← Book details Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 47

Sashe 44

Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sanyin murya, "Me yasa an gidanku ba sa sona???" Hannunsa na dama ya sanya ya tallafo ha arta hakan ya bashi damar kallon fuskarta, cike da tausayinta ya ce "Ba ke ce ba sa so ba ni ne, ba ki da wani aibu wanda zai sa a i sonki Asma'u, ba sa so na yi farin ciki ne shi yasa suke son rabuwata da ke, Babana ya na gidan nan Da shi da Zara su ka ai ne danginki; ko da Zara ba ta nan ki dinga zuwa wajensa ki na zama kin ji ko?" "Amm...." saurin katse mata hanzari ya yi ta hanyar girgiza mata kai don haka ta yi shiru gami da yin asa da kanta. Sun auki an lokaci a haka ba tare da kowa ya yi magana ba, Rislan ne ya katse shirun da cewa "Ki duba a cikin kayana akwai Jallabiya na san akwai wadda za ta yi miki sai ki sakata, zan je wurin Abee na dawo sai mu je ki gaisar da shi." Yanzu ma kai ta gya a masa ba tare da ta ce komai ba, cikin nutsuwa ya zameta daga jikinsa ba don ta so ba, bai ara kallon inda take ba ya fice ya nufi sashin Abee. Sai da ta da e a zaune a wurin sannan ta iya tashi ta nufi wajen sif ta bu e, kaya ne a ciki masu tarin yawa kuma duk insu sabbi ne ba wanda yake nuna alamar an saka shi, bayan ta gama are musu kallo ta ri e ha a ta na cewa "Oo!! ikon Allah a ce cikin kayan mutum kwata-kwata ba tsoho? ko dai ya kai wanki ne??" Kasancewar ita ka ai ce a akin babu me bata amsa ya sa ta rufe bakinta ta ci gaba da burkita kayan don ganin wadda ta yi mata, sai da ta gama ruwan ido sannan ta auko wata doguwar Jallabiya Maroon ita in ma ta yi mata yawa daga fa in har tsayin, amma da yake abin aro ne haka nan ta sanya sannan ta auki lafkeken hijab inta ta saka ta koma ta zauna jiran shigowarsa. "Abee ka san dai ina da hankali kuma na san ciwon kaina, to don me zan yi abinda ba shi ne daidai ba?, kawai don ba sa son farin cikina ne shi yasa suke cewa haka, ni da Asma'u duk mu na son mu rayu tare, na san kai ma ba za ka so a rabamu ba." Abee ya jinjina kai kafin ya ce "Wannan Gaskiya ne, shi yasa dama sam ban goyi bayan kowa ba don na san mafi yawancin abinda za ka yi me kyau ne." numfasawa ya yi kafin ya ci gaba da cewa ''Yarda da kai da na yi shi yasa nake maka wannan shaidar kuma na Amince da abinda ka yi, ba na so ka ban kunya ka ji Dattijo?" ya arasa maganar cikin Sigar lallami, gya a kai ya yi sannan ya ce "In sha Allah Daddy." "Ita Matar Aure ba wai abar muzgunawa ba ce ta na da daraja da kima, sannan a ri e amana kar wani abu ya sa a ci amanarta da iyayenta, sannan a mayar da kai wajen sauke ha inta da kuma kare shi, Allah ya yi muku Albarka." nannauyar ajiyar Zuciya ya sauke tare da amsawa da ''Amin, bari ta zo ta gaisheka Abee" ya fa a tare da mi ewa tsaye. Zara ta ce "In zo in raka ka??" juyowa ya yi ya maka mata wani banzan kallo, ta yi saurin sunkuyar da kai gami da ha e bakinta, ya yi wafa bai ce komai ba ya fice. Shiru ne ya ratsa na wani lokaci kafin Abee ya katse shirun ya na murmushi ya ce "Allah Sarki Dattijona; Zahra'u labarin me muke yi ma kafin ya shigo??" ta ce "Labarin rashin lafiyata, Wallahi Abee idan mutum ba shi da lafiya sai ya ji unci ka ga ko fita ba na iya yi sai dai in ga kowa ya na ta yawonsa ba me kulawa da ni, don ma yanzu ka dawo." "To ai jikin naki ya yi sau i sosai ko?, to ai Zahra'u ciwo ba shi da da i ko ka an, kin ga ni shekaruna goma sha ina zaune ba na iya tafiya ba na iya tashi komai sai an yi min, don ma Allah ya azurta ni da zuri'a, kuma hakan ya na daga cikin baiwarsa, babu wanda rayuwarsa ba ta tafiya tare da jarrabawa kuma kowa da irin ta shi, sannan a rayuwa abubuwa da yawa suna da silar faruwarsu." gyara zama Zara ta yi cike da al'ajabi ta ce "Wai da gaske Abee da ka na tafiya?" tambayar tata sai da ta sa shi dariya, ba tare da ya dena dariyar ba ya ce "Da garau nake tamkar ke, kamar yadda na gaya miki komai ya na da sila to nima hakan ce ta faru da ni." "To Abee meye silar?" kafin ya yi magana Akhiee ya yi sallama hannunsa auke da Husnee wadda ya rungumeta a irjinsa tamkar ar jaririya sai da ya zo gabansu sannan ya direta ya na cewa "Abee gata nan." Abee dai lamarin na Akhiee ya sa shi kasa cewa komai, Zara ce ta yi arin cewa "Ciwo ta ji a afarta ne Akhiee?" idanunsa a asa ya ce "Wai tsoron duhu take ji, kuma ba ta san kan gidan ba shi ne kawai na akkota." Abee ya murmusa ba tare da ya ce uffan ba, zuwa yanzu ya gama gazgatawa kansa ba aramin so Akhiee yake yiwa yarinyar nan ba, indai kuwa haka ne ta cancanci shi ma ya so ta domin alamu sun nuna itace silar farin ciki da kuma sauyawar rayuwar an nasa." (Ma su karatu ba ku ce min ina Husnee ba?" Ai ya na direta ta zagaya bayansa ta uya sabida wata muguwar kunya da ta lullu eta, ji take tamkar asa ta bu e ta shige ciki, da ta rasa abin yi kawai sai ta fashe da wani an marayan kuka. Zahra dai dariya take yi musu, Akhiee kuwa ba tare da damuwa ba ya zame ya koma kusa da Akhiee ya yi zamansa, cusa fuskarta ta yi a cikin hijab inta ta na ara sakin wani sabon kukan. Zahra ta na dariya ta ce "Kai Anti Husnee sai ka ce aramar yarinya?, Abee ne fa" Akhiee ya ce " yaleta in ta gaji da tsayuwa sai ta zauna ko?" Abee ya ce "A'a ba za a yi haka ba, zo nan ata, ki rabu da wa annan zolayarki suke yi." Kasa motsawa ta yi don har ga Allah ji take tamkar za ta nutse, Abee ya ara da cewa "Zo ki zauna kusa da ni; ke ma yanzu ata ce ai, tamkar Muhammad haka kike a wajena, kin ga shi tamkar aboki haka ya aukeni." Har yanzu ba ta da niyar gusawa daga ina take tsaye, a ufule Akhiee ya ce "Wai ba kya ji Abee na magana ne? ko so kike sai na araso da ke da kaina??" ta san zai aikata fin haka ya ara mata wani abin kunyar don haka ta salalla a can bayan Zara ta lafe, shiru ne ya ratsa wajen na an lokaci kafin Abee da yake ta murmushin farin ciki ya katse shirun da cewa "To Barka da da Dare ata tinda kin kasa magana." Sai a lokacin ta tuna abinda ya kamata ta yi wato gaisuwa kuma ta kasa, murya can asa ta ce "Ina wuni" cikin jin kunya. Ya na fara'a ya amsa da ''Lafiya Lau, ya rayuwa?" ba ta ce komai ba hakan ya bawa Zara damar cewa "Ki fito sarari mana ya kamata Abee ya ga fuskarki kar ya kasa ganeki gobe, kin san idon manya ka an-ka an suke gani." ta arasa maganar cikin sigar zolaya, Abee ya yi dariya gami da cewa "Na fi ki lafiyar ido Zahra'u." "To ai Abee naka idanun sun manyanta sosai, dole nawa za su fi kyau. "Na tsofi kuma ai ya fi arko" Abee ya bata amsa. kafin ta ce wani abu Akhiee ya shiga zancen da cewa "Wai ke kin auka Abee Kakanki ne da kike zolayarsa?, Abee ka dena biye mata don Allah." Abee ya rausayar da kai gami da cewa "To!! Dattijo su waye Abokan nawa in ba ku ba?, to a bar zancen dai, Yanzu na dawo kan ata." an tsahirtawa ya yi sannan ya ci gaba da cewa "Asma'ul- Husna! ga amana nan ta ana Muhammad Rislan, shi maraya ne ya rasa Mahaifiyarsa tin bai wuci shekaru goma sha aya ko shabiyu a Duniya ba, tin daga lokacin kuma rayuwarsa ta sauya, farin ciki ya aurace masa, ni kuma ina matu ar sonsa ina son ganin farin cikinsa; za ki same shi a wani irin bau en Mutum, hakan ya na da nasaba da irin tashin hankalin da ya tsinkaya a rayuwarsa a daidai lokacin da shekarunsa ba su kai ya ga wannan tashin hankali ba, hakan ya bada gudun mawa wajen canjawarsa sosai, ni kaina na sani rayuwa da shi sai da ha uri sai an jure, a dinga ha uri da juna a dinga kawaici da juriya, a dinga tausasa zuciya sannan a kyautatawa juna." an jim!! ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Jikina ya bani cewar ke ce silar canjawar rayuwarsa, ya na bu atar temakonki sosai domin tin da ya rasa mahaifiyarsa bai ara samun wata uwa mafi kusanci da shi ba sai ke. Mayar da kallonsa ya yi kan Rislan gami da cewa "Dattijo! ba na son na ji sa ani a tsakaninku, kuma ka sa a ranka indai na samu haka kai ne me laifi." ya gya a kai alamar ya gamsu. Husnee kuwa ta yi tsit!!!! kamar ruwa ya cinyeta , kalaman Abee sun yi bala'in ratsa Zuciyarta kuma sun jefata cikin tunani iri daban-daban, ga tarin tambayoyi da ta rasa wa za ta yiwa su Akiee in ko Abee in?. Nasihu Abee ya yi musu sosai wanda suka ratsa Zuciyar Husnee jikinta ya yi sanyi salam! Zuciyarta ta tsumu kuma ta samu nutsuwa, bayan ya kammala ya rufe da Addu'a sannan suka bar sashin nasa tare da Zara ita ma
Chapter 44 · 0% Book details