← Book details Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 47

Sashe 12

Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ayeesha Abdulkareem INDO *M.W.A Kafin ta ce "Ke dalla kar ki zo mana da raini mana, shi ai ba irinki bane ya na da kamun kai, ko me zai yi da ke ma ki na famar tafiya a karkace?" Zabira ta ce "Gaggauta fita daga nan kafin mu rabaki wallahi, mara kunyar banza aramar ar kwalta!" wani shu'umin murmushi Tankar Ya i ta saki kafin ta ce "Idan ba ku san ni ba shi ya san ni, kuma ba wurinku na zo ba, ku gaya min inda yake tin kafin na shiga nemansa da kaina, koda kuwa ba ya nan zan jira har lokacin da zai dawo." Zabira za ta yi magana Laita ta katse ta da cewa " yaleta, ita za ta sayowa kanta wahala barta ta jira shi, kuma yadda ta fito haka za ta koma." Zabira ta koma ta zauna cike da takaicin Tankar Ya Gwaja ne ya tanka eyar Rabi'u su ka shigo tare, Gwaja ya kalli Laita ya na cewa "Laita ga yaronki nan ya dawo daga makaranta!" Rabi'u da ke ta famar ha e rai ya ce "Ni yunwa nake ji" Wani shegen kallo Laita ta zuba masa kafin ta ce "Zo ka yanka ni ka ci, ko ni zan nema sannan in sayo maka abincin? ka bada ku i a sayo maka mana" Kamar zai yi kuka ya ce "To ai ku in nawa sun are." Harara ta zuba masa gami da cewa "Zo nan!" ya arasa ya tsugunna a gabanta, fuska a aure ta ce "Da ina ka ke samun ku in? ba ka ce ba ka sata ba?" "To ai nawa ne da su na zo." Gwaja ya ce " arya ka ke yi munafuk..." aga masa hannu ta yi kana ta ce "Je ka duba min ku in da nake ajiyewa a akin kwanansa." Bai ce komai ba ya juya ya nufi akin, Rabi'u kuwa ya yi wu i-wu i da ido duk ya tsorace. Ba da ewa Gwaja ya dawo ya sanar mata ba sa nan, ta kalli Rabi'u kamar za ta dake shi ta ce "Fito mini da ku ina ko na harra a ka!" hawaye ya goge gami da cewa "Allah i baki ha uri, wallahi idan na ji yunwa ne ki ka ce na kawo ku in abinci sai in auka a cikinsu kuma yanzu sun are." Gyara zama ta yi kafin ta ce "Ka san Allah sai ka biya ni, in ba haka ba me rabani da kai sai Allah, kuma ba me baka ku in Abinci sai dai ka nema da kanka, ai ba ka san darajar nema ba shi yasa ka ke almabazzaranci da ku i har ka ke yin sata." fashewa ya yi da kuka ya na bata ha uri ita kuwa ta ce ba ta san zance ba. sai da ya ga ba za ta tausaya masa ba ya ce "A ina ake neman ku i to?" ta ce "Yanzu ka yi magana, ka ga wa ancan ciyayin? maza ka je ka dinga fige su ka na ha a mini su wuri aya, sai ka yi cikin hannu biyar zan ba ka Naira biyar, adadin yawan da ka tara adadin ku inka, idan ba ka yi ba kuma ba ka da Abinci, sai dai ka mutu, kuma da haka za ka biya ni ku ina ko na yanke maka hannu". Zuwa yanzu ya gane ba ta da imani ko na kobo, don haka ya tashi jiki na rawa ya fara tsigar ciyayi, ya na yi ya na kuka sabida yunwa da takaici da su ka ha ar masa. Sai a lokacin Tankar Ya i ta magantu da cewa "Ke wallahi anyi mara imani, yanzu wancan an yaron ne ki ke yiwa irin wannan, nawa ne ku in naki ni in biyaki?" Kallon she e Laita ta yi mata gami da cewa "Da wace kamar?? ke kina ganin ki na da ku in da za ki iya biyana ne? ai duk danginku ba me iyawa bare wata ke." A fusace Tankar Ya i ta ce "Kar ki yi mini rashin kunya fa, wallahi na fi ki dattin walwa." maida kallonta ta yi kan Rabi'u gami da cewa "Kai zo ka kar i ku i ka yale wannan ar balaja'un" Laita ta murmusa gami da cewa "Maza zageni lokacinki ne" Rabi'u kuwa ya zo da gudunsa ya kar i ku in ya na murna, ko gama jin uminsa bai yi ba Laita ta kira shi ta wace su, bai gama tunanin abinda za ta yi ba ya ga ta yaga su gutsi-gutsi ta watsar, ai kuwa ya ara fashewa da kuka, tin kafin ta yi magana ya tashi ya ci gaba da aikinsa. Rai ace Tankar Ya i ta ce "Ni za ki yagawa ku i? amma ba komai ku ci gaba wallahi indai na Auri Rissy za ku ga wula anci da rashin mutunci duk sai na antar da ku" Dariya su ka sanya harda tafawa, daidai lokacin Salansa ya shigo ya na cewa "A gyara hanya me gayya ya shigo" Laita ta na jin haka ta fashe da kuka, ita kuma Zabira ta zuba tagumi ta yi wani kalar tausayi kamar itama za ta fashe da kukan. Tankar Ya i dai sabida mamaki kawai ta saki baki ta na kallon ikon Allah don ta zata ma Aljanu garesu. Har zai wuce ya ji ba wadda ta tanka masa ga sautin kukan Laita ya na ji don haka ya tsaya ya na zuba musu idanu, sai lokacin ya lura da Tamkar Ya i da ke tsaye hannayenta ri e da ugunta, "Me yake faruwa ne?" ya tambayesu Laita ta ara sautin kuka, Zabira ce ta murje ido sannan ta ce "Wannan Matar ce ta zo wai ita Kazarka ce, don mun ce ba ka nan shine ta zazzage mu, nima don dai ina da juriya ne da tuni na fara kukan don zagin are dangi ta yi mana" ta arasa maganar tana tatta e baki. Ransa in ya yi dubu ya aci, maida kallonsa ya yi kan Tankar Ya i da ta kasa rufe bakinta, lallai yau ta shigo inda aka fi ta makirci, tunanin da take yi kenan, ya katse ta da cewa "Abin naki ya wuce kaina ya koma kan Iyalina kenan?" da sauri ta ce ''Wallahi ko aya, ni fa ba abinda na yi musu ka tsaya ka saurare ni." "Ina yale ki ne kawai sabida ke macece, ki fita kafin na yi miki illar da ba za ki ara taka afarki ba. Cike da acin rai ta ce "Na ji, zan fita amma sai lokacin da na ga dama tinda ba kai ka kawo ni ba, nifa wallahi duk abinda za ka yi mini ina sonka ba zan fasa ba sai dai in ba na numfashi, don ma ina son naka shine ka ke wani jiwa mutane kai, duk abinda ka ke ta ama da shi nima ina da shi, kuma ka sa a ranka ba za ka ta a Aurar wata mace bayan ni ba, duk wadda ta so ka ma sai na kasheta kuma na kashe banza. "Ki kasheta mana idan za ki iya, kuma idan ba ki kasheta ba ni zan kashe ki, fice mini da gani shashasha" ya yi maganar cikin acin rai da takaici. Dogon tsaki ta zabga kafin ta ce "Kar ka yi zaton yale ka na yi, zan dawo, ku kuma wa annan munafukan ku kuka da randa za ku shigo hannuna." ta na kaiwa nan ta fice cikin sauri kamar me shirin tashi sama. Risslan kuwa bai bi ta kansu ba ya wuce angarensa cike da takaicinsu da su da suka tsaya yi mata kuka da ita tsagerar." Yana barin wurin Laita ta goge hawayen ta na cewa ''Ita aramar ar bariki ce, ni sabida tsabar makircina aka ra a min Laita, kuma wallahi in ba ta yi a sannu ba sai mun sa ya kasheta." Zabira ta ce "Wa yake ta ta-ta ma har me akai aka yi ta? ai bigi sai bigi." Gwaja ya ce "Na tsorata da ku mutanen nan" Laita ta murmusa gami da cewa ''Ka an ma ka gani" hira su ka ci gaba da yi akan ta yadda za su koya wa Tankar Ya i hankali, kowa na bada ta shi shawarar. Hajiya Laure Kamar yadda ta fa a tin wuri ta shirya ta nufi gidan Hajiya Saudah daga nan su ka rankaya zuwa wajen boka. ar bukka ce wadda tin daga waje ma za ka gane ba alkairi ake shukawa a cikinta ba duba da yadda aka yi mata ado da ashushuwa da kawuna warangwal- warangwal na dabbobi iri-iri. Hajiya Laure ce ta turje ta kasa shiga, a tsorace ta ce "Hajiya Sauda wai ki na ganin abinda nake gani kuwa?? ni fa gaskiya ba kowane boka na yarda da shi ba, ki zo mu koma don ba na son wanda garin na cutar da wani ni sai ya cutar da ni" Hajiya Saudah ta ce "Ai kin ji inda ki ke bada mata wallahi, to bukkar boka barore ba a shiga a fito ba nasara kuma ki yi tambaya ga wa anda su ka san shi ki ji, komai wuyar aiki inda kin kawo shi wajen boka barore kin gama." Hajiya Laure za ta yi magana karsanar muryarsa mara da in ji ta kara e kunnuwansu, "Shai anun Aljanu sun yi marhabin da zuwanku!!, ku araso ciki!!!!!!, ba a zuwa tsibirinmu a koma haka nan dole sai an gana da mu in ba haka ba a hau-kace!! hhhhh" Hajiya Saudah ta ce ''To kin ji ka an daga cikin sharu ansa gwara ma ki nutsu." jan hannunta ta yi kiiii su ka danna kai ciki. Duhu gami da wata irin guguwa me arfi su ka gauraye bukkar, kwata-kwata ba a ganin komai sai arar guguwar wadda iyakacin cikin bukkar ta kara e, Hajiya Sauda da Hajiya Laure su ka ha e kai su ka ame juna. Guguwar ta kai tsawon minti guda 1 har da an sakanni ta na juyawa sannan ta tsaya cak, wani jan haske ya tsago daga jikin bango sai ga boka Barore tsubul a zaune, sai kuma haske ya dawo daidai. a tare su ka numfasa musamman Hajiya
Chapter 12 · 0% Book details