← Book details Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 47

Sashe 32

Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

idanunsa, bai katse wayar ba sai da ya tabbatar mata gobe za su shu igar da ara Kotu dolen doliya sai an raba Auren, a cewarsa ba zai kai arsa inda za a dinga ciyar da ita da Haram ba. Ko da Muddassir ya jewa Malam Kabiru da tambayar sai da ya ha a masa da Shaidu wa anda a gabansu aka aura Auren sannan su ka ha u su ka yi masa bayani, nan fa ya ara burkicewa ya rasa inda zai tsoma rayuwarsa, shi ba abin ya dinga kurma ihu ba ko ya samu sau Ma'u na kicin tare da Iya da Talatu su na girke-girke Yazeed ya shigo kamar an jefo shi. da sauri Iya ta ce "Lafiya kuwa Yalla ai?! an sosa eya kafin ya ce "Don Allah ku an ba ni wuri mana." Iya ta koma e baki Zuciyarta cike da sa e-sa e, kafin Iya ta mi e Talatu da Ma'u sun mi e, Iya ta ce "Ke ar nan kamani in mi e mana." Ma'u ta temaka mata ta tashi sannan su ka nufi hanyar fita, jikin Ma'u na rawa sai gaggawa take yi don ta yi ta fita kar ya ce mata wani abun. Caraf ta ji ya dam o hannunta, a firgice ta juyo ta na zazzaro masa ido, ya marairaice kamar zai yi mata kuka "To Ma'u kika tafi ki ka bar ni da wa zan yi magana? dominki fa na zo." da kyar ta fizge hannunta daga ri on da ya yi mata cike da ba in ciki ta ce "Ni ban ga abinda za ka yi mini ba Yalla ai, indai Abinci ka ke so ka nemi Iya mana sai dai in zalumci ne ya kawoka". wani irin sakin baki ya yi galala ya na kallonta kafin ya ce "na yi miki kama da Azzalumai Ma'u?? to in ma haka ki ka gani ni ba haka ce a Zuciyata ba, ki je ki shirya ki raka ni." "Ni ba zan je ba!!" ta fa a a masife kamar za ta hau kansa da dukan. wani lallausan murmushi ya saki Gami da cewa "Dama kin iya fa a? sai naga kin yi kyau a cikinsa; ke sai fa kin je ko kuma in auke ki da kaina in zuba ki a Mota, wata cikal-kal da ke har wani hargowa ki ke yiwa mutane? to ki gaggauta shiryawa in ba haka ba zan aukeki ko babu gyale." Ba ta ce masa komai ba ta fice daga Kicin in ta na kuka ta nufi akinsu. Iya da Talatu na zaune sun ci gaba da hirar da su ke yi ta shigo ta na kuka, Iya ta ri e ha a gami da cewa "Oo! Duniya, me ya yi miki ki ke kuka haka?? ni fa ina ji miki tsoron yaron nan, me ki ka ci masa me yake ta zawarcenki??" Cikin shashshekar kuka ta ce "Ba abinda na yi masa haka kawai yake mini haka, wai yanzu ma in shirya in raka shi, ni dai ba zan je ba ko me zai yi mini." Talatu ta yi karaf ta shiga zancen da cewa ''Ke wallahi ki bi shi ki ga inda zai kai ki, ai dai ba zai sayar da ke ba ko." cikin takaici iya ta zabga tsaki gami da kaiwa Talati duka ta na cewa "Ja'irar gora, to in bai sayar da ita ba ai zai rabata da darajarta, ki na gani in uwar ba ta nan yadda yake yo safarar Mata ya na kawowa gidan." Talatu ta ce "Eh kuma fa haka ne..." Ma'u kuwa ara fashewa ta yi da kuka jikinta sai tsuma ya ke yi gabaki aya ta ara firgicewa. Sun auki lokaci a nan Talatu da Iya su na maida yadda aka yi Ma'u kuwa ta na razga kuka....... Kamar daga sama su ka jiyo muryarsa ya na walla mata kira, ta ara sautin kukanta cike da tsoro da firgici. Iya ta rausayar da kai kamar marigayin zakara kafin ta ce "To Allah i tsare sai ki tashi ki je, amma ki dinga Addu'a." Talatu ta na jin haka ta tashi ta akko ko en Hijab inta ta fara aba mata, ta na turewa ta na komai amma sai da ta sa mata shi sannan ta akko mata takalmi ta ajiye mata ta na cewa "Gwara ki bi shi ta maslaha kar ki yi masa abunda zai cuceki a banza, sai ki dinga Addu'ar." Sai da kyar da si in goshi suka lalla ata ta fito wujiga-wujiga da ita sai murza kuka take yi kamar an yi mata wahayinsa. Shi dai ba abinda ya ke iya yi banda kallonta, har cikin ransa ba ya jin da in kukanta amma ita ta kasa ganewa. A wani rafkeken Super Market ya yi Parking, ido ya ara zuba mata kamar zai cinyeta, kanta ya na asa har lokacin ba ta dena kuka ba. Cikin wata karyayyar murya ya ce "Ma'u me yasa ba za ki saki jiki da ni ba? ba zan iya cutar da ke ba Ma'u hasalima burina a koda yaushe in ga ki na farin ciki, kuma ina so farin cikinki ya ore har Abada, ki temaka ki gaya min damuwarki domin ina so in zamo miki Bango." Ya sosa mata inda ke mata ayi, ai kuwa ta ara fashewa da wani sabon kukan filll, cikin shashsheka ta ce ''Ba zan iya ba!!" "Yau na ji ikon Allah, kuka na ara sa ki? to Allah i ba ki ha uri na dena, ki kwantar da hankalinki, Nasan ki na tunanin wasu halaye nawa ke ba ki yi kama da irin wa annan matan ba, ke mace ce wadda ya kamata a yi kishinta, ki zo mu je to, sayayyar kaya zan yi miki sai ki za i abinda ki ke so." "Ni ba zan je ba" ta ba shi amsa cikin kuka. Bai matsa mata ba ya wuce shi ka ai, bayan wani lokaci ya dawo auke da tir a-tir an ledoji guda biyu wanda aka sha esu da kaya, bayan ya zuba a Motar ya shiga mazauninsa sannan ya ja ta. Har su ka dawo gida Ya na zuba mata surutu ita kuwa ba ta da aiki sai kuka, muryar ta shi ma duk ta gaji da ji; ji take kamar ta kashe shi ta huta. Talatu jiki na rawa ta fara zaro kayan ta na dubawa sai murna ta ke yi kamar ita aka bawa. Dogayen Ruguna ne wanda yawancinsu Abaya ce, sai riga har asa me wando, sai kayan ciki su pant, da su turaruka, da Alewoyi da chocolate kala-kala . Iya da Talatu sai yabawa su ke yi yayin da Ma'u ta ke jin Zuciyarta na wata irin una, lokaci guda zazza i ya rufeta bayan ta gama masifa da cewa ba za ta yi amfani da komai a ciki ba ta haye yamutsatstsiyar shimfi arsu ta kwanta, ba abin da ke aga mata hankali idan ta tuna sama da surutan da ya dinga yi mata a hanya kamar mahaukacin da ya wato da ga gidan Masu rangwamen hankali. Sai da su ka gama gani sannan su ka mayar su ka ajiye mata, ita kuwa ko wajenda kayan suke ba ta ara kalla ba. Washe-gari Ranar litinin kenan, Ranar jirginsu Abhi da Jaafar ya aga zuwa Saudi Arabia, hakan ya mugun yiwa Akhiee da i ya san duk rigimar da za a yi za ta are kafin Abhi ya dawo. Gidan Su Husnee Komai ya yamutae lokaci guda ta zamo tamkar Mujiya a cikinsu kowa ya i saurararta hatta Khausar in ta kulata sai Mommy ta doka mata tsawa, Fa a kuwa ba irin wanda ba ta sha ba Muneeb har da kai duka. Cikin kwana aya ta wani zuge ta zube ta yi zuru-zuru ta dawo tamkar tsumungiya, ga wani ciwon kai da ya sakota gaba ko abinci ta kasa ci, Ta rasa inda za ta sa kanta ta ji da Wata Zuciyar ce ta bata shawarar kiransa ta sanar masa abinda ke faruwa don haka ta akko wayar ta lalubo lamba ta tura kira. Ya na tsaye a kan wani tsauni hannayensa har e a bayansa, sai arewa ko'ina kallo ya ke yi Zuciyarsa cike ma il da tunane-tunane, jin motsin wayar ta shi ya dawo da shi hayyacinsa ya auka ba tare da ya ce komai ba. Cikin Dasashshiyar muryarta ta ce "Akhiee!!" "Asma'u ki na lafiya? waye ya ta a ki?" goge walla ta yi kafin ta ce "Ba wanda ya ta a ni kawai ina cikin tashin hankali ne, iyayena da an uwana duk fushi su ke yi da ni, na fahimtar da su na basu ha uri amma duk hakan bai yi tasiri ba, kuma sun ce sai sun rabamu." aramar ajiyar Zuciya ya sauke kafin ya ce "Asma'u Calm dow........" kafin ya arasa fa en abinda ke Zuciyarsa ya ji anyi masa wata muguwar runguma ta baya wadda ta sa Numfashin da Zuciyarsa su ka dena aiki na wucin gadi, ya rintse idanunsa da arfi gami da cije gefen le ensa. Ya na jin Husnee na kiran sunansa gami da tambayar lafiyarsa amma ba zai iya ce mata uffan ba a wannan yanayin. a hankali sautin kukanta ya fara kara e kunnuwansa hakan ya sa tsigar jikinsa su ka hau tashi. katse wayar ya yi gami da sakinta ta fa asa, cikin wata irin rikitacciyar murya ya ce "Raziahh!!!!!" Cikin shashshekar kuka ta ce "Kai fa Mijina ne Risslan me ya sa za ka ha a ni kishi da wata? ka san kai ka ai nake so kuma ina kishinka shine za ka je ka auri wata? me yasa ni ba za ka so ni ba?" Cikin wata irin murya me matu ar gusar da hankalin duk wanda ya ji ta take maganar, a sannu ya zagayo da ita gabansa su na fuskantar juna ya jefa idanunsa wanda su ka canja launi cikin nata, kamar wanda aka tilastawa yin magana ya ce "Amma duk da ke matata ce wajibi ne na nemawa kaina Abokiyar rayuwa, kin sani dai ba jinsinmu aya ba, babu orarren aure tsakanin Mutum da Aljan, ko ba ma haka ba Asma'u ta cancanci hakan, ki yi ha uri" Sake ame
Chapter 32 · 0% Book details