Sashe 27
Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ayeesha Abdulkareem INDO *M.W.A "Wannan shine Wakilinta" ya fa a ya na nuna Amadu, kafin ya ora da cewa "Ni kuma kai za ka yi mini komai; Ba na so na aikata ba daidai ba shi yasa na ke bin komai a maslaha." (Ohh! ni Indo su Amadu an zama Wakili Zaro ido Amadu ya yi cikin matu ar razani da firgici ya ce "Iye? wallahi Malam Allah aya ba zan iya ba, a je a nemo wani dai don Allah." wani shegen kallo Akhiee ya aika masa wanda ya sa shi saurin ha iye surutun nasa. Malam Kabiru ya san halin Akhiee sarai, zai iya tu e rigar kunya ya zuba masa rashin mutunci duk da cewar Abokin babansa ne don haka ya jinjina kai kana ya ce "Shi kenan, na san zan iya yi maka komai amma ina son sanin dalilin da ya sa kake so ayi hakan." "Ina so ta dawo ashin kulawata ne sabida za'a iya cutar mini da ita idan na tsaya ata lokaci, Yanzu abin da za'ayi ka tattaro dattawan Abokanka innan ku yi komai tare." Malam Kabir ya ce "To Sadaki fa?" "Yanzu za a kawo" ya fa a a ta aice. Malam Kabir dai a gefe cike yake da fargabar aura auren don kar wani abun ya je ya zo, a gefe guda kuma ya na shakkar iya shegen Akhiee, don haka ba shi da za in da ya wuce ya aura Auren kawai a huta. aya daga cikin alibansa ya tasa ya ce ya je ya gayyato masa Dattawan da ke zaune a wajen Masallaci. Ba tare da wata da ewa ba suka shigo Tare da su Salansa. Kusa da Akhiee ya zauna sannan ya mi o masa ku in, Akhiee ya ce "Ka lissafa?" "Eh Dubu Tamanin ne kamar yadda ka ce" bai ce komai ba ya mi awa Malam Kabiru gami da cewa "Ga shi nan idan da ciko su yi bayani zan basu ko nawa suke bu ata." Malam Musa ne ya dubi Malam Kabir cikin rashin fahimtar abinda ke faruwa ya ce "Me za a yi ne Malam?" Dalla- dalla Malam Kabir ya yi musu bayanin duk abinda ya faru da kuma wanda zai faru anan gaba, ba su yi musu ba su ka gyara zama domin aura Aure. Malam Kabir ya mi awa Amadu da ya gama rikicewa ku in gami da cewa "To gashi, idan an yiwa iyayenta bayani idan suna bu atar wani abin sai a sanar" Amadu ya kar a hannunsa na rawar mazari, ko uffan ma ya kasa cewa. Tare da sauran aliban Malam Kabiru manyansu da yaransu aka aura Auren. Bayan an gama su Gwaja su ka kawo Alewa da Biskit da Dabino aka rarraba, sannan kowa ya san inda dare ya yi masa. Akhiee ma sallama ya yiwa Malam Kabiru sannan ya fito, su Salansa na biye da shi ciki kuwa har da Amadu da jikinsa duk ya gama mutuwa. Ta na ganin sun fito ta fito daga cikin motar ta tsaya ta na binsa da kallo. Tinda su Gwaja su ka fa a mata abinda aka yi ta fara kuka ta cika da tsoro da fargabar abinda za ta tarar a gidansu. Har ya araso inda take shi take kallo har ya zo gaf da ita, idanunsa masu matu aukar hankali ya zuba mata ya na jin kukan nata har cikin ransa, wani farin hankicif ya zaro a Aljihunsa ya fara goge mata wallar ya na hura mata iskar bakinsa a hankali, hakan ya sa ta fara fizgar numfashi ta na sauke ajiyar Zuciya, cikin wata tattausar murya wadda duk wanda ya jita zai so ya ara saurarenta ya ce "I'm so sorry Asma'u, ba ni da za in da ya wuce haka, Allah ya riga ya addara ke ce abokiyar rayuwata, kuma abubuwa da yawa na cutarwa su na bibiyar rayuwarki shi yasa na yanke wannan hukuncin, da zarar na kai ki gidanmu babu wani abu da zai ara barazana wa rayuwarki sai dai in kin fito daga cikinsa." an jinkirtawa ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Ki dena kuka, ko da duk Duniya za ta juya miki baya ni ina tare da ke, tinda ki na so na a ganina ba abin tashin hankali ba ne hakan, kuma ba na yi ne dan na ata miki ba sai dan ba na son na ga kin cutu, ki na da muhimmanci a rayuwata kuma ke ta musamman ce a wurina; Yanzu ki bi Amadu ya kai ki gida kafin na zo aukarki." Sunkuyar da kanta ta yi asa zuciyarta cike da tunane-tunane, ganin ta kasa ko motsawa ya sa shi kamo hannunta ya bu e mata motar gami da cewa "Shiga mana" shigar ta yi har lokacin ba ta ce ko uffan ba, wata tamfatsetsiyar waya ya zaro cikin Aljihunsa ya mi a mata gami da cewa "Ga wannan a koda yaushe idan ki na nemana za ki sameni, lambobin ciki duk nawa ne." a ta yi gami da gya a kai ba tare da ta yi magana ba, ido ya zuba mata a ransa ya na jin kamar ya tafi da ita tin a yanzu sai dai ya na so iyayenta su fara sani ya ga iya gudun ruwansu, don ya san mawuyaci ne su amince da shi. Cikin sigar zolaya Salansa ya ce "Me House ko za ka bi ta ne?" rufe motar ya yi gami da yin baya, Su Salansa kuwa sai dariya suke a ciki-ciki don kar ya ji su. Amadu ne ya matso kusa da shi kamar zai fashe da kuka ya ce "To Yalla ai ni dai wannan a a matsayin amana take a wurina da zarar na rabota da gidan iyayenta, sai gashi yanzu kai kuma ka mallaketa ta hanyata ba ta hanyar iyayenta ba, nima na shiga matsala ban san wane kallo za su yiwa hakan ba, ina fatan ba don cutarwa ka yiwa wannan baiwar Allah haka ba." Dafa kafa arsa ya yi kafin ya fara magana cikin salonsa na izza "Ita in matata ce kuma mallakina, Ka kula mini da ita sosai, ba ka cikin matsala don kuwa ina da kafa un da zan iya aukar komai akanta, inda zan iya cutar da Asma'u da na da e da rabata da rayuwarta ko kuma wani abu mafi muhimmanci nata, ku je kawai a gaishe mini da mutan gidan". Amadu ya jinjina kai, yanzu ya samu warin guiwar da zai iya komawa gidan sa anin da da ya cika da tsoro. Sai da motarsu ta bar layin sannan Akhiee da tawagarsa su ka aga. Kai tsaye Makwantarsu su ka koma inda suke yiwa la abi da suna Masarautar Sar Har cikin Fadarsa su ka raka shi a memakon su bashi wuri kuma sai su ka zauna su ka mamaye shi, kowa cikinsa cike taff da tambayoyin da yake son yi masa, ciki kuwa har da su Laita da duk sauran yaransa. Zabira ce ta fara bu e musu fagen tambayar da cewa "Wai dama ka na soyayya Abba?" Da sauri an Bakwai ya ce "Yauwa!! abinda nake son ji kenan nima, da ina da ke kanki ya na kawo wuta ta gidana" Nan fa kowa ya fara tarkato tashi tambayar ya na jefowa, shi kuwa Akhiee sai shan wiwi insa yake yi ya i cewa komai. Sai da su ka gama su ka fara yin slow sannan ya an yi gyaran murya duk su ka nutsu, "Ni ba na soyayya hasalima ban san ya akeyinta ba, abinda nake so ku sani shine Asma'u ita ka ai gareni, idan a cikinku ne aka illata wani to ina da wani, amma ita duk Duniya ba ni da tamkarta, kuma ba ni da wadda za ta zamo kamarta, duk tsawon rayuwarku da ni bayan Iyalina akwai wata mace da kuka ta a ganin ina saurara?" amsawa su ka yi da "A'a" ya ci gaba da cewa ''Nima kaina na yi mamakin ta yadda aka yi na fara saurararta har ta yi nasarar sa ni abubuwa da dama a cikin wa anda ba na yinsu, haka kawai nake jinta tamkar Ruhina idan aka cutar da ita tabbas an yi mini babbar cuta, hakan ne ya sa nake so ta dawo ashin kulawata hankalina zai fi kwanciya, ga bayani nan na yi muku wanda bai fahimta ba kuma ba zai ta a fahimta ba don haka ku tashi ku ban wuri ba na bu atarku a yanzu." ewa su ka yi su na ta murna su ka rankaya su ka yi waje, can gefe su ka ha a majalisa su ka fara tattaunawa, Gwaja ya ce "Ai na godewa Allah tinda yanzu ya samu mata mu ma ila zai barmu mu dinga kula mata har mu yi Aure" "Mewtchh!!!" Salansa ya doka tsaki kafin ya ci gaba da cewa "Kai ta Aure ma ka ke yi, idan shi ya iya kula da ita kai yadda kake kai a sama innan ba abinda za ka iya yi mata, arshe ka sa ya kasheka a banza" an sassauta murya yayi kafin ya ce "Wai kun san me? ya ce bai san so ba ko? to wallahi sonta yake yi." Laita ta yi dariya kafin ta ce ''Bar an iska ya na son kayarsa mana." su ka ara kwashewa da dariya, hira su ka ci gaba da yi cikin farin ciki domin kuwa su da i abin ya yi musu. angaren Husnee kuwa kamar arauniya haka ta shiga gida da san a, ta yi muzu-muzu da ita kamar ji iyar kaza. Mommy da Yaya Muddassir su na zaune su na hirar yaushe gamo ta shigo Falon cikin takunta me kama da na masu koyo. Yaya Muddassir ya bita da kallo kafin ya ce "Lafiya kuwa anwata?" kusa da shi ta zauna kafin ta yi magana cikin muryarta da ta dishe, "Lafiya lau" Mommy ta ce "Lafiyar Kura ba? in gaya maka gaskiya sai an ha a da addu'a don kuwa Aljanu ne su ka shafeta, ka ga yadda tafita azu lafiyar Allah ko? to ka ga yanzu yadda ta dawo, to haka take kan da lafiya jikin ba da i, kwanaki haka su ka dinga lallan wasa kamar tsutsa, ni dai naga abin al'ajabi, na