← Book details Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 47

Sashe 25

Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

amma ina so ka sani da ni da su duk da kai mu ka dogara, sai anjima" daga haka ta katse wayar. Bin wayar hannunsa ya yi da kallo cikin tashin hankali da mamaki sai dai a kan fuskarsa sam babu wata damuwa. A gefe guda kuwa tunanin wanda ya yi masa wannan anyen aikin yake yi. Tsugunne ba ta are ba, an sayar da Biri an sayi Mage, don haka bai ga ta zama a makaranta ba. CP ya turawa kira, har ta katse bai auka ba sai da ya ara kira sannan ya auka. "Yalla ai akwai damuwa fa!" Rass irjin CP ya buga da sauri ya ce "What Happen Risslan?" "An sace mini yara guda biyu, kuma Mata, hankalina ya tashi domin kuwa an samu wanda ya iya gane Lagona, za su yi mini illa ta angaren iyalina, amma ba komai ina so ka tayani binciken waye ya aukesu da kuma wanda ya sa a aikata, sannan ina bu atar in gansu." CP ya jinjina kai kafin ya ce "Gaskiya kuwa in haka ne an samu matsala, amma su da aka rasa in sa Allah za su dawo, ba za su iya yin galaba akanka ta kowace hanya ba, ya kuma zama dole ka ru anya tsaro ka sa taka-tsan-tsan akan duk wa anda su ka shafeka, domin da alama kowaye ya aikata hakan ba aramin shege bane don ba wanda ya san ka na da iyali bayan wanda ake ganinku tare, lallai ka kula nima zan yi iya arina daga nan." "Okay" kawai ya ce ba tare da ya ara magana ba ya katse wayar. Yasayyadi Usman Jaafar Adamu Hamza, su na zaune suna tattaunawa akan batun Abhi da Akhiee. Adamu ne ya ta ule baki kafin ya ce "Wallahi ina jin haushin wannan son kai na Abhi, ban san me yasa ba ya fi son lalataccen Yaron nan." "Aikin banza kai ma ba ka ji ance lalataccen a ya fi shiga rai ba?" Hamza ne ya yi maganar cike da tsanar Akhiee. Jaafar ya ce "Ni ba wannan ne tashin hankalina ba, wai Makkah na fa ya ke son zuwa amma Abhi duk yawan an gidan nan da yayyen Akhiee in wa anda da can su suke kai shi Makkahn amma wai yanzu Akhiee ya nema, shi kuma sabida munafurci har da wai shi zai yi komai." "Ai ba zai yuwu ba, ba za mu bari akai Mahaifinmu Makkah da ku in Haram ba ya zama dole mu nemi Yaya Sani da Yaya Bello mu sanar musu tsiyar da ake shirin tufkawa, ko Sheikh Auwal ma ba za mu bari ya sani ba in sun ji sai su sanar da shi." Adamu ya ce "To banda abinku ai Sheikh Auwal in ne ya ke aure masa, wallahi shi ya ke goyon bayansa shi yasa ma ba ya jin maganar mutane, munafukan banza." Yasayyadi Usman ya ce "Ina sane da su ai, kar ku damu mu ma lokacinmu zai yi ai." Jafaar ya tafka tsaki kafin ya ce "Ni fa da ni na ke so a je Makkan nan idan an tashi, ato! " Adamu ya ce "Yo dama kai Abhi in ya ce ai bayan Akhiee sai ku yi ta tafiya Allah i tsare." A gadarance Jaafar ya amsa da "Amin" surutu su ka ci gaba da yi akan Akhiee kowa na tofa tashi. angaren Akhiee komai ara cin tira yake yi, don kuwa gashi har wuni ya na neman arewa la'asar ta yi ba a ji ko da labarin su Zakiyya ba. acin rai da takaici sun yi masa caa! ya ma rasa me zai yi gabaki aya. Sai la'asar in ya shigo makaranta shima ba don ya so ba sai don ya rasa inda zai je ya ji da Bai bi takan kowa ba ya wuce inda ya saba tsayawa. Idanunsa a asa ya na tunanin ta inda zai ullowa lamarin wanda ya ke bibiyarsa kamar daga sama ya ji Muryar Husnee a kusa da shi...... "Ai na zata ba za ka zo ba" kallonta ya yi kafin ya doka tsaki cikin acin rai ya ce "Wai ke kunnen ashi gareki ne??" Jingina ta yi a jikin makari ta na murmushi, cikin sanyin jiki ta ce "Kunnena irin na kowa ne, ka yi ha uri Akhiee na ma yi ari da na jure rashinka na an lokutan da su ka wuce a baya, ni fa da gaske da kai nake so na yi rayuwata, kuma idan ka shiga tsakanina da kai to tabbas abinda ba ka so na zama zan zama, ba za a kuma ganina a makarantar nan ba, kwanan gidan iyayena ma zai gagareni, nima zan lalace na dawo irinka, bai zama lallai ka yarda ba amma za ka gani a aikace." "To wai ke me kike so na yi miki? na gaya miki shiga rayuwata ba burgewa ba ce, ban yi miki wani abu na untatawa ba duk da irinn takurawar fa kike yi mini, na kasa aukar mataki akanki, har yau kuma ki na samun damata, to me ya rage miki? ni na ce miki ban san menene so ba. "To Akhiee tinda ni na so hakan ai ban damu da sai na burge wasu ba indai na burge kaina, dan dai ka na ganin kamar da wasa na ke yi maka ne, amma har cikin raina ni ina aunarka, ban damu da halinka ko wani abu ba iya abinda na sani shi ne ina sonka!" Shiru ne ya ratsa tsakani na an lokaci sanna Akhiew ya katse shirun da cewa "Kin shirya Rayuwa da ni?" Lumshe ido ta yi ta na murmushi cikin warin guiwa ta ce "I'm ready" "Okay good, i want you to vote for me" Idanu ta zuba masa cikin sauri ta ce "Ban fahimci inda maganarka ta dosa ba." gyara tsayuwarsa ya yi sannan ya ce "Ina nufin ki za eni ki bar kowa, in kin yi hakan shine zan san ki na tare da ni duk rintsi duk wuya, nima zan fi jin da in kasancewa a tsaginki" ya yi maganar ya na zuba mata kaifafan idanunsa, sai da ta sunkuyar kai sabi da kallon da yake binta da shi, ta an numfasa sannan ta ce "I already voted for you, tin tuni kai na za a shi yasa ma na gaya maka iya gaskiyata" Cikin sassanyar murya me sanya nutsuwa ya ce "Kin tabbata?" kai ta gya a gami da cewa "Eh" Bai ce uffan ba ya kama tsintsiyar hannunta ya shiga janta, da kallo ta bishi a ranta ta na tambayar kanta ina zai kaita? kuma gashi ta kasa cijewa ta dena binsa. Haka ya ratsa jama'a da ita ba tare da damuwa da kallon da ake yi musu ba, sai da su ka dangana da wajen da Amadu ya ajiye mota sannan ya tsaya, daidai lokacin Zara ta araso da gudu-gudu hankali tashe ta ce "Ina za ki je Husnee??" "Nima ban sani ba tambayi Akhiee" ta fa a ta na kallonsa. "Ki koma makaranta kar ranki ya aci" ya fa a ya na zuba mata wani shegen kallo wanda ya sa ta yi saurin juyawa. Amadu tuni ya fito daga cikin Motar cike da mamaki ya ce "Lafiya dai?" Akhiee ya ce "Ki shiga mota Ni zan tafi akan Dokina, amma kar ku bari na ace muku duk inda na yi nan za ku yi." Amadu ya an yi gyaran murys cike da tsoro ya ce "To Malam ina za mu je haka?" Rikitattun idanunsa ya watsawa Amadu gami da cewa ''Kar ka bari ka yi mini ba daidai ba." daga haka ya ci gaba da tafiya zuwa wajen Dokinsa. Husnee dai sai rarraba ido ta ke yi duk ta rasa ma tunaninta gabaki aya. Amadu ne ya katse mata tunani da cewa "Innata ki na ganin mu bi shi ko kuwa?" bu e motar ta yi ta shiga ba tare da ta ce komai ba hakan ya sa shima ya shiga ya bata wuta ya shiga bin bayan Akhiee. Bakin wani masallaci ya tsaya wanda Almajirai ke ta karatu a ciki da wajensa. wajen Motar ya dawo ya an le a gami da cewa ''Ki jirani anan Asma'u! kai kuma ka zo mu shiga ciki" gya a kai ta yi gami da sa hannu ta buga tagumi ta na tunanin abinda ke shirin faruwa sai dai duk iya nazarinta ta kasa fahimtar komai. A cikin Masallaci kuwa gaban Babban Malamin Makarantar Allon su ka dur usa daga shi har Amadu. Malam Kabiru da fara'a akan fuskarsa ya ce "A'hh! yau an namy ne a gabana haka?" Akhiee ya ce "Ni ne Baba Kabiru, wata alfarma na zo ayi mini." Malam Kabiru ya jinjina kai cikin dattako da manyance ya ce "To ina saurara Allah i sa abinda bai fi arfina ba ne, duk ya wajen manyan ina Baban naku ya na lafiya? kwana da yawa ban zo mun gana ba" Akhiee ya gyara zama sannan ya ce "Yana lafiya, Aure nake so a aura mini a yanzu-yanzu, Baba Kabiru kai Aminin Mahaifina ne, hakan ne ya sa ba ni da wurin zuwa ayi mini haka in ba wurinka ba" Kamar saukar aradu haka Malam Kabiru ya ji maganar Akhiee ta fa o masa, tsananin mamaki da ka uwa su ka lullu e shi lokaci aya, sai dai abin manya sam bai nuna alama ba, cikin nutsuwa da kuma tattausar murya ya ce "Muhammad! Aure fa ba abin wasa ba ne, idan har da gaskr ka ke yi mini me yasa ba ka sanarwa Mahaifinka da an-uwansa ba? me yasa kuma sai yanzu-yanzu kake so a aura?" Sam ba ya son yawan tambaya don kuwa ransa aci yake yi, amma da yake Malam Kabiru tamkar uba yakw a wurinsa sai ya danne. Kai tsaye ya ce "Ba bu atar kowa ya sani har sai bayan anyi, ka manta da batun gaya musu kawai." "A'a fa, ko ba ka so Malam Muhammad ya sani ai ya kamata ko yayyenka ka sanarwa, Muhammad Aure fa ba a yi masa gaggawa, idan aka jira lokacinsa ya yi sai a yi shi cikin kwanciyar hankali, kafin aura Aure ana bu atar Dangin iya domin a gana a san juna kuma a nemi yardarsu."
Chapter 25 · 0% Book details