Sashe 14
Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ayeesha Abdulkareem INDO *M.W.A Zakin Ya na direwa a gefe ya zamo mutum, kamanninsa da tsayinsa da komai irin na Akhiee ne sak har kayan jikinsa, dariya ya yi hakan ya ara fito da tsantsar kyawunsa, cike da zolaya ya ce "Yau duk ina zafin kan naka?" Daidai lokacin Akhiee ya yo fitar burgu daga cikin ruwan tare da wurgo masa wata shar uyar wu a fara tarr sai yall da aukar ido take, cikin hanzari ya yi gwauron tashi ya dire a gefe har lokacin dariya yake yi wadda take ara dugunzuma zuciyar Akhiee, jikinsa har kakkarwa ya ke yi sabida acin rai, "Na rantse da Allah Russlan ka bari na kamaka sai na kakkarya ka, na gaya maka ba na son wasan banzan nan naka ko? ka barni da abinda yake damuna amma ka zo ka na ara tunzura ni; za ka sa na yi arnar da ba za ta yiwa kowa da i ba wallahi." Ya yi maganar ba tare da alamun wasa ba, jin haka ya sa Russlan ya dakatar da dariyar, cikin sigar rarrashi ya ce "Yi ha uri mana, ai abin bai yi zafi haka ba, ni ban san ranka a ace yake ba Allah i baka ha uri jarababbe." jin ya kira shi da jarababbe ya sa ya ara hassala, ya bu i baki zai ara zaro wata maganar Mother ta iso wajen, cikin yanayinta na kamala ta ce "Russlan ba ka san cewa an uwanka ya fa o daga sama ba ne? jikinsa na ciwo shine za ka ara zuwa ka tayar masa da hankali?" ido Russlan ya zazzaro gami da cewa "Da gaske? sannu Brother!" dogon tsaki kawai Akhiee ya doka ba tare da ya ce uffan ba, Mother ta kama hannunsa ta zaunar da shi gefe, Towel ta sa ta na tsane masa gashin kansa wanda ya sauka a gadon bayansa, fuskarta auke da lafiyayyen murmushi kamar kullum, cikin sassanyar muryarta ta ce "Me yasa za ka fa o daga sama haka? Domin wannan Yarinyar ne?" asa ya yi da ido kafin ya ce "Mother! sabida ni ne hakan ta faru, da ace ban je makaranta ba ma da Allah ne ka ai ya san abinda zai faru da ita, Tsafi ne aka turo, kuma don ni aka turo shi amma ya tafi zai fa a kanta, shine garin na janyeta na taka awon ayaba sai muka fa o, amma mutane gani su ke yi kamar wani abu na yi mata ko kuma ina sane na jawota" Mother ta jinjina kai alamar gamsuwa sannan ta ce "Amma me yasa ta suma?" "Ohh my god!" ya fa a gami da dafe goshinsa, Mother ta lura tambayar ta-ta ce ba ta yi masa ba don haka ta ce " Please tell me my son" "It's not my fault, kawai zafin tsafin ne ya ta a ta shine ta suma, na rasa gane me hakan yake nufi Uwa!" murmusawa ta yi kafin ta ce "Da sannu-sannu za ka gane, ka kula da kanka." Russlan da ke zaune ya zuba musu ido sai a lokacin ya ce "To wai ma Uwa! har akwai wanda ya isa? na yi mamaki da jin hakan gaskiya." Mother ta ce "Ba abin mamaki bane;, Risslan ka zo mu je ciki ka huta na san ka na bu atar hakan." Bai ce komai ba ya mi e ta na ri e da hannunsa su ka wuce cikin tafkeken gidansu. Husnee Tinda ta koma gida ba wanda ta saurara ko da Mommy ta tambayeta abinda ya faru da ita sai ta ce ba komai don haka Mommyn ta zuba mata ido. Toilet ta wuce ta ha a ruwan zafi me zafi sosai ta yi wanka sannan ta fito, doguwar riga mara nauyi ta saka kana ta koma kan gado ta du une, jikinta ko ina ciwo yake amma da ta yi wankan ta an ji sau Khausar ce ta shigo ta na cewa "Anti Husnee wai ba za ki ci abincin ba?" kamar za ta yi kuka ta ce "Ke dalla na oshi" Khausar ta ce "Wallahi ba ki da lafiya, dole ma ki ga likita bari Daddy ya dawo." Husnee ba ta ce komai ba don maganar ma ba son yi take ba. Sai da aka yi kiran Sallar magrib sannan ta fito ta aura alwala, Yaya Muneer ne ya dubeta a tsanake ya ce "Ya jikin naki?" da sauri ta ago ta na kallonsa a ranta ta na tunanin ''Wai ce musu aka yi ba ni da lafiya?" a zahiri kuwa cewa ta yi "Da sau i" Yaya Muneer ya ce "Ba ki da lafiyar amma ba za ki fa a ba sabida Allura ko?" da sauri ta girgiza kai alamar a'a, kafin ya yi wata maganar tuni ta gudu aki. Bayan an idar da sallar isha'i ta na zaune kusa da Mommy, duk sauran yayyenta dake Parlon su na hira da raha amma banda ita. ta yi nisa a duniyar tunani Ahmad ya yi sallama, ko zama bai yi ba ya ce "Ina Me hawaye ba kukan nan?, ya jikin?" ya yi maganar ya na dariya. uro baki ta yi gami da cewa "Ni fa lafiyata alau." Yaya Muneeb ya ce "A'a gaskiya dole akwai wani abin da ke damunki, ke da surutu kuma har a zauna hira ba ki ce komai ba?" Ahmad ya ce "Ku yaleta ar zafi ce ta isheta, ai an gaya mini abinda ya sameta." Daddy ne ya dube shi a nutse ya ce "Zauna Ahmad" zaman ya yi a kan carpet ya na ar dariya asa- asa ya na kallota gami da yi mata gwalo, ita kuwa hankalinta duk ya tashi, fargabarta aya a fa i wani abinda zai sa su gane cewa ta gama yin zurfi a cikin shishshigewa Risslan. Daddy ya ce "Nutsu ka gaya mana abinda ya faru da ita, ba ma son shiririta." Ya ce "To Daddy, maganar gaskiya ko me ta ce arya ta ke yi, daga saman makarantarsu ta fa o, ba ma fa daga afar bene ba daga can sama, in gaya muku gaskiya gwara ku kaita National Orthopaedic Hospital ta cancanci ganin likitan ashi." Ido warwaje Mommy da Khausar su ka furta "Daga sama???" Ahmad ya ce " warai kuwa ga ta nan ku tambayeta." Mommy ce ta kama hannunta gami da cewa "Ke tashi in ganki, ai wallahi da gaskiyar Ahmad gaba da Orthopaedic ma sai a kaita." Husnee ta mi e kamar za ta yi kuka ta na cewa "Ni fa ba na jin komai kawai ciwon jiki na ke ji ka an." Ba wanda ya tanka mata sai ma ido da suka zuba mata, Mommy ta ce "Taka in gani, jeki kusa da Ahmad ki dawo." ba dan ta so ba ta taka zuwa inda ya ke don dai kawai ta na son tabbatar musu alau take. Ganin ta na tafiya sak! ba alamar ciwo ko buguwa ko ingishi ya sa Ahmad cewa "Kai anya kuwa Daddy yarinyar nan Aljanu ba su shafeta ba? ka ga ar da ta fa o daga sama? tangaras abinta ko targa e babu? wallahi ni Aliyu cewa ya yi mini da ta fa o ma suma ta yi sai daga baya ta farko amma kalleta don Allah." Daddy ya numfasa kafin ya ce "Kai fa Ahmad akwai ka akwai shiririta, wane irin Aljanu kuma ana zaune alau?" Ya Muneeb ya ce "Abin dai da alamar tambaya akai, daga kan keke ma idan mutum ya fa i jiki yake ji bare ta fa o daga sama amma ta mi e garau" Ya Muneer ya ce "To ai ma abin tambayar anan shine, asali me ya gusar mata da hankali har ta fa o daga sama? ko tsokanar wata ki ka yi ta ebeki ta watso?" girgiza kai ta yi alamar a'a Mommy ta ce "Ni dai barkana, tinda alau take ai ta kwana gidan sau i, mu ga hannunki" ta fa a ta na mi a mata nata hannun, ba musu ta mi o duka hannayen nata, Mommy ta mammatsata ta ji dai ba ta yi ko gezau da sunan an ta a mata inda ke mata ciwo ba, sakinta ta yi ta na cewa "Ikon Allah, Allah ya tsareki Husna" Khausar da ta saki baki ido da hanci ta na bibbinsu da kallo sai lokacin ta ce "Gaskiya ke ar baiwa ce Aunty dama ni ce" Ahmad ya yale da dariya ya na cewa "To Bugun la'asar, ke da ina da ke muguwar tafki ce, ta fa o daga saman ki ce dama ke ce? to idan ke in ce ki ka fa o kuma ki kwararra e fa? ita in ma ila Aljanu ne su ka shafeta." Zuwa yanzu surutan nasu sun fara atawa Daddy rai, a tsawace ya ce "Kar na ara jin wani ya ce wai Aljanu gareta! ku ba ku san kiyayewar Allah ba? sau nawa ake yin ha ari har wasu su mutu amma a ciki sai ku ga wasu ma abin bai shafesu ba kamar ba sa ciki, amma don ta fa o daga sama ba ta ji ciwo ba sai ku ce Aljanu ne? ba ku san cewa Allah na kare bayinsa ba? ya kuke abu kamar ba musulmi ba?" Ahmad ya ce "Ayi ha uri Daddy mun dena." Husnee kuwa komawa ta yi ta zauna ba tare da ta ara bi takansu ba. Washegari ba wanda bai yi mamakin ganin Husnee ta dawo makaranta ba don a zatonsu ko za ta kuma zuwa sai bayan ta yi doguwar jinya, sai kuma su ka ganta katsam, su kansu malaman sun yi mamaki, su Yasayyadi Usman aya bayan aya sai tambayarta su ke yi abinda Akhiee ya yi mata, ita kuwa gaskiyarta take fa a musu cewar ba ta san abinda ya faru ba dole su ka gaji su ka yaleta. Yamma ce li is..... Tankar Ya i da Abokananta su na zaune a wani fili wanda suke kira Bakin Kwalta, anan su ka saba zaman shaye-shaye da hira. yau ma kamar kullum kowa na shan abin mayen da ya fi yi masa da i amma banda Tankar Ya i gabaki aya ta kasa yin komai hankalinta ya tafi akan tunanin Risslan. an Kurada ne ya lalla o