Sashe 18
Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ayeesha Abdulkareem INDO *M.W.A A take wani irin duhu ya rufe masa idanu ganinsa ya fara aukewa, hakan ne ya basu damar ci gaba da yankarsa; yanka uku su ka yi masa warara ya zube a wurin jini na shatata. su na ganin haka su ka ara a ta kare su ka bar wajen cike da farin ciki da murnar sun yi nasara. a sannu-sannu duhun da ya mamaye ganinsa ya fara washewa har ya bu e idanunsa tangaras, cikin arfin hali da tsaurin zuciya irin na shi ya mi e ya na takawa a hankali a hankali ya nufi makaranta, kafin ya kai ga zuwa tuni wa an da su ka ganshi a hanya sun je sun kwanzamawa su Sheikh Auwal nan fa duk hankalinsu ya tashi su ka bar cikin makaranta su ka fito wurinsa. Cikin tausayawa Sheikh Auwal ya ce "Akhiee maza mu je a kai ka Asibiti don ka na gu atar temakon likita." Kamar ba shi da kunne haka ya yi don kuwa ko alamar ya ji ma bai yi ba, Yasayyadi Usman ne ya dubi Sheikh Auwal cike da takaicin ba ar gaddama ta Akhiee ya ce "Ka ga irinta ko? ya na ji fa ba wai ba ya ji ba amma sabida an iska ne ya yi banza, ka je ka mutu ma mana ina ruwan wani?" Yasayyadi Muhsin ya ce "Ai shi dama hadari aya ba ya yi masa ruwa, Kai Akhiee ka zo tin da girma da arziki a kai ka Asibitin nan don wallahi jini na zuba a jikinka sosai." Cike da zafin rai gami da zafin ciwo ya ce ''Ku yaleni abina, ba ruwanku da ni tinda ba a jikinku ciwon yake ba kuma in na mutu ba ku da asara, duk ku watse ku ba ni wuri." Yasayyadi Jameel ya tausasa murya cikin sigar rarrashi ya ce "Yanzu ba lokacin wannan ba ne, duk ara ata lokacin da ka ke yi ara cutuwa ka ke yi, don Allah ka bar labarin yasayyadi Usman ka yale surutansa ka zo mu je." wani dogon tsaki ya doka ba tare da ya ara ce musu ko kanzil ba, sai lumshe idanu yake ya na cije gefen le ensa. Sheikh Auwal da Yasayyadi da sauran wasu daga cikin malaman har ma da ma ota sun taru akansa sai rarrashi su ke yi su na ha a shi da Allah da Annabi amma ya yi kafus, ya ce murje shi fa allambur ba wanda ya isa ya kai shi wani Asibiti. Haka su ka yi ta fama da shi har Tashin hankali ma ya sa sun manta sun baro alibai a ciki gashi har lokacin tashi ma ya wuce ana ta turnu u da shi. shi kuwa har lokacin girarsa aya ba ta karayaba. Magriba ce ke shirin rufawa amma a yau MADARASATU NOORUL ISLAM ba alamun za a sallami alibanta. Tin su na karatun da aka koyar da su cikin warin guiwa har su ka gaji wasu su ka fara yin shiru, ananu kuwa tuni wasu sun fara kuka sabida tsoro don sun yi tunanin anan za'a bar su su kwana. Husnee ce ta shafa cikinta da ke kukan yunwa kafin ta ce "Asiya wai lafiya kuwa? ace har yanzu ba malamin da mu ka gani bare ya sallamemu?" Zara ce ta le o tsakaninsu gami da cewa "Bari na je na duba ni dai wallahi na gaji a zo a sallamemu haba!" Husnee ta yi dariya ta na cewa "Yauwa anwar masu abin jeki don Allah." Harara ta maka mata kana ta fice. Ba ta wani da e ba ta dawo hankali a matu ar tashe, ganin haka ya sa zuciyar Husnee ta fara dukan sittin saba'in tamanin casa'in ari da hamsin! an Daba ne su ka sassari Akhiee, jini sai zuba ya ke yi a jikinsa amma ya i yarda a kai shi Asibiti, shine duk su ka taru a kansa, har babban Yayanmu ma ya zo amma ya i Amincewa, kuma wallahi ya na shan wahala sosai jininsa zai iya arewa" arasa maganar gami fashewa da kuka mai ta a zuciyar duk wani me imani. Husnee ta na jin haka ba ta bi ta kan Zara ba ta falla da gudu ta yo waje. Turmutsawa ta yi tsakankanin mutanen da su ka yi masa da'ira wanda yawanci Yayyensa ne.......... Gaba Da tambaya su ka isa ofar gidan jikinta sanyi salam haka ta fito daga mota ta na arewa tafkeken get in gidan kallo, yadda gidan yake tamfatsetse idan na shiga ina zan fara tinkara? tambayar da zuciyarta ta ke yi mata kenan. Kamar Amadu ya sani ya ce "Innata shiga za ki yi da Bismillah ki na addu'ar Allah i ha a ki da wanda ki ka sani kawai." Jinjina kai ta yi gami da sauke ajiyar Zuciya sannan ta nufi get in gabanta na ara fa uwa. Sallama ta yi a haraba ta na rarraba ido don ganin ta inda za'a ullo. Ji ta yi an amsa sallamar daga can gefenta ta yi saurin kai dubenta wurin, Hamza da Adamu ne zaune kan wata makekiyar tabarma sun tasa kofuna da fulas in shayi gaba da alama karin kumallo su ke yi ko kuma za su yi. Danne fargabarta ta yi ta an dubesu gami da cewa "Ina kwana!" duk idanunsu na kanta Hamza ya yi zaram ya amsa ya na fara'a. Cikin kame-kame ta ce ''Um!..in..ina ne... zan ga Akhiee?" Idanunsu ne su ka ara girma su ka yi kallon kallo cikin madarar mamaki, Adamu ne ya yi saurin shiga zancen da cewa "Waye kuma Akhiee ? daga ina ki ke meye ha inki da shi??" baki na rawa ta ce "Muhammad Risslan fa ni...ni..a..." kasa arasa maganar ta yi sabida kuka da ke shirin kufce mata. Hamza ya karka e mazaunar rigarsa ya mi e ya na cewa "Abin ya ara girma kenan, bari dai in matso in ji yadda ake ciki." ar ajinmu ce ita, kuma ta zo duba lafiyarsa ne, Husnee sannu da zuwa mu je in raka ki wurinsa." Zara da ta iso yanzu ta basu amsar tambayarsu, kana ta ja hannun Husnee su ka kutsa kai ciki. e ha a Hamza ya yu ya na cewa "Iyye? neman mata ma ya fara yi kenan? to Allah i sauwa e lallai Abhi ya haifi bala'i." Adamu ya ta e baki ya na cewa " addararre ni wallahi na so ma sun kashe shi kawai mu huta aikin banza, kullum sai ya yi mana ba in tambari ya gada mana abin magana sannan ya ke jin da i, ya gama gur ata kima da mutuncin Ahalinmu." Hamza ya ce "Ni ma da hakan ta faru ai sai na fi kowa murna wallahi, yanzu ga dai wannan yarinya har yarinya amma ya lalatata." Adamu ya ce "Umm! to ya za mu yi haka za mu suba ido har sai ya mutu sannan mu huta, an wahala kawai." Masifa su ka ci gaba da zazzagawa kowa na tofa albarkacin bakinsa wanda yawanci ba alkairi su ke fa e akan Akhiee ba. Sai da su ka ara shiga ciki Husnee ta ara tabbatar da girman gidan, sashi kala daban-daban ga akuna rututu haka mutane yara manya maza mata duk gasu nan a hakan ma wasu sun tafi makaranta, matan gidan da ananun yara sun fi yawa sai samari su na ta shirin fita kasuwa. Ita dai kamar arauniya haka ta ke tafiya sa af-sa af sai fi i-fi i ta ke yi da idanu kamar an tarfa munafuka. Duk wanda ya lura da su sai ya tambayi wacece da uwar safiyar nan ta zo musu gida musamman matan gidan, sai Zara ta yi zaram ta ce ar ajinsu ce sai kuwa su ta e baki. Da haka su ka isa can arshen gidan. inda ba mutane wuri ne a an kewaye wanda za a iya kiransa gida arami me aki aya sai ban aki da wani aramin aki wanda bai kai a kira shi aki ba sai an tsakar gida ba wani babba ba, wurin shiru sai iskar safiya da ke ka awa a hankali a hankali don kuwa wurin ya yi nesa da cikin jama'a sosai kwata- kwata bai ala anci wani sashi na mutan gidan ba. Husnee dai da bata iya gani ta yi shiru sai da ta kalli Zara ta ce "Ni ban ta a ganin i da tsangwama ba sai a gidanku, wato akin nasa ma shine a can bayan gari inda ba mutane, wajen kwanan ma sai an nuna bambanci ko?" Zara ta ce "Ai ba laifina ba ne Husnee nima tinda na yi wayo a nan na ga ya na kwana tin kafin ya girma shima, ban sani ba ko shi ya za i hakan ko su su ka za a masa, amma ba me shigowa ma sai in baya nan ko kuma dai wani babban abu ya kawo mutum." Daidai lokacin Zara ta kutsa kai cikin akin nasa tare da sallama, Husnee kuwa dakatawa ta yi domin a bata izini sannan ta shiga. Turus Zara ta yi ganin Wata kyakkyawar budurwa wadda ba ta wuce shekaru daidai na da na Husnee ba zaune ku sa da shi idanunta sun yi jajir sun yi ulu- ulu da zarar me hankali ya kalla ko ba a fa a ba ya san kuka ta ci har ta godewa Allah, har yanzu ma akwai sauran hawayen akan dogayen gargasar idanunta. Akhiee kuwa ya na zaune bisa aramin gadonsa wanda aka shimfi e shi da kyakkyawan bargo duniyar kuliya. abin ya bala'in bawa Zara mamaki don kuwa kaf shirin akin da su ka yi ita da Sheikh Auwal an canja shi ciki kuwa har da wasu abubuwan irin su bedsheet pillows da sauransu. Idanu ya zubawa Zara alamar tambaya, ta yi asa da kai zuciyarta sam ba da i ta ce ""Husnee ce ta zo dubaka shine na rakota." Juyawa ya yi ya zubawa ar budurwar ido a na yi mata wani shegen kallo me cike da alamomi daban-daban. Zirrrrrr!!! hawayen su ka ara biyo kan kumatunta. Tsaki ya yi kafin ya bu i baki a hankali ya ce "Ta shigo kawai." Zara ta juya gami da cewa "Ki shigo Husnee" ba za ta iya komawa