iyar Mata ce Babbar Mace wadda hutu da jin da i suka zauna, sanye take cikin dakakken Leshi Ba i wulik an yi masa adon Orange me duhu, ya sha Beads work ta ko'ina, Mayafinta ma Orange ne an yi masa adon Beads work ba i, komai ya ji banda tsiya in ji maro Sassanyan murmushi ta sakar musu kafin ta ce "Come hare my daughter!" a tsorace Husnee ta yi baya ta na kallon Akhiee gami da cewa "Wacece??" "Mamata ce, kema Mamarki ce kuma ita za ta yi miki duk abinda Uwa take yiwa arta, a tare da ita kuma akwai an Uwana, tare za ku tafi, ni zan tawo daga baya." Rushewa ta yi da kuka kamar an ce gobe za ta mutu, cikin shashsheka ta ce "Ni dai tsoro nake ji ka shiga mu tafi tare." girgiza kai ya yi kafin ya ce "Ni wanene to Amsa'u?, ki na tare da kariyar Allah ba kya bu atar kariyata, nima shi ne yake kareni." Matar cikin Motar ce ta ce "Mutane dai su na kallonku ata, ki bari idan kun ha u a akinku sai ku tattauna." Sai a lokacin ta tuna fa ashe da dubban idanu a kansu, shiga Motar ta yi ta zauna sannan ta ce "Akhiee don Alla....." zuba nata idananun da ya yi ne ya sa ta fasa maganar, bai ce komai ba ya rufe Motar gami da juyawa. Ya na jin Mutane su na bidiyo su na bada labarin wannan shine an Daba mafi ha ari a asar Nigeria kuma yau ne Kotu ta mallaka masa Matar da ya aura ba bisa a'ida ba, bai bi takan kowa ba ya arasa inda su Salansa ke tsaye tare da Prince, su ma bai ce musu komai ba ya ya ci gaba da tafiya. Motoci uku ne su ka yi Parking a ofar gidan su Akhiee. Jin an dena tafiya ya sa Husnee ta ara sakin wani sabon kuka don yanzu ta tabbatar an zo inda za a watsar da ita. Inna ce ta kalleta cikin nutsuwa ta ce "Ki dena kuka ki yi ha uri, kowace iya mace ta gaji haka, dole ne wata rana sai ta rabu da iyayenta ta tafi gidan Miji; ki auka nan ma gidanku ne, kuma ina da ya ini akan an Manya zai ri e ki da daraja kuma zai kare ha inki, Allah ya sanya alkairi ya baku zaman lafiya." Ba ta iya cewa komai ba sai dai ta sassauta kukan. Mukhtar ya ce "Yanzu shiga ciki za ku yi ko sai kun jira an zo an shigar da ku?" kafin Inna ta yi magana Rahma ta bu e Murfin Motar ta na cewa "Mama ku fito mu shiga mana." Maman ta ce "Okay mu je in, kama hannunta." Rahma ta murmusa gami da cewa "Allah Sarki yarinya mu ma haka aka yi mana muna ta kuka aka kaimu aka baro." Husnee kuwa ta na jin haka ta are are baki, Inna ta ce "Ke Rahma kul! ki na tsorata yarinya a memakon ki rarrasheta?" Dariya kawai ta yi ba tare da ta ce ala ba. Sai da Inna ta yi rarrashi sosai sannan Husnee ta fito daga cikin Motar suka rankaya zuwa cikin gida tare da su Zabira da su Surayya. Sun yi sallama a tsakar gidan ta fi sau goma amma an yi musu banza, Su Innajo da su Umma Uwani su Inna Huwaila su na zaune a can gefe sai kallonsu suke yi sama da asa suna tsegumi. Zahra da ke kwance a akinsu ba lafiya ta lalla o ta fito ta na amsa sallamar. Umma Uwani ta ce "Ke ubanki! me za ki je ki yi musu?? kin san irinsu??" kamar za ta yi kuka ta ce "Amma ko ban san irinsu ba ai mu Musulmi ne ya kamata a amsa musu sallama, bare kuma na san ba wani mugun abun ne ya kawosu ba, Husnee ce dai ba kwa so kuma Allah ya yarda ta zama ar gida sai dai ayi ha uri." Inna Huwaila Matar Baba Sa'idu ta shiga tafa hannuwa ta na cewa ''La ilaha illallahu wa annan a ba kunya, ku ji itama ta kangare yarinyar nan??" ta fa a ta na kallon Innajo gami da ri e ha arta alamar mamaki, Innajo ta ta e baki kafin ta ce "Shegiya me kama da tsintacciyar Mage, ai mun yi mata komai dole ta yi mana rashin kunya akan wannan an Kukar." Ba ta sauraresu ba ta wuce inda su Inna suke ta na fara'a ta arfin hali, "Sannunku da zuwa, ku shigo in raka ku akin Akhiee inaga anan ne za ta sauka." Inna da Aunty Rahma suka amsa sannan sannan su ka rufa mata baya. Bayan sun huta a akin ne Laita ta ja dogon tsaki ta ce "Wallahi Allah na kusa hudawa Mace tumbi a gidan nan, in banda rainin hankali suna kallonmu amma sai kace mun zo musu da ajalinsu?" Zara ta ce "Allah ya baku ha uri, halin gidan yawa ne sai Addu'a" Inna ta ce "Haka ne ar nan, kar ki damu mu ba mu yi
Chapter 40 · 0% Book details