Sashe 16
Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ayeesha Abdulkareem INDO *M.W.A an Daba ne su ka sassari Akhiee jini sai Zuba yake a jikinsa amma ya i yarda a kai shi Asibiti, shine duk su ka taru akansa, har babban yayanmu ma ya zo amma ya i Amincewa kuma wallahi ya na shan wahala sosai jininsa zai iya arewa" arasa maganar gami da fashewa da kuka mai ta a zuciyar duk wani me imani. Husnee ta na jin haka ba ta bi ta kan Zara ba ta falla da gudu ta yo waje. Turmutsawa ta yi tsakankanin mutanen da su ka yi masa da'ira wanda yawancinsu yayyensa. Ya na tsaye ya jingina da bango sai asa- asa yake da idanunsa da su ka ara wani irin haske wayar idon ta ara riki a ta yi ba i si ik, fuskarsa ma kanta ta yi jawur sabida tsabar zafin rai da kuma azabar da yake ji a jikinsa, ganin yadda jini ya ji a shaddar jikinsa me ruwan toka ta koma ja ya sa Husnee fashewa da kukan da sai da ta sa shi agowa ya zuba mata ido, ba ma shi ka ai ba duk mutanen wurin idanu su ka zuba mata cike da mamakin tsaurin ido irin nata, ba su gama firgita ba sai da su ka ji Tassss!!!!! arar marin da ta she a masa ya kara e kunnuwansu, cikin shashshekar kuka ta ce "Akhiee me yasa ba ka san ciwon kanka bane!!!? don me ba za ka je asibiti ba ka na fama da wannan rauni a jikinka?" Cikin muryar da ke fita yar ya ce "Asma'u! ki yale ni ko mutuwa na yi ba su da asara tinda ba aunata su ke yi ba." cikin tsananin acin rai ta daki irjinsa cikin tsawa tace " arya ka ke yi Akhiee!!! wanda ba ya aunarka ba zai so lafiyarka ba!!, yanzu duk wannan tashin hankalin da su ka shiga ka na nufin ba auna bace?? wallahi tallahi indai ba ka je ba nima sai na ji wa kaina, idan ka mutu kai ka tafi kenan mu za ka bari da tunaninka!!!!" ta arasa maganar gami da fashewa da wani sabon azababben kukan, "Asma'u ba zan iya ba ki yale..." ba ta bashi damar arasa maganar ba ta ara kwarfa masa wani shegen mari wanda ya sa ganinsa ya auke na wucin gadi, kamar za ta yi hauka ta ce "Kar na ara jin zancen banzar nan a bakinka! in ba haka ba zan yi abinda ba zai yi maka da i ba wallahi." sassautawa ya yi kafin ya ce "Asma'u Calm down cuta fa ba mutuwa ba ce, amma ba na so ki cutu sabida ni, zan so a ce kin rabu da ni kawai" "In dai ka na so hankalina ya kwanta ka bi an uwanka su kai ka asibiti, in ba haka ba nima...." katseta ya yi da cewa "Na yarda zan je amma ki gaggauta tafiya gida." Daga haka ya ra e ta kusa da ita ya wuce, a kusa da Sheikh Auwal ya tsaya ba tare da ya kalle shi ba ya ce "Mu je" Sheikh Auwal ya ri e hannunsa su ka nufi wajen mota, su Yasayyadi Jameel da IP Khalil wanda aka gaiyato tin azu su ka mara musu baya. a wurin Husnee ta zube ta na ara sakin kuka me tsuma zuciya. Zara ce ta dafa kafa ar ta na walla ta ce "Na gode Husnee kin temakemu ba don ke ba na san ko me zai same shi ba zai ta a yarda ya je ba, ki tashi ki tafi gida ki dena kuka anan kin ga mutane su na kallonki." Husnee ba ta iya cewa komai ba sabida kukan da take yi, sai da Zara ta yi da gaske sannan ta yarda ta shiga mota Amadu ya ja su ka nufi hanyar gida. har su ka isa ba ta dena kukan ba ta na shiga gidan ta wuce aki ta fa a gado ta ci gaba da abinta, Mommy da hankalinta ya gama tashi ta yi mata tambayar duniya amma ta yi banza, jikinta ya yi sanyi tuni ta fara tunanin ko dai da gaske Aljanu ne su ka shafeta. Tunanin Amadu Direba ne ya fa o mata don haka ta yanke shawarar tambayarsa, ya na zaune ya yi jugum akan an bencin me gadi ta iso wajen cikin sanyin jiki, gaisheta ya yi ta amsa ba yabo ba fallasa kana ta ce "Na ga Husnee ta shigo gida ta na ta kuka, na yi tambayar duniya ta i yi mini magana." Amadu shima kamar zai fashe da kukan ya ce "Wallahi Hajiya tashin hankali ta gani wanda dole ta yi kuka, ko ke Hajiya in ki ka gani ila sai kin yi hawaye don mata kuna da rauni sosai." hankalin Mommy ne ya ara tashi, ta zaro idanu gami da cewa "Me ya faru ni Salamatu!" Amadu ya ce "Hajiya Yaron masu makarantarsu ne an daba su ka sassare shi, kar ki ga yadda su ka yi masa jina-jina amma sabida zafin rai da gardama yaron nan sai ya i a kaishi Asibiti, da kin ganshi kin san ya galabaita amma wallahi sabida taurin kai irin na an daba sai ya i, in ki ka ga jinin da ya zubar za ki koka masa Hajiya." Mommy ta ce "Ikon Allah, Allahu Akhbar Allah i bashi lafiya, kowa dai da irin addararsa shi kuma irin ta shi kenan! Allah ya bi masa ha insa in cutarsa su ka yi." Amadu ya ce "Amin Hajiya" jiki ba wari ta koma cikin gidan, wajen Husnee ta koma ta zauna gefenta ta fara rarrashinta gami da kwantar mata da hankali. Ba su suka dawo gida ba sai arfe 11:00 na dare, a hakan ma gado asibitin su ka so ba shi amma ya tubure ya ce indai su ka kwantar da shi duk sai ya arasa sauran marasa lafiyan da suke tare jin haka ya sa su ka tarkata shi su ka dawo da shi gida. Sheikh Auwal da Zara ne su ka gyara masa akinsa su ka yi masa kyakkyawar shimfi a gami da ajiye masa abubuwan ciye-ciye na marmari kala daban-daban sakamakon jinin da ya zubar. Sauran mazan kuwa duk sun watse sai matayensu da matan Abhi da kuma sauran an uwan nasa su ke ta le o shi, wasu su ce Allahi i sauwa e wasu su yar masa da magana su yi gaba. Shi dai ko kanzil bai furtawa kowa ba hasalima ba ya ora hankalinsa akansu don in ransa ya aci duk zai iya yi masa illa. Da zazza i Husnee ta kwana, amma hakan bai hana ta shiryawa don zuwa makaranta ba kasancewar ranar lahadi ce ba za ta je boko ba don haka ta shirya tin sassafe. Ta na fitowa Mommy ta ce "A'ah Husnee lafiyarki alau kuwa? da zazza i ki ka kwana fa har da surutai marasa kan gado amma yanzu kin auki uban hijabi kin zurma kin ce za ki je makaranta, kya bari ai jikinki ya yi wari." "Ni na ji sau i Mommy, ba zan iya zama a gida ba hakan shine zai ara mini zazza in ma, don Allah ki barni in tafi Mommy. Mommy ta rausayar da kai kamar marigayin zakara gami da cewa "Allah i tsare sai ki kula sosai, ni ban ta a ganin makarantar da ki ke so da auna ki ka nacewa zuwanta irin wannan ba, Allah ne masanin abinda ke oye a cikin hakan" Husnee dai ba ta ce ala ba tuni ta wuce hanyar fita. Ta yi sa'a ba ta yi karo da wani ba har su ka fice daga gidan ita da Amadu direba. "Innata ya jikin naki na ji Khausar ta ce ba ki da lafiya" ya fa a cikin tausayawa "Na ji sau i Malam Amadu, don Allah ka kaini gidan su Akhiee idan ka sani. Durumm!! Bom in zuciyarsa ya tashi sabida jin abinda ta fa a, cikin sauri ya ce "A'a Innata ki shafa min lafiya in kai ki makaranta don nan aka sa ni in dinga kai ki." "Malam Amadu kai ma ka shafa mini lafiya ka kaini in ganshi ko hankalina zai kwanta, zazza in da na ke yi kawai tunanin halin da yake ciki ne ya kawo hakan, kwana na yi ina mafarkai kala-kala akansa, har mafarki nayi ni ce me jinyarsa ina kusa da shi ina yi masa komai, sai da na farka na ga mafarki ne sai na ji haushi don na so ace da gaske ne. Amadu ya jinjina kai cike da tausayinta, zuwa yanzu ya lura gabaki aya hankalinta ya koma kan Akhiee, me kuwa za a yi mata wanda ya wuce a tausaya mata, ta na da uruciyarta da hankalinta amma za ta lalata ta hanyar wannan babban tantirin, abin da yake tunani a zuciyarsa kenan, a zahiri kuwa bai ce mata uffan ba. *************************** White diamond watch da ke hannunsa ya kalla kafin ya yi magana cikin muryar da ba hayaniya ba tashin hankali, "Asma'u Please! It's time for prayer, i'm going to the masque" "Please Akhiee you listen to me!" ta arasa maganar gami da fashewa da kuka........ Fararen idanunsa masu tamkar nono ya zuba mata har na an lokaci sannan ya ce "Kukan naki zan saurara kenan??" girgiza kai ta yi ta na arin goge hawayen cikin sauri, dandanan ta tsayar da kukan ta goge wallar kamar ba ita ke kukan ba sai dai da an kalleta za a gane ta yi, ido ta zuba masa sai kuma ta rasa abin ce masa, sai da ya ce "Go ahead!" sannan ta yi zumbur ta sauke nannauyar ajiyar zuciya gami da tattaro dukkan nutsuwarta, cikin sanyin jiki ta ce "Akhiee ban san abinda ya faru ba ranar nan, na ji su Yasayyadi Usman sai tambayoyi su ke yi mini, na ga mutanen makarantar nan sai wani irin kallo su ke yi mini, gashi kai kuma ka i zuwa bare na ji da i, ina arin zuwa makaranta kullum sabida in ganka, amma kai ba ka son ganina." Lumshe idanunsa ya yi ya bu e a hankali ya ce "Za ki fa i ne shine na yi arin tsayar da ke sai kuma na