Sashe 37
Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yayin da hannunta ke ma ale cikin tafin nasa hannun. Sun da e su na kallon kallo kafin ya kawar da kai, ya sassauta murya sannan ya ce "Asma'u in na rasa ki ne akwai tashin hankali, zan yi arna sosai domin kuwa haukacewa zan yi!!! don Allah ki tayani kula da kanki kar ki bari a illata mini ke." asa ta yi da kai ba tare da tace komai ba, sai a lokacin zafafan hawayen da ke kawo-kora a cikin idanunta su ka samu nasarar zillowa su ka yo wajen. lumshe idanunsa ya yi gami da sauke nannauyar ajiyar Zuciya. A hankali ya bu e idanun gami da zubawa kyakkyawar fuskarta su, cikin wata irin murya me rikita lissafin me saurarenta ya ce "Da gaske nake Asma'u, ba na iya oye miki sirrin Zuciyata, tabbas idan aka cutar da ke an yi mini Lahani, ki tausayawa Mijinki Asma'utah!!." wani mugun ha en shauki ne ya ratsata ta ko'ina, ba ta san lokacin da ta Fa a cikin faffa irjinsa ta na ara sakin wani sabon kuka me unshe da wani salo da sirrin shagwa a ba. Dimm!!! dimm!!! bugun Zuciyarsa ya ara sauya salo, hannayensa ya sa duka biyun ya zagayota gami da gyara mata kwanciya a jikinsa, cikin sassanyar murya ya ce "Ba na son jin kukan nan Asma'u, ko so kike Zuciyata ta karye??" ba tare da ta dena kukan ba ta girgiza masa kai. A hankali sautin bugun Zuciyarsa ya fara sauya mata tunani hakan ya sa ta yi shiru ta na sauraren Zuciyar tashi. Jin ta nutsuwa ne ya bashi damar zaro wani siririn Diamond ring aya daga cikin Zobuka goma da ke hannunsa, ya ri o hannunta na dama ya zubawa zaratan yatsun natsa ido kafin ya zura mata shi a na kusa da na tsakiya, wato na kusa da aramin yatsa. arin zamewa daga jikinsa ta fara yi amma ya i bata dama, cikin muryarsa me sanya mata nutsuwa a duk lokacin da ta saurara ya ce "Kasancewarki tare da Zoben nan tamkar kasancewa tare da Mijinki ne, kar ki bari ya fita daga hannunki komai wuya komai rintsi." a kai ta yi alamar eh, don haka ya ya bu e hannayensa gami da cewa "To jeki gida, kar ki ara fitowa fa." "To" ta fa a tare da sauke nannauyar ajiyar Zuciya. Ya na tsaye har ta shige gida sannan ya ace ya yi nasa wuri. Hajiya Laure Da Hajiya Saudah..... Wani ha en Sa ago su ka gani ya na tinkaro su, ya na tafiya cokal!! cokal!!! cokal!!!! da siri-sirin afafunsa tamkar za su karye, sai uban kai rangwameme kamar zai rinjayi Wuyansa, gashi wargwan- wargwan zallar ashi sai tarin muni, ga ramin ido zuru-zuru ga ha ora kacar!!! kamar tsangayar ashi. Wannan Dalilin ne ya sa su ka ara shiga Firgici bayan wanda suke ciki, har ya jawowa Haj Saudah suma. Hajiya Laure kuwa kururuwa kawai ta ke yi idanunta a rintse. Ta da e cikin wannan yanayi na tashin hankali da fitar hayyaci idanunta a rintse, bayan ta auki lokaci me tsayi ba ta ji ta mutu ko kuma ta shiga hannun Sa agon ba ya sa ta sassauta ihun da take yi ta fara bu e idanunta da suka aure suke wata azaba tamkar an yi dakan Barkono a cikinsu, a hankali a hankali har ta bu e idanun nata garas! ta shiga arewa wajen kallo, ganin babu wannan sa ago ba alamunsa ya sa ta sakin ajiyar Zuciya wadda ta tawo tare da wani sassanyan kuka na da Da rarrafe ta arasa wajen da Haj Saudah ke kwance kamar gawar sababi, ta fara jijjigata ta na kiran sunanta amma shiru, wani sabon kukan ta saki ta na cewa "Wayyo Allah yanzu ya zan yi idan Saudah Mutuwa ta yi ai na shiga uku." Zama dafa'an ta yi ta na rero baitin kuka kamar don shi aka kawota Duniyar. Bayan wani an lokaci ne ta tuna da Motar da su ka zo ba za a rasa ruwa ba don haka ta tashi ta na jan afafunta da su ka yi tsami ta isa wajen Motar, cikin sa'a ta na dubawa ta samu ta akko ta dawo wajen Haj Saudah ta yayyafa mata ruwan. A firgice ta farka ba tare da ta jira wani abu ba ta mi e za ta ci gaba da gudu, Haj Laure ta sa iya arfinta ta ri ota ta na cewa "Ki tsaya mana, tinda Allah ya sa kin farko ki yi maza ki shiga Mota mu gudu." Haj Saudah ta na jin haka ta yi saurin bu e Motar ta shige ta rufe baram don kar ma wani abun ya biyota. Haj Laure ma cikin sauri ta akko wata babbar Darduma da ta gani a cikin Motar ta aura a ugunta domin oye acin da kayan jikinta su ka yi. Haj Saudah ta zama ba baka sai kunne, Haj Laure ma ba magana, tinda ta fara tu a motar Ta ke an addu'o'inta ta kama waccan ta saki ta kama waccan. Sai da ta biya ta ajiye Haj Saudah ko sallama ba su yi ba ta shige gidanta, Haj Laure ma ta arasa nata gidan da yar don kuwa tuni zazza i ya rufeta. Yazeed na gama yin parking itama ta yi parking ta fito da kyar da kyar, turuss!! ya tsaya ya na kallonta sabida ganinta wujiga-wujiga kamar an watota daga bakin kura, ga Darduma da ta aura a ugu jikinta ko mayafi babu. Cikin tsananin mamaki ya ce "Mommy! meye haka kuma?? lafiya??" wata sahihiyar kunya ce ta lullu eta sai ta ma kasa aga ido ta kalli an nata bare ta san amsar da zata bashi, su ur-su ur ta yi cikin gidan ba tare da ta saurare shi ba. Talatu ce kawai a Falon a lokacin da ta shigo, Talatu ta zuba mata ido cike da mamaki, "Sannu da zuwa Hajiya" ta fa a ta na ara zuba mata ido. Banza ta yi mata, tsabar ba in ciki da takaici ji take kamar ta ha iyi Zuciya ta mutu, kai tsaye akinta ta nufa daga can ma ta wuce Toilet domin gyara jikinta. Yazeed kuwa tinda ya saki baki ya fara tunane-tunane sai da ya kwashi lokaci me tsayi sannan ya samu warin guiwar shiga cikin gidan, Zuciyarsa cike taf da tambayoyi akan Mommynsa. Husnee ta na shiga cikin gidan ta yi kaci us da Momy a tsaye sai safa da marwa take yi hankalinta a matu ar tashe. e-ra e ta fara yi Zuciyarta na tsananin bugawa, daga ganin yadda ran Mommy yake a ace ta san itama nata ran zai aci. Mommy kuwa ta na ganinta ta yo kanta ta na cewa "Zo Dan ubanki!! wato kin kangare ba kya jin magana ko??" Cikin rawar murya ta ce "Don Allah Mommy ki yi ha uri ba zan ara......" shiru ta yi sabida fizgota da Mommy ta yi ta fara irka mata dundu da iya arfinta ta na yi ta na cewa "Dan Ubanki ashe da afarki ki fita? kin tashi hankalina na zata ma sace ki aka yi; gidan uban wa kika je???" Kuka kawai ta ke yi ta na bata ha uri amma ba ta fasa ba sai da ta gaji tukunna ta saketa, a hakan ma ba ta ha ura ba ta ci gaba da fa a kamar ta ari baki. Husnee ta ja afarta da kyar za ta wuce ciki ta na tafe ta na sharar walla, aga hannun da ta yi ya bawa Mommy Damar ganin Zoben da Akhiee ya bata, ta sanya salati kafin ta ci gaba da cewa "Zo in gani, uban waye ya baki Zoben nan?? wato wajen an iskan Yaron nan kika je ko? sabida ke ga gantalalliya mara mafa a, to ba dani ba zo ki cireshi ko kuma in yi miki dukan kawo gishiri yanzun nan." jin abinda Mommy ta ce ya sata sake fashewa da wani sabon kuka me cike da tashin hankali gami da tausayin kanta. oye hannun ta yi a baya ta na ce "Don Allah Mommy kar ki cire mini ki bar mini shi, wallahi in na cire ransa aci zai yi!!!". Kuka take yi tamkar ranta zai fita amma hakan bai sa Mommy ta tausaya mata ba. Cikin tsawa ta ce "Ni kike gayawa ransa xai aci?? iye??? ni abokiyar wasanki ce ina magana kina magana???" Girgiza kai ta shiga yi domin kuwa ta kasa magana sabida kukanta da ke ara arfi. Fizgota Mommy ta yi ta na arin cire zoben, Husnee kuwa ta dam e hannunta katamau ta na kuka harda shi ewa. Daidai lokacin Muddassir ya yi sallama ganin su na ta kici-kici ya sa shi saurin arasowa ya na cewa "Lafiya kuwa, me ya faru??" cikin acin rai Mommy ta ce "Wai Yarinyar nan sabida ta rainamu ta mayar da mu mutanen banza ita ce da fita ta tafi wajen wannan an iskan harda kar ar zobe a hannunsa?, Ni fa ba za ta jawo min zagi ba gwara in sha areta in ta mutu ma dan ubanta ba ni da asara." Karyar da murya ya yi kamar wani mutumin kirki ya fara cewa "Haba dai Mommy, don zobe dai? don Allah yale mata mana haba? ba wani abin tashin hankali ba ne, shi so ai ba a yi masa shamaki ku barta ta rayu da wanda take so don Allah." Mommy ta ce "Haba kai ma fa e kake yi!, ina sane dai da hankalina ka san ba zan aurar da ata a inda za ta dinga ci da haram ba, Yaro an ta'adda, ta adari, an iska, an daba shi kake cewa mu bashi armu? " "To wai Mommy ba Allah ne me shiryawa ba? addu'a ya kamata mu yi masa ba mu dinga kiransa haka ba, don Allah Mommy kwantar da hankalinki; ke Husnee wuce ciki" ya arasa maganar ya na kallonta, jin haka kuwa ya sa ta yi zuruf ta wuce ta na ci gaba da razga kuka. Mommy ta raka bayanta da harara kafin ta yi wafa alamar zamu ara ha uwa. Muddassir kuwa kwantar da kai ya yi ya dinga rarrashin Mommy gami da ha urtar da ita, ba don komai ba