← Book details Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 47

Sashe 10

Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ayeesha Abdulkareem INDO *M.W.A "Asma'u!!!!!!" kira ya walla mata da arfi cikin tsananin ka uwa da tashin hankali, cikin zafin nama ya finciko hannunta da mugun arfi hakan ya sa ta dawo kansa, garin daidaita tsayuwarsa ya taka awon ayabar da ta jefo masa santsi ya ja shi, gabaki aya su ka yi wata muguwar sufa su ka rikito daga saman benen su ka nufi asa, rimmm!!!!! sai gasu a tsakiyar harabar makaranta. Ihu an matan da ke kaikawo a wurin su ka sanya gami da tarwatsewa kowacce ta na neman wurin uya. Hankali tashe Akhiee ya ture Husnee da ke kwance akan irjinsa ya mi e ya na zuba mata idanu don sanin halin da take ciki, hankalinsa ne ya ara dungunzuma ganinta a sume ta wani irin ashe ta ara haske kamar ba jini a jikinta, da sauri ya sanya hannunsa cikin tafin hannunta ya dam e jikinsa na wata irin tsuma sabida tsananin acin rai. "Me ka yi mata??" muryar Yasayyadi Jameel ce ta dawo da shi cikin makarantar sa anin da da duk hankalinsa ya yi nisa, sai a lokacin ya lura da mutane sun yi da'ira akansu kowa ya zubawa sarautar Allah ido. a fusace Yasayyadi Usman ya araso wajen ya ri ayan hannun Akhiee ya finciko shi, ba tare da nazari ba ya afka masa wani lafiyayyen mari, "Uban me ka yi mata?? ba tambayarka ake yi ba?? me yasa ba ka jin magana kai?" ago hannu ya yi zai ara tsinka masa wani marin Akhiee ya fizge hannunsa ya doki irjin Yasayyadi Usman da arfi sai da ya yi taga-taga zai fa i su Yasayyadi Jameel su ka daddafe shi. Idanunsa da suka canja kamanni ya zubawa sauran alibai an kallo kafin ya ce "Kowa ya ace daga nan ko na illata masa rayuwa wallahi; kai kuma kar ka ara gigin marina in ba haka ba zan tarwatsa maka farin cikinka, idan ta tashi sai ku tambayeta idan akwai tsiyar da na yi mata." Ya na gama fa en haka ya koma inda Husnee ke kwance ba alamun numfashi a tare da ita. an makaranta kuwa tuni sun fice da gudun ceton rai, sai ai da ba su arasa fita ba. rungumarta ya yi a irjinsa ya nufi cikin ajinsu ba tare da ya bi takan kowa ba, ajiyeta kawai ya yi ya fito ya sa kai ko kallon su Sheikh Auwal bai yi ba ya fice daga makarantar, tafiyar kawai yake yi amma bai san inda ma zai dosa ba don kuwa ransa ya gama kaiwa ololuwar aci, bai san inda zai nufa ya ji da i ba. Su dai sun tsaya curko-curko kamar dangin Kaji an rasa me yin ko warar magana. "Za ka ci Ayaba?" ta fa a gami da mi a masa ragowar wadda take ci. girgiza kai ya yi alamar a'a, ta ci gaba da cin kayarta hankali kwance, jin bai ce ala ba ya sa ta cewa "Akhiee! yau ba za ka yi mini magana ba ne? ni fa so nake in ga dariyarka, kullum sai dai ka dinga ha e rai kamar hadarin gabas" Kyawawan idanunsa ya zuba mata cikin lallami ya ce "Ni fa ki yale a yadda nake don ni ba na dariya." da sauri ta ce "To sabida me?" shiru ya yi kamar ba zai bata amsa ba sai kuma ya ce "Ta na karya min tambaya ne" "Iyye?!!" ta fa a gami da sakin baki, "Ni fa ba na gane wannan yaren naka, ka fa a min da hausa" ''Ai ba za ki gane ba sai dai ki wahalar da ni." turo baki ta yi cike da shagwa a ta ce "Don Allah ka yi dariya ko da sau aya ne na san za ka yi kyau" banza ya yi mata kamar ba da shi take ba, jifansa ta yi da awon ayabar da ta cinye gami da cewa "Sai ka ri e abarka ba a so ma, kuma na yi fushi ba zan ara kula ka ba" daga haka ta juya fayau-fayau da nufin barin gurin cak!!!!!! ta tsaya sabida muryarsa da ta kara e kunnuwanta. sun da e a tsaitsaye jiki duk a sanyaye kafin Yasayyadi Jameel ya ce "Mu dai mu na ganin takanmu a rayuwa, wannan yaro ko annoba?" a sirrince Sheikh Auwal ya goge zazzafar wallar da ta fara gangarowa daga cikin idanunsa, cikin dakiya da mazantaka ya ce "Kar ku damu in Allah ya yarda ba abinda zai faru, ku ci gaba da Addu'a watarana sai labari." Yasayyadi Usman dafe da irjinsa da yake jin kamar ma aukansa ( ashushuwan ha arinsa) sun kakkarye cike da tsanar Akhiee ya ce "A tunaninku wannan shai anin zai shiryu ne?? ai kuma ya yi nisa ba zai ta a jin kira ba, Wai har Abhi ya ce wani kar a ara zuwa ana zancensa, ai abin fa en yake yi ba dole a fa a ba?" Malam Zayd ma ya taya Yasayyadi Usman su ka ci gaba da yi, takaici da tashin hankali sun hana Sheikh Auwal yin magana, gashi ya na son shiga ya ga halin da Husnee ta ke ciki sai dai ya na tsoron abinda zai tarar. Amadu direban gidan su Husnee ya shigo ya na walla sallama, Sheikh Auwal ne ya amsa ya na arin daidaita nutsuwarsa ya nufi hanyar ofa don ganawa da Amadu. Musabaha su ka yi kana Amadu ya ce "Malam na ga kowane alibi ya fita ne to banga Husnee ba shine na araso in tambaya ko ta yi laifi ne an tsareta?" jim!! Sheikh Auwal ya yi kafin ya ce "Ba laifi ta yi ba kasan yau da gobe sai Allah, larura ce ta sameta." Hankali tashe Amadu ya ce "To fa ikon me sama, me ke faruwa Malam?" "Ai ba wani abin tayar da hankali bane da sau i in sha Allah. Amadu ya ce "To to to, ai ba komai Allah i bata lafiya, za ta iya fitowa mu koma gida ko?" a hankali ta bu e idanunta da su ka yi wani nauyi jingim kamar an ora musu dala da gwauron dutse, tunanin abinda ya faru ne ya fara dawowa mata, ba za ta iya cewa ga abinda aka yi ba don kuwa tin wannan kira da Akhiee ya walla mata ba ta ara sanin abinda ke faruwa ba. urawa ta yi ta tashi da yar jikinta duk ya hau ciwo kamar wadda aka yiwa duka da sanda. Cikin rashin warin jiki take takawa har ta fito harabar makaranta inda malamai suke tsaye duk sun rasa abin yi, ganin ta fito ya sa duk suka tsaya kallonta, Yasayyadi Usman sam bai so farkawarta ba,, ya so rigimar ta ara girma ta yadda zai huce takaicin ciwon irjin da Akhiee ya sa shi. Farin ciki ne ya lullu e Sheikh Auwal a ransa ya godewa Allah a zahiri kuwa ya cewa Amadu "To ga ta nan ma" Amadu ya washe baki gami da cewa "Ma sha Allahu ai da sau i sosai." Husnee dai da ta duba gabas da yamma ta ga saura ita ka ai a cikin alibai sai ta fashe da kuka, hakan ya ara sanya zargi a zukatan su Yasayyadi Usman. Malam Zaidu ya ce "Ke Husna me Akhiee ya yi miki?" girgiza kai ta yi alamar ba komai don kuwa ba za ta iya magana ba, Amadu ne ya araso wajen ya na cewa "Sannu Husna! Sannu Innata! Allah i sauwa e, mu tafi gida sai a je asibiti ko?" ba ta kula shi ba ta fice shima ya bi bayanta da sauri, gidan baya ya bu e mata ta na shiga ta kwanta ta ci gaba da rera kuka. Cikin sanyin jiki Amadu ya ce "Ki yi ha uri Innata, kanki ke ciwo ne? kar dai wannan an daban ne fa ya yi miki wani abun don na lura kamar malaman nan ba wata gaskiya garesu ba." Jin surutun da yake ya sa ta danne kukan nata cikin muryarta da ta yi sanyi kamar yadda jikinta ya yi ta ce "Ba na so ka fa a a gida cewar wani abu ya sameni, nima kaina ban san abinda ya faru ba kawai dai na fahimci cewar na suma ne, kuma ila ma Aljanu ne, ni yanzu ba abinda yake damuna don Allah kar ka fa a za su hana ni zuwa makarantar ni kuma hankalina ba zai iya aukar hakan ba" cikin tausayawa ya ce "To shikenan ba zan fa a ba Allah i ara lafiya." Ba ta ce komai ba sai ma ara yin lamo da ta yi ta na tunane-tunane. baya........ Hajiya Laure har su ka isa gidan Aminiyarta Hajiya Saudah masifa take zazzagawa kamar zararriya. A falo ta samu Hajiya Laure ta hakimce ar aikinta na yi mata tausa, jin muryar awarta ya sa ta fara fara'a ta na cewa "Hajiya Laure manyan asa me ke faruwa ne na ji kina ta an surutai tin daga nesa?? wai ma ina takabar taki?" "Hmm!! abinda ya fi haka ma ai zan yi, bar ni da batun takabar nan a cikinta nake, amma hankalina ba zai ta a kwanciya ba indai wanda ya kashe Alhahi Salisu ya na yawo a gari, abinda ya sa ki ka ganni anan neman shawararki na zo yi don ke ce ka ai za ki share min hawayena." Hajiya Saudah ta ce "A'ahh ban gane ba ina kamashi da an sanda su ka yi?" "Yo an sanda ko an iska? bayan kawai ku ina Inspector innan ya ci arshe ma ashe sun sake shi? ai cewa na yi na gaji da shigo-shigo ba zurfi gwara na zuba ku i a harra a min shi lokaci aya." shu'umin murmushi Hajiya Saudah ta saki kafin ta ce "Ke Baraka bamu wuri." ewa ar aikin ta yi ta basu wuri, Hajiya Saudah ta numfasa kana ta ce "To yanzu ta wace hanya ki ke ganin za mu bi?" "Ni fa wallahi ta kowace hanya ma zan iya bi, ni fa shawara na zo nema kawai ni ki bani shawara. "To ai in hagu ta i sai a koma dama, in da dama sai a dama, gobe in Allah ya kaimu ki shirya mu je an tsibirin boka Barore, in
Chapter 10 · 0% Book details