← Book details Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 47

Sashe 42

Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bu e yake, sai aramin wandonta iya guiwa. A gefen gado ya ajiyeta sannan ya shiga toilet, bayan ya fito ya zura rigar sannan ya nufi kan Gado. A gefenta ya zauna ya zubawa fuskarta da take a cukurku e idanu tamkar don ita ka ai aka halitta masa idanun ko son iftawa ba ya yi, daga yanayinta ya fuskanci a cikin damuwa da takura take yin baccin da alamu ma ba jin da insa take yi ba, gashi ta du une cikin lafkeken Hijab wanda ko likafani za a yi mata da shi zai isa. Cikin nutsuwa ya ora tattausan hannun akan fuskarta ya na shafata a hankali a hankali, "Asma'u!! ji nake tamkar tamkar garkuwa ce ke gareni, zan so na kasance me sanya ki farin ciki a koda yaushe, sai dai ba zan iya ba rayuwata cike taf da abubuwa iri-iri, a memakon ki yi farin ciki sai dai ki kasance cikin zubda Hawaye Asma'u" a zahiri yake maganar ya na yi ya na kewaye hancinta da kan idanunta da babban yatsansa, har zuwa lokacin kallonta yake yi tamkar wata sabuwar halitta ba mutum ba. ebi an lokaci cikin wannan yanayin kafin ya janyota jikinsa ya rungumeta a cikin rijinsa ya fara arin cire mata hijabin a hankali ta yadda ba za ta farka ba, har ya cire ya ajiye shi can gefe ba ta farka ba sai ma numfashi dogaye da take ja ta na ara lin aya a cikin baccin, ga dukkan alamu ta samu sauyin yanayi wanda ya sa Zuciyarta ta samu sakewa, har ila i yau bai dena kallon fuskarta ba kai ka ce ha iyeta yake shirin yi, idanunsa sai wani irin she i da yalli suke yi su na ara canja kala. Hannunta ya ri o ya zuba masa ido, ganin zobensa ya na nan a jikinta ya sa shi sauke wata sirrintacciyar ajiyar Zuciya, "Asma'u ina bu atarki a rayuwata, ki kasance tare da ni ." Ya fa a cikin wani irin yanayi wanda ya na da nasaba da shaukin sonta, wanda shi kansa bai san da hakan ba. Har 04:00am daidai ya na rungume da ita sannan ya zameta daga jikinsa ya kwantar da ita, sai da ya ara ibar lokaci me tsayi ya na kallonta sannan ya sauka daga kan gadon, Alwala ya auro sannan ya canja rigar jikinsa ya zura wata sabuwar jallabiya Brown ya sanya hula arama ta ani ka ji hadisi sannan ya fara Sallar nafila. Sai lokacin da aka kira Sallar farko sannan ya tashi daga kan dardumar ya fice daga gidan baki aya. Sai bayan an idar da sallah a masallatai Allah ya bata ikon farkawa firgigit kamar wadda aradu ke shirin fa owa a ka. Zazzare ido ta shiga yi ta na duba ko'ina ko za ta ga Akhiee amma fayau ko yallin rigarsa ba ta gani ba, wayarta ta jawo ta duba agogo ganin lokacin salla na neman ure mata ya sa ta yi saurin direwa ta fito daga aki ta na dube-dube ko za ta ga ban aki, aki biyu ne a wajen daga wanda ta fito daga ciki sai wani da alamu dai ba ban aki, gashi ko ina a bushe yake ba alamun akwai ruwa. Komawa ta yi aki da zummar aukar waya ta kira Rislan don jin inda za ta samu ruwan ta na komawa idonta ya sauka akan ofar toilet na cikin akin, duk da ba ta da tabbas amma ta na kyautata zaton shi ne don haka ta nufi wajen domin ganewa idanunta. Sai da ta sauke ar ajiyar Zuciya ta jin da i sannan ta auro Alwala ta fito, ta na idar da sallar ta yi addu'a ta zame ta kwanta akan dardumar daga haka bacci ya sake surarta. Yazeed kwana biyun nan sam ba ya iya baccin kirki sabida tunanin Ma'u, har agara yake a kira Asbah da ya fita masallaci ya dawo ko akinsa ya ba ya komawa sai dai ya zauna a harabar gidan don kuwa in ya koma ma ba shi da abin yi sai damuwa anan kuwa ko shuke-shuke ya kalla zai rage zafi. Yau ma kamar kullum ya na zaune ya buga tagumi kamar a mafarki ya ga gilmin Ma'u da ullin kayanta a hannu ta nufi wajen get. Zundum!!! Zuciyarsa ta yi wata mummunar bugawa wadda ta yi daidai da tashinsa tsaye, razanar da ya yi gami da bugun Zuciyarsa suka bada gudun mawa wajen juyawar kansa hakan ya haifar masa da jiri idanunsa su ka fara ganin duhu kansa na wata irin majaujawa tamkar ana girgizar asa a cikinsa. Cikin wata wahaltacciyar murya ya shiga kiran sunanta duk da ba shi da tabbacin za ta ji shi kuma ta saurare shi, da yake suna linzami ne kamar gizo haka ta ji an kira sunanta, gabanta ya yanke ya fa i har asa, kasa juyowa ta yi don kuwa ba ta san me kiran nata ba, a wannan lokacin kuwa ba ta son kowa ya ganta don so take ta gudu, in ma ba inda za ta je gwara ta dinga tafiya ko ba ta da wurin zuwa, a tunaninta Allah zai ha ata da wa anda za su temaketa, Ta auki an sakanni a tsaye ba ta ara jin an kirata ba don haka ta ci gaba da tafiya cikin san a har ta isa bakin get, sai dai abinda ba ta sani ba ko kuma ta manta da shi, me gadi ya na sa mukullai a ofar kuma ba wanda zai bata su sai shi ko Haj Laure, turus ta tsaya Zuciyarta ta karaya tamkar za ta fashe da kuka. Juyawa ta yi ta na kallon akin me gadi tare da tunanin ko zuwa za ta yi ta ro i alfarmarsa? Kamar saukar aradu haka ta ji lokacin da muryar Yazeed ta kara e Fadar cikin Masarautar Kunnuwanta, sabida firgici sai da Zuciyarta ta an tsaya na wucin gadi yayin da numfashinta ya sar e kamar me shirin sumewa. Da rarrafe ya araso inda take don kuwa ya na mi ewa zai iya fa uwa, sai da ya dangana da inda take sannan ya tsaya dur eshi akan gwiwoyinsa, idanunsa da ke gani dishi-dishi ya ago ya na kallonta kafin ya fara magana cikin sar iyar murya tamkar an sha are shi, "Ma'u kar ki gudu ki barni, don Allah ki tafi da ni duk inda za ki je zan biki, kuma akanki zan iya jurewa kowace irin rayuwa wallahi!!" Yadda yake maganar tamkar zautacce ya sa Ma'u ta ara tsorata da shi, salon bugun zuciyarta ya ara canjawa daga sauri zuwa gudu, kai kawai take girgizawa don kuwa yadda numfashinta da Zuciyarta suka burkice ba za ta iya furta ko uffan ba. "Ma'u zan mutu idan ki ka gujewa rayuwata, wallahi zan iya makancewa idan idanuna suka dena ganinki, iya tashin hankalin nan da suka gani har sun fara dena nuna mini daidai, duhu nake gani, walwata ta na juyawa alamar hauka ta fara tabbata a gareni, wallahi Ma'u ina sonki so me tsanani, irin azababben son nan da yake tarwatsa rayuwar an adam, ki ji aina ki tafi da ni ko zan samu sassauci. Abin nasa haushi yake bawa Ma'u a gefe guda mummunar tsanar da ta yi masa na ara zigata akan ta ci mutuncinsa ko zai gane da gaske ba za ta ta aunarsa ba, cikin sassar ewar murya gami da arfin hali ta ce "Ni ba zan ta a son watsatstse irinka ba, mazinaci azami mashayin giya wanda bai san daraja da kimar kansa ba bare ta wani, ka fita daga rayuwata in ba haka ba kashe kaina zan yi wallahi, ni na tsaneku baki ayanku kuma Allah sai ya saka min." Wasu zafafan hawaye ne suka yiwa fuskarsa mugun wanka, ya girgiza kai gami da dafe irjinsa daidai saitin Zuciyarsa, "Ma'u Zuciyata shirim fashewa take yi, don Allah kar ki hukuntani akan laifin da ba ni na aikata ba, idan wani ne ya yi miki laifi don Allah ki antani daga angarensa, ni ban kasance irinsu ba, kuma wallahi tallahi ba na iya zama na sha giya tin daga ranar da na furta miki kalmar so kika jefani cikin tashin hankali, a da na auka abinda nake yi shi ke kawo nisha i na auka tarayya da matan banza shine more rayuwa, amma tinda na kamu da sonki na gane martabar mace, na gane duk abinda nake yi ba shine ke sanya farin ciki ba, na dena ba zan ara ba na tuba ki yafe min; yanzu rayuwata da mutuwata sun rataya a wuyanki Ma'u!! ina fatan ki yi mini kyakkyawan za arasa maganar gami da rushewa da wani susutaccen kuka tamkar aramin yaron da ke neman Mahaifiyarsa. Dogon tsaki Ma'u tafka me cike fa acin rai da tsantsar iyayya, ba tare da ta sake kallon inda yake ba ta ja ullin kayanta ta koma cikin gida cike da ba in ciki da takaicin yi mata silar rashin guduwar da ta yi niyya. A take a wajen wani mugun azababben tari ya sar e shi wanda ya haifar masa da shi ewa daga haka bai ara sanin inda kansa yake ba. Tin da safe da Baba Sa'idu ya je gaisawa da Abee ya gyara zama ya tankwashe afa kamar me shirin kwasar taushe, ya karya harshe ya rattabawa Abee maganganun son rai akan Auren Rislan da Husnee, Abee ya gama saurara sannan ya jinjina kai ya ce "Duk ina an uwan nasa?, a zo min da su don in ji menene aibun da suke gani a cikin hakan?" Baba Sa'idu ya ce "To Yaya" tashi ya yi ya fita don nemosu, da Adamu ya fara karo don haka ya ce masa ya je ya tarkato sauran. Da yake duk jiran ka an suke yi da wane gayawa wane dandanan suka cika tafkeken akin Abee in, ciki kuwa harda Umma, Innajo, Umma Azima, Umma Uwani, matan Abee, sai Matan Baba Sa'idu su biyu, Inna Huwaila da Inna Kulu, sai iyalinsu cunkus amma banda Sheikh Auwal da Zara da Sauran wa anda ba sa kusa. Duk yawansu sai da Abee ya saurari ta bakin kowa wanda yawancinsu bayan nuna rashin goyon baya akan Auren sai sun ara da sharri da arya,
Chapter 42 · 0% Book details