← Book details Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 47

Sashe 29

Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ayeesha Abdulkareem INDO *M.W.A "Kin i yin Bacci ko??" muryarsa ce ta doki dodon kunnenta, ta zazzaro ido a an razane kafin ta sauke nannauyar ajiyar Zuciya ba tare da ta yi magana ba, Jin ta yi shiru ya sa shi arawa da cewa "Me yasa to?" kamar za ta fashe da kuka ta fara magana cikin muryar shagwa a, "Tsoro na ke ji Akhiee!!" an jim ya yi kafin ya ce "Haka ne? ko in zo mu tafi gidanmu?" ara firfito da zara-zaran idanunta ta yi "Tsakar dare ne fa yanzu!! kai ka na ina ba ka tafi gida ba??!" ta yi maganar cikin firgici. Cikin wata kasalalliyar murya ya ce "Asma'u ni dare ba ya hanani yawo hasalima ban fiye bacci da daddare ba da rana nake yi, ina kusa da ke in ki na so na zo mu tafi zan zo idan kuma ba kya so to ki yi baccinki cikin kwanciyar hankali." Ajiyar Zuciya ta sauke gami da sassauta murya a sanyaye ta ce "Ka na kusa da ni Akhiee to ta ya kenan?" auke wayar ya yi daga kan kunnensa kafin ya furzar da wata zazzafar iska, ya so ya yi aram- atama kuwa, kiran sunansa da ta yi ne ya dawo da shi hayyacinsa, cikin nutsuwa ya ce "Ina nufin ki sa hakan a ranki kawai, Sai da safe yanzu zan shiga gida." da sauri ta ce "Akhiee!!" cikin wata irin shagwa a ta yi maganar kamar wata ar shekara biyu na kiran Ummanta, rasss zuciyarsa ta buga ya lumshe idanunsa da su ka fara canja launi kafin ya mayar mata da martani ta hanyar kiran nata sunan "Asma'uhh!!" murmushi ta saki kafin ta ce "Da gaske ne ka na kusa da ni? kuma ka na tare da ni Akhiee? " "Kin san ba zan fa a miki arya ba don hankalinki ya kwanta, ki yi baccinki ina tare da ke, kuma za ki yi mafarkina." gya a kai ta yi ta na murmushi cike da farin ciki da shaukin sonsa ta ce "Allah i tsare min kai Akhiee." kai kawai ya gya a ba tare da ya yi magana ba ya kashe wayar. Sumar kansa ya cafka gami da sauke nannauyar ajiyar Zuciya me tafe da wata Zazzafar iska. Ji ya yi an dafa kafa arsa ya yi saurin cewa "Russlan!!" Russlan ya zauna a gefensa kan katafaren gado irin na sarakuna da yake zaune a gefensa. Cikin sanyin jiki Russlan ya ce "Ko shakka ba na yi ka na son matarka Risslan, ya zama dole ka dinga iya bakinka kar ka fa a mata abinda dole ne sai ka kasheta da hannunka." jinjina kai ya yi kafin ya yi magana "Ban san me yasa Asma'u take da tasiri a kaina ba, na kasa samun nutsuwa sai tunaninta na ke yi, ji nake tamkar na je na kwana a kusa da ita domin na bata dukkan kulawata." Russlan ya ce "Na gane hakan ai duba da yadda ka ke zagewa ka na gaya mata gami da nuna mata iyakar abinda ke oye a Zuciyarka wanda ba kowane me wannan Darajar ba, amma fa ina ji maka tsoron Uban Dawa kar ya hukuntaka akan aurenta ba tare da sanin iyayenta ba." Shiru ya yi na an lokaci kafin ya ce "Asma'u! itace maha in rayuwata ko da so ko babu da ita zan rayu, ko da Father zai yi fushi zan jure duk hukuncin da zai yi mini, abu aya kawai na yarda da shi kuma na sa a Zuciyata, ko da ta sanadin Asma'u za a yi mini izayar da ban ta a fuskanta ba duk tsawon rayuwata ba zan Saketa ba ina tare da ita kamar yadda na yi mata al awari har sai in itace ta so rabuwa da ni wannan zan iya amincewa; Bayan haka kuma sama da asa, Duniyar Mutane da ta Aljanu har ma da sauran Duniyoyi babu wanda ya isa ya sa ni sakinta duk azabarsa, Allah ne ya halicceta kuma ya jefota cikin rayuwata kuma ina komai ne da ikonsa shine ka ai zai rabani da Asma'u ta kowace hanya, ko a raye ko muce Russlan kai ma ka ri e hakan." Zuwa yanzu Russlan tsananin tausayun an uwan nasa ya gama kama shi, ya san a zaman tare dole wataran za ta gane gaskiyar waye shi, kuma hukuncin wanda ya yi hakan kisa ne, bayan haka akwai alubale da yawa a gabansu wanda shi Risslan ba ya hangosu sabida idanunsa sun rufe, "Risslan na yarda da kai kuma na san za ka aikata amma ka sani akwai sauran rina a kaba." "Na san da hakan Russlan, ka koma gida kawai nima zan wuce gidanmu Gadon nan ka sa Dogarai su kwashe shi kar safiya ta yi Bil'adam su dinga karo da shi." Russlan ya ce "Okay sai ka fito goben, Mu ha u a Daji in an isa." a hankali Risslan ya ce "Ka san fa ni ba kamar kai ba ne, musamman ina cikin wannan yanayin da akwai mutane da yawa wa anda su ke bu atar kulawata." Russlan ya ce "Okay shi kenan see you later." Risslan bai ara magana ba ya ace att! sai gashi a kusa da Dokinsa. Prince na ganinsa ya fara haniniya ya na aga afafu sama ya na direwa, Risslan ya shafa shi cike da aunarsa hakan ya sa ya sunkuyar da kansa asa kamar ba shi ya gama dara ba yanzu, wata kyakkyawar sufa Akhiee ya yi ya dire akan Prince tare da Komawa asalin Suffarsa ta an'adam wanda kowa zai iya ganinsa sa anin Da da ya koma Suffar mutanen oye. Hanyar komawa Hotoro yankinsu ya auka ya na tafiya cikin kwanciyar hankali ba tare da wata fargaba ba. Cijewa Prince ya yi gami da angale afafunsa ya na wata irin haniniya hakan ya tabbatarwa Akhiee wani abin ya gani. Bai gama nazarta yanayin ba ya ga Alburushi ya nufo kansa gadan-gadan sunkuyawa ya yi ya wuce sannan ya ago, kafin ka ifta ido ka bu e wasu murtuka-murtukan mazaje sun bayyano ta kowace kusurwa ta filin, sanye suke cikin ba en kaya kowanne fuskarsa a rufe, su na auke da wasu lafiyayyun bindigu wanda suka rufe bakunansu ta yadda ba za su yi ara sosai Ba. Harbi suka fara ba shi ta ko'ina ba autawa idanu a lullu e neman makasarsa su ke yi. Abin da ya yi bala'in basu mamaki gami da dugunzuma hankulansu, kasancewar wararrun maharba ne ba sa sa a saiti bayan Alburushin farko ba wanda su ka harba masa ya fa i duk sun same shi sai dai da zarar Alburushin ya sauka a jikinsa zai gangare ya fa asa ba tare da ya ratsa shi ba, duk da suna ganin hakan kuma sun razana amma ba su fasa ba don kuwa ganu suke yi kamar za su iya cimma nasara in suka arta. Wani wawan juyi ya yi gami da bu a hannayensa ya yi wani wurwuro kamar fanka sannan ya diro asa hannunsa ri e da manyan bindigu guda biyu. Turus su ka tsaya kallonsa ido a warwaje, sun kai ma urar tsoro da firgici ganin bindigu sun bayyana a hannunsa bayan ba shi da su ba shi da dalilinsu. Cikin rashin imani da tausayi Na Akhiee ya fara sakar musu harbi a matu ar fusace, ganin haka ya sa su ka ci gaba da harbinsa su ka fara artabu tsakaninsu, sai dai shi harbi aya yake yi musu su baje don dai su na da yawa. ata lokaci duk ya arar da su saura mutum aya wanda Alburushi ba ya shigarsa don kuwa shi ma babban shege ne. Akhiee ya yi wani waran taku gami da watsar da bindigun a gefe dandanan su ka ace att!! sai kuma wata lafiyayyar farar wu a ta bayyana a hannunsa, duk da dare ne hakan bau hana yallinta da haskenta fitowa ba, kan Maharbin ya nufa gadan-gadan hakan ya sa ya arta da gudu domin ceton ransa, jefa masa wu ar ya yi cikin sa'a kuwa ta ratsa ashin bayansa, ya saki ihu gami da zamewa ya kife a rubda ciki, Akhiee ya arasa gabansa ya dur usa kafin ya ce "Duk wanda ya ga wannan Sirrin nawa mutuwa ce makomarsa ba za ka iya tsere mini ba, amma kafin ka mutu ina son sanin wanda ya aiko ku." cikin arfih hali Mutumin ya kama dariya ya na cewa "Wani Jarumi ne, kuma ya riga ya sa ka a tarko ta kowace fuska, ya yi mummunan shiri na kawo arshen hatsabibancinka, kuma ina me tabbatar maka ruhina ba zai tafi a banza sai ya aukar mini fansa, Gobe za ka samu gawar anka mun ci moriyarsu don haka za mu dawo maka da su, ka shiga matsala Sar a, duk hatsabibancinka sai wannan Shu'umin ya ga bayanka shi ba kanwar lasa bane zazzafa ne, kuma jama'arsa daga kowane State na Nigeria har ma da asashen etare sun shigo Nigeria sun yi maka awanya, in ka isa ka tsira hhh!!!". arasa maganar ya na ara alewa da dariyar mugunta a wahalce. A fusace Akhiee ya zare wu ar da ke ma ale a bayan Mutumin ya suka masa ita a wuya, ko shurawa bai ara yi ba tuni ya mutu idanunsa a bubbu Akhiee ya mi e jikinsa na wata irin tsuma sabida acin rai, tuni wani irin duhu ya mamaye idanunsa kansa ya fara wata irin yamutsawa. Bai bi ta kan Dogarawan Aljanun da suka kewashi ba ya haye kan Prince ya ci gaba da tafiya. Aljanun su ka koma kan mutumin da ya kashe daga arshe shi ma su ka auke gawar ta shi sauran kuwa tuni sun kwashe su sun kai su bakin wani Daji sun zubar. Ba su gushe daga wurin ba sai da su ka gyara shi tsaf ba alamun jini ba alamar Alburushi ba ma me cewa wani abu ya faru a wurin. ya na isa bakin get in gidan ya dire daga kan Prince ya dafa ofar nan-take ta bu e ba tare da hayaniya ba, ya shiga gidan tare da Prince sannan ya ara dafa ofar ya rufe, sakatu harda Pad lock in da ake sawa get in duk su ka koma su ka
Chapter 29 · 0% Book details