← Book details Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 47

Sashe 28

Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

ce ma zan kaita Islamic Center ko Allah zai sa a samu sau Muddassir ya bi Husnee da kallo, shi dai a rayuwarsa Allah ya iga masa so da aunar anwar ta shi fiye duk sauran annensa, tausayinta ya gama kama shi, cikin sanyin jiki ya ce "Sannu kin ji anwata?, meke miki ciwo yanzu." "Ba komai" ta fa a ta na turo baki gaba. Ya ce "Kin tabbata?, to idan ki na bu atar wani abin sai ki gaya mini kin ji? ko mu je ki sha Ice Cream?" rasss ta ji gabanta ya fa i, "Ba ka san cewa ni yanzu matar Aure ba ce Yaya" abinda ta fa a a zuciyar kenan a sarari kuwa ta yi saurin girgiza masa kai. Ya ce "Shi kenan yanzu ki samu ki ci abinci ki huta in anjika zan baki labarin Kaduna, kin ce ma za ki bini ko?" girgiza kai ta yi alamar "a'a" gami da cewa "Na fasa" ya yi dariya a ransa ya ce "Nima ba za ni da ke ba" a sarari kuwa ya ce "To shi kenan." Tashi ta yi ta koma akinsu ba ta nemi abincin ba ta baje anan bacci me cike da mafarkai masu da i da marasa da i ya yi tafiyar ruwa da ita. Hajiya Laure na zaune ta na waya ita da Hajiya Saudah, orafi take yi akan Boka ya i kiransu har yanzu, Hajiya Saudah ta ce "Ke fa kin fiye gaggawa awata, ki jira mana ai komai ya na da lokacinsa indai Boka Barore ne za ki sha mamaki, ai ja da baya ga rago ba tsoro bane shirin fa a ne." Hajiya Laure ta sauke wani gwaurin nishi gami da murmushi, cikin jin da i ta ce "Allah i nuna mini wannan ranar awata, na ha ura ai ni da na ji shiru har na yanke shawarar za mu canja wuri." Hajiya Saudah ta ce "Ina!! ai ba wannan maganar, ke wai ba ki ga yadda nake ba a gidana? Boka Barore fa ba wasa ba ne in gaya miki gaskiya." Hajiya Laure za ta yi magana ta ankara da Yazeed akanta, fasa maganar ta yi daga arshe ma sai ta katse wayar, ta bishi da kallon rashin gaskiya ta wani ci mur, a masife ta ce "Kai kuma mara Zuciya alau kake kallona? mara kishin nasa?" Zama ya yi kafin ya ce "Ni indai irin kishin nan naki na bin bokaye ne ba ni da shi, In da an daba ki ka ha a ma da tuni sun yi miki abinda kike so amma sai wani arar min da dukiya ki ke yi akan bin bokaye, ai an Daba da an Daba ake ha a shi." Ta yi tsaki kafin ta ce "Kai dallah rufe mini baki shashasha, kai ai soko ne na asali, yaron da ya gagari hukuma shine ka ke tunanin wasu an daba za su iya da shi? shima fa an daban ne kuma ya na da an daban, ni na fi son abinda zan yi masa illa lokaci guda." "Allah ya bada sa'a" ya fa a ya na ta e baki. "Amin" ta amsa a gadarance gami da mi ewa ta bashi wuri, a cewarta ya katse mata magana. Kashingi a ya yi a kan kujera ya na lumshe ido, sanyin AC na ratsa shi, Kwatsam! tunanin Ma'u ya fa o masa, musamman yanayinta a da ta na da fara'a ga ladabi da biyayya ba ruwanta da shiga shirgin da ba nata ba "To wai meye ya sameta da ta dena walwala?" tambayar da ya yi wa zuciyarsa kenan sai dai ba shi da amsarta, ya da e ya na tunaninta kafin ya yanke hukuncin zuwa ya tambayeta ko za ta fa a masa damuwarta. ewa ya yi ya fice daga sashin Mommy ya nufi an sashin da aka ware domin an aiki. Da Iya ya fara kaci uss ta yi saurin bu a masa hanya gami da gaishe shi, bai amsa ba ya ce "Ni fa ba na so ki dinga gaishe ni tsofai-tsofau da ke" Ta ce "To annan ai ni baiwarku ce, Hajiya ta yi mana umarnin mu dinga gaishe da kowa." an tsaki ya yi kafin ya ce ''Ni ba na so, yanzu dai ina wannan ba ar yarinyar Ma'u?" Iya ta ce ''Aff! Ta na kicin ita da Talatu bari in kira maka ita." Da sauri ya ce "No ba bu atar hakan zan je can in sameta." Iya ta amsa da "To" a ranta ta na mamakin neman nata da yake yi. Ta na cikin yankan Albasa kamar ance juyo ta na kallon hanyar shigowa idanunta su ka yi katari da shi, Gabanta ya yanke ya fa i har asa, da sauri ta sunkuyar da kanta ta na jin wata irin tsanarsa da shi da mahaifiyarsa, shi kuwa kallonta kawai yake yi kamar tsohon maye. Sai da Talatu ta gaishe shi sannan ya farga ashe ba su ka ai ne a wurin ba. e fuska ya yi cike da manyance da nuna isa ya ce "Maza ki bar nan" Talatu ta ce "To" jiki na tsuma ta ajiye abinda take yi ta ra a ta kusa da shi ta wuce. Ma'u kuwa jin abinda ya cewa Talatu ya ara firgita ta jikinta ya au karkarwa, tunanin abinda Mommynsa ta yi mata ne ya fara dawo mata, musamman irin tashin hankaki da azabar da ta fuskanta a wajen Boka. Ta lula duniyar tunani hakan ya sa ba ta san ya zo kusa da ita ba sai jin muryarsa ta yi har cikin walwarta tamkar an kau a mata ba arfe a ka, zaburar da ta yi ta sa wu ar hannunta ta kufce ta shigi an yatsanta, da sauri ta watsar gami da dam e yatsan ta saki ara. Zazzaro idanunsa ya yi a kanta yana sa cewa "Lafiya??" ganin ta ri an yatsa ya sa shi saurin ri o hannun nata ya na cewa "Mu gani?" arin fizgewa ta fara yi ta na yi masa magiya akan ya saketa. kamar zai fashe da kuka ya ce "Sannu! Ki dinga bi a hankali, kin ga kin yanke kanki ko tunanin me kike yi oho." ya na sakar mata hannun ta yi sauri matsawa gefe ta na fashewa da kuka. Cike da takaicin kukan nata ya ce "Ai ka ji!!!! dama na zo tambayarki akan matsalarki ne amma yanzu kin ara iro wata matsalar." Cikin kuka ta ce "Ba abinda yake damuna don Allah ka dena nemana" "Dole in nemeki mana tinda kin barni cikin tunaninki? ki fa a mini damuwarki ki ka sani ko zan iya yi miki maganinta?" "Ba abinda yake damuna fa!' ta yi maganar ta na shashshekar kuka, an tsaki ya yi kafin ya ce "Ke na ga abin kukan ma ba ya yi miki ka an, ranar da ba kya kukan sai ki gaya mini abinda aka yi miki" ya fa a tare da juyawa ya nufi hanyar fita Zuciyarsa sam ba da Husnee misalin 02:40 juyi kawai take yi akan katifa yayin da bacci ya auracewa idanunta, ba abinda take tunani sai Akhiee da kuma abinda zai iya faruwa idan iyayenta su ka san gaskiya, ta yi nisa a tunanin ta ji motsin wayar da ya bata wadda ta zo ta turata a ashin filonta don gani take idan ta ajiye a wani wurin kamar za a iya dubawa a ganta. Da sauri ta tashi ta zauna ta na dube-dube, babu alamar kowa a kusa Khausar ma sai baccinta take lakadan, zaro wayar ta yi daidai lokacin da wani sabon kiran ya kuma shigowa, Lamba ce sabuwa ma'ana ba save, gabanta ya yanke ya fa i dandanan jikinta ya au karkarwa ta shiga firgici da razani gami da kokonto akan me kiran nata da tsohon daren nan, shawarwari take yi akan ta auka ko a'a wata zuciyar ta na garga inta wata kuma na tunzurata akan ta auka in, zuciyarta na dakan sha-lugude ta ta a kore gami da ora wayar akan kunnenta.............. SHARE FISABILILLAH Na Ku i ne.... Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba. VIP 500 Posting Kullum. domin arin bayani 09079885632 INDO* [8/26, 4:38 PM] INDO: https://chat.whatsapp.com/FuB2OR4qBx189IdAM0hXbG SAHUN KEKE Ep 18
Chapter 28 · 0% Book details