Sashe 43
Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
wasu kuma suna fa en iya abinda suke tunani, wasu kuma dai suna tsakatsaki su basu ce a raba ba ba su ce a bari ba, bayan ya gama saurarensu tsaf sannan ya yi gyaran murya ya fara da cewa "To duk na saurari kokenku, amma ni ba ni da ancin Sakar masa mata ko kuma na tilasta shi akan sakinta, amma zan yi magana da shi, don haka kowa ya tashi ya tafi uzurinsa, masu zuwa makaranta maza su shirya masu fita kasuwa su ma su shirya." Kallon kallo suka shiga yiwa juna cike da ba in cikin furucin Abee sun san tinda abin ya zama haka, ko ana ha maza ha mata ba ta yadda za a yi ha arsu ta cimma ruwa, don haka wasu suka fara sa ewa su na fita cike da takaici. Su Innajo da su Inna Huwaila kuwa suna fita suka dasa zancen su da sirikansu, irin Su , Ummu Nusaiba, Matar Babban Yaya, Yaya Lantana, Matar Yasayyadi Usman, Yaya Asiya, Matar Yaya Habibu, Yaya Fiddausi, Matar Yaya Aminu, Umman Azima, Matar Yasayyadi Jameel. Matar Sheikh Auwal wadda ake kira Yaya ita ce ba ta fito ba ita in ma Sheikh Auwal ne ya hanata banda haka da ita za ayi. Hasan na shirin fita ya na an gungunai Abee ya kira sunansa don haka ya tsaya, Abee ya ce "A zo min da Magajin Malam" wato Sheikh Auwal kenan, sunan nan da Abee ke gaya masa ma ba in cikin hakan suke ji, don gani suke yi tamkar ya fi sonsu. Ko to bai ce ba ya zunguri uban kai kamar damin gumama ya ci gaba fa tafiya. cikin ansu da ke ta sha'anoninsu ya aika aya akin Sheikh Auwal ya kira shi, bai ara bi ta kai ba ya fice daga gidan baki aya. Abee ya na dariya irin ta yaro man kaza ya ce "Magajin Malam yanzu aka gama kawo min arar an uwanka akan Aurensa, sai dai ban ji ta bakinka ba." Sheikh Auwal ya rissina a ladabce ya ce "Abee kuskuren da ya aikata shi ne Aurenta ba a kan a'ida ba, bai kyautu ya je ya yi gaban kansa ba, mu ba mu sani ba iyayenta ba su sani ba, sannan duk ba mu amince ba, sannan ya gardame akan shi ba zai rabu da ita ba duk da cewar iyayenta suna son hakan." an tsagaitawa ya yi kafin ya ci gaba da cewa "Abee! in da Akhiee ya na jin magana kuma ya na aukar shawara, ba wanda zai ce dole sai an raba Aurensa, su kansu iyayenta da ya na yin abinda ya kamata na san ba za su i ba shi arsu ba, amma yanzu ka ga abinda ya yi kowa bai ji da i ba, raina aci yake yi idan na ji irin maganganun da ake fa e akanmu, amma ina ganin indai har ba zai dinga cutar da ita ba kawai kar a ce za a rabasu don hakan ma wani aikin ne babba, kuma ta riga ta faru sai ha uri, ko an rabasu dai abin ya riga ya shiga kundin tarihi ba wanda zai manta." Abee ya yi murmushin manyance kafin ya ce "Wannan gaskiya ne, ya yi kuskure amma ana bu atar yafe masa; Wai ni ko akwai abinda kuke oye min dangane da shi ne Magajin Malam?, a gidan nan kowa ba ya laifi sai shi ka ai? ba a fa en aibun kowa sai na shi, anya kuwa ba wani abin kuke oye mini ba?, ko kuma don shi Maraya ne yasa ku ke yi masa hakan?" Hawayen da suka cika idanun Sheikh Auwal suka samu damar zubuwo, goge su ya yi cikin sauri kafin ya ce "Abee nima fa maraya ne, da ni da shi da Zahra Mahaifiyarmu aya kuma ba ta raye a Duniya, kawai dai shi ya bambanta da kowa ne, ya fi son ya yi abinda ra'ayin kansa ne ba ya jin bari, kuma irinsu su na da wuyar sha'ani". Abee ya ce "Allah ya jaddada Rahma garesu ita da sauran anta da mu ka rasa, amma akwai abinda ba kowane ya san shi ba a tare da Dattijo, kuma ba wanda zai iya fahimta har sai wanda Allah ya bawa iko; a gaya masa ina bu atar ganinsa." Sheikh Auwal ya amsa sannan ya mi Yazeed a hankali ya fara bu e idanunsa da suka yi masa nauyi suka rirri e kamar an yi ya in basasa a cikinsu, da ledar ruwa da Allurai ya fara yin tozali hakan ya tabbatar masa a gadon Asibiti yake, wani marayan kuka ya saki me cike da tausayin kansa, "Me rayuwa take nufi da ni? me yasa zan kamu da son wadda ta tsaneni? me yasa ba za ta tausayi min ba?" tambayoyin da wani sashi na Zuciyarsa ke yi masa kenan sai dai ba shi da amsarsu. Hajiya Laure da ke zaune a gefen gadon ta zuba tagumi ta yi saurin juyowa gareshi sabida jin sautin kukansa, "Sannu Yazeed, Allah ya baka lafiya, me ya jawo maka ciwon Zuciya Yazeed?" ta arasa maganar a marairaice tamkar da ance ar za ta fashe da kuka. a hankali ya ri o hannunta kam ya na cije le ensa, da alamu azabar da yake sha ta wuce kwatance, cikin sar iyar murya ya ce "Mommy! mutane nawa kika zalumta a Duniya? Mutane nawa kika wula anta a Duniya?? Da ni da ke na san har da Daddyna mun kasance baragurbi a cikin Al'uma, ban ta a ganin inda muka gina Alkairi ba; Daddyna kulluyaumin burinsa ya za a yi ya kere Abokin kasuwancinsa ko ta hanya me kyau ko marar kyau, ban ta a ganin inda ya kyautatawa marasa arfi ba, ko Islamiyya bai ta a ginawa ba bare Masallaci, Haka kema burinki kawai kar ya yi miki Kishiya, muradinki ki kere sa'a a cikin awaye, aikin kenan biye-biyen bokaye, ba ku da tunani sai haka, shi yasa kuka manta da ni kuka kasa Ba ni tarbiyar warai wadda kowa zai gani ya yaba, na kasance mazinaci an shaye-shaye; ban ta a yi muku nasiha akan abinda ku ke yi ba, nima duk da na samu damar da zan kyautata amma ba na kyautatawa kowa sai abokan ta adirancina, Kaiconmu Mommy!!, rayuwa ta riga ta sauya kuma daga yanzu har wani lokaci a koda yaushe kina iya rasani, kuma na yi imani da Allah ire-iren kusakuran nan namu su ne suke bibiyarmu, shi sharri an aike ne da zarar ya isa zai juyo zuwa ga wanda ya aika shi, ni dai Mommy ba na bu atar ki ara bawa wani boka Dukiyata, da ita zan gina Alkairin da muka kasa ginawa a baya ko hakan zai sa mu samu sassauci, zan nemi Malamai da Shaidu a biya wa anda suke bin Daddy bashi sauran kuma a sallameki nima a sallameni, in ya so sai ki yi duk abinda za ki yi da naki." Jikin Haj Laure ya yi sanyi salam tamkar an zare mata laka, wani sashin na Zuciyarta ya na son gazgata zantukansa musamman idan ta tuna irin abubuwan iftila'i da masifa da ta fara gani ta silar bin bokaye, wani sashin na Zuciyarta kuwa zigata yake yi akan cewar zafin ciwo ne ya sa Yazeed yake wa annan surutan, ba ta iya ce masa ala ba sai ma tagumi da ta buga ta lin aya a cikin duniyar nazari. Sai misain arfe goma na dare ya shigo don zuwa kiran da Abee ya yi masa. Husnee na zaune a bakin gado ta zuba tagumi da duk hannayenta, jin motsi ya sa ta agowa ta zubawa bakin ofa idanunta da su ka kumbura tulu-tulu sabida kuka, har ya araso ya zauna a kusa da ita idanunta na kansa, shi ma ya zuba mata nasa idanun na an lokaci kafin ya ce "Kuka kika yi ko? me yasa ma ba ki yi bacci ba?" cikin muryar kuka ta ce "Ta ya ba zan yi kuka ba Rislan? ta ya zan iya bacci bayan tin jiya rabona da ganin iyayena da an uwana? kuma ban san halin da suke ciki ba, kai ma kanka sunan ina tare da kai amma tin jiya ba ka ara waiwayata ba ni ka ai na kwana a akin nan, gashi ban san kowa ba kuma na ga ba sa aunata an gidanku Zara ce kawai take tausayina, haka suka dinga li owa suna kallona kamar ni ba kutum bace, kowa da irin kalma marar da i da yake fa e a kaina, kai ka ai zan gani Zuciyata ta yi sanyi amma ka i bani damar hakan!!!" ta arasa maganar gami da fashewa da wani kasalallen kuka me ta a zuciyar me saurarensa. Mashin tausayinta tuni ya da e da huda Zuciyarsa, a hankali ya sanya tattausan tafin hannunsa ya shiga goge mata wallar sai dai da ya goge da wata ta zubo. cikin nutsuwa ya ce "Kinsan ba na son ganin kukanki, za ki sa na yiwa kaina tsatstsauran hukunci." INDO* [9/10, 1:17 AM] INDO: * Ep 25 "To ai kai ne tinda ka tafi ka bar ni jiya ba ka ara nemana ba, ko kaya fa ba ni da su da na yi wanka ma sai na jikina na mayar, don Allah ka kai ni gida in auko kayan daga nan sai na yi magana da su Mommy." Tsirawa bakin nata ido ya yi ya na kallon yadda take maganar cikin yanayi me kama da shagwa a. Ga abinda take fa a masa amma shi tunanin da yake yi daban, a hankali ya sauke babban an yatsansa zuwa kan la anta ya na shafasu cikin nutsuwa da wani irin salo, cak!! kukan ya tsaya ta ago ido ta zuba masa ta na jin wani irin yanayi har cikin ranta, sassanyar iskar da ya hura mata a fuskarta ta sa ta yi firgigit ta an tsorata gami da fa awa jikinsa ta ame shi ta na sauke nannauyar ajiyar Zuciya. "Zan sa a kawo miki kayanki gobe, ba zan bari ki je gida yanzu ba." ya fa a cikin wata kasalalliyar murya me sigar ra Sake cusa fuskarta ta yi a cikin irjinsa ta ara lafewa sannan ta yi magana cikin