Sashe 8
Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ayeesha Abdulkareem INDO *M.W.A Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta bu e idanun nata, fayau babu shi a wurin, juye-juye ta fara yi ko za ta hango inda ya yi amma ko yallinsa ba ta gani ba. e ha a ta yi cike da mamaki ta tambayi kanta "Wai har ya ace min?" Wata ar budurwa kamarta ce ta araso inda take ta na fara'a, Husnee ta bi ta da ido gami da cewa "Ya akai?" "Don Allah so nake mu zama awaye, ni sunana Asiya ajinmu aya ma da ke'' Husnee ta murmusa cike da jin da i, dama tinda ta zo ba ta samu awa ba sai Zara ita ce su ke an mutunci su ma anayi ana fa "Ni kuma sunana Husnee, daga yau mun zama awaye to" Da sauri Asiya ta ce "na ji da i wallahi na gode" Husnee ta ce "Mu je mu yi Alwala" da to ta amsa sannan su ka sauka asa. Sai da ta je yin Alwalar ta lura hawayen idanunta sun dena zuba cak! kamar ba su yi ba, nan fa ta dinga murna kamar ta hau sama ta fa zaune yake kan aramin gado da aka yi shi da jan katako aka sanya masa ar katifa daidai da shi, sai shimfi ar gado ta bargo me taushi. Salansa da an Bakwai na tsaye gefensa curko-curko, Waya ce a hannunsa ya na latsawa cikin kwanciyar hankali, Lambar IP Khalil ya lalubo gami da tura kira. Inspector Khalil na zaune kusa da matarsa su na kashe love wayarsa ta yi ara, aramin tsaki ta yi gami da cewa "A daren nan ko waye me kiranka?" Murmusawa ya yi cike da son ko ansa ya ce "Nifa an Sanda ne, ko da yaushe ma ana iya kirana, ba ki saba da hakan bane sabida ban riga na Aureki ba, amma yanzu tinda mun yi aure ai za ki ga abubuwa daban-daban" murmusawa ta yi kafin ta ce "Gaskiya ne Jarumina, ba ka auka ba to har kiran ya katse, ko in baku wuri ne?" Da sauri ya ce "No zauna abinki" daidai lokacin wani kiran ya ara shigowa, latsa kore ya yi gami da aza wayar kan fala-falan kunnuwansa tubarkallah. aramin Sufeto, Albishir zan yi maka akan mutuwar Abokin wanda case insa ke hannunka, Alhaji Habibu Mai Kwalli; na kashe shi." "What!!!!!!" IP Khalil ya fa a cikin ka uwa da razani. "Yaushe? kuma ta ya? me ya yi maka?" "Idan ka matsanta bincike za ka zamo na gaba a wa anda za su mutu don kai ma akwai tamu da kai, amma ba na son kasheka yanzu tamkar na kashe maciji ne ban sare kansa, har sai na kashe ashin bayanka sannan zan kasheka! na fa a maka ne don ka rubuta a file ina ba wai don ka wahalar da kanka wajen kamani ba; na samu labarin ka yi Aure, waccan ha uwar tamu ba ka zo min da maslaha ba bare in yi maka murna, Happy marriage to you, a gaida iyali. Ya na kaiwa nan ya katse kiran gami da mi awa Salansa ita, an Bakwai ya mi o masa wata gami da cewa "Gaba salamun baya salamun, Sahun Giwa me badda na Ra umi, SAHUN KEKE Ba a Gane Gabanka!!!" ar wayar ya yi ya na arin yin wani kiran aya wayar tashi ta fara ara. IP Khalil, kamar sakatar sakarai haka ya saki baki, duk jikinsa ya yi sanyi kamar an zu e masa ruwa, nazari yake akan shaharar ta'addancin Risslan, ya rasa ma abinda zai yi masa ya kawar da shi, shi dama kowa ya san ba mutumin kirki bane bare ayi masa wani mugun sharrin, Zulaihat ba ta lura da halin da ya ke ciki ba don hankalinta na kan kiran da take son yi, "Nima bari in kira Babana mu gaisa, tinda mu ka yi Aure ba mu gaisa da shi ba ." IP Khalil dai ba baki sai kunne. Zaro wayar ya yi daga Aljihunsa ya zubawa screen in ido har na an lokaci sannan ya auka ba tare da ya ce komai ba, "Baba!!!" muryar Zulaihat ta doki dodon kunnensa, kasa amsawa ya yi har sai da ta ara kiransa sannan ya ce "I'm So sorry my daughter! me kike yi har yanzu ba ki yi bacci ba? ina mijin naki??" ya jefeta da tambayoyin a lokaci aya. zaku awa ta yi kana ta ce "Sorry for what my Daddy? kai fa ba ka laifi, ka ganshi nan ya na gaisheka, ko in ba shi ku gaisa?" Da sauri IP Khalil ya aga mata hannu don kuwa ba zai iya magana ba a yanzu musamman da babban mutum wanda take kira Baba. Risslan ya ce ''No need, barshi kawai ina amsawa, na san ba kya rabuwa da orafi shiyasa na fara baki ha uri don na san dole za ki yi" Ta ce "To shikenan, amma Baba ba ka zo Aurena ba ya kamata ka zo ganin aki, amma tinda duk ba ka zo ba Birthday ina ya kusa, amma za ka zo ko??" "Sai yadda yanayi ya nuna Daughter, ta yuwu ma ko na zo ba za ki ganni ba, amma kar ki damu kawai." Rausayar da kai ta yi sannan ta ce "To sai da safe" "Allah i kaimu" Bai jira cewarta ba ya katse wayar, ya ajiye gefe, Kira ya tura da aya wayar ba ata lokaci aka auka, kai tsaye ya fara da cewa "Zan shigo garinka gobe da daddare, a janye tsaro." IP Hussain ya ce "An gama sir!" Daga haka ya katse wayar, kiran CP ne ya shigo Salansa ya aga kana ya mi o masa "Yalla ai" shine abinda ya fa a sannan ya yi shiru don jin abinda CP zai ce "Na san ka sani ba sai na fa a maka ba, kuma na san za ka aikata, fatan nasara an nasarawa, ni kuma a ta nan zan dafe komai." CP ne ke yin maganar cikin hikimar harshe. Risslan ya ce ''Na lode kuma zan ka ar, so na gana da IP Hussain ma ta angarensa ba damuwa; Shu'umin Jami'i Yalla ai CP Abubakar Ado Gezawa!" CP ya yi dariya me isarsa kana ya ce "Ja'irin Yaro Muhammad Risslan Sheikh Muhammad Risslan! sai na ji ka zuwa jibi don gobe na san ba ka da lokacina." Risslan ya ce "Ba shakka Bukar, amma ko me zai faru ka auka kawai ha ari aka yi mota ta kama da wuta, banda tsananta bincike" "Yes sir!" CP Abubakar Ado ya fa a cikin sigar Zolaya. Da haka su ka yi sallama sannan Akhiee ya mi e ya na cewa "Yau da wuri zan shiga gida, ku dafe ko ina, ku kula da sauran Iyalina, ina Zare da Aci-bal-bal suke ne??" Salansa ya ce "Su na can su na bawa shegiya wuta Ya Babba! nake li a maka Zare ya kwashi harawa, ya kwashi harawa, shiruu!! ka ke ji, magana ma an iska ba ya iya yi." Risslan ya ce "Bari gobe zan ci Ubanshi, shi ga aramin kai ga son aukar kaya" an Bakwai ya ce "Inaa! lumbu-lumbu ce, yanzu ka kai masa sara nan za ka gane iskancin nashi na arya ne, a sauka lafiya me gayya!" ya arasa maganar tare da rissinawa Risslan, "Hmm!!" kawai ya ce sannan ya fice. aton kango ne me auke da part part da akuna daban-daban a ciki ma in ba zagayawa za ka yi ba sai ka yi kwana da kwanaki ba ka gamu da wani ba. ko da ya hau dokinsa ba su dena binsa ba har sai da ya fice daga tafkeken Kangon. Washegari Bayan Sallar Isha'i ya auki hanyar Kwanar an Gora a kan dokinsa. Bayan ya one motar ya kama hanyarsa ta komawa gida ba tare da tsoron dare ko shakkar wani abu ya gifta masa ba. Da sauri ya ago kai ya na kallon mahaifin nasa cike da rashin sanin abin fa a, Murmushin gefen baki Hamza ya yi, a ransa ya ce "Ai Yau taka ta are fa en gaskiya ya zama dole." cikin son kauda zancen Akhiee ya ce "Abhi! wani abin su ka ce na yi?" Abhi ya ce "A'a, na ji ne su na ta zancenka ba dare ba rana dole na san akwai abinda ka yi musu." Gyara zama ya yi sannan ya ce "Abhi! ka san dai an Adam ba a iya yi masa, kawai fa kwana biyu ne ban je Makaranta ba shine ake ta wannan tashin hankalin." Abhi ya jinjina kai cike da gamsuwa sannan ya ara da cewa "Me yasa to ba ka zuwa? ka san fa kai Malam ne." "To ai abubuwan ne da yawa Baba, ka ga ana fita nema haka sannan ka ga yanzu damuna ce ina yawan zuwa gona, shi yasa amma ko jiya... au jiya ban je ba, amma shekaran-jiya na je, ka san fa ni manomi ne Abhi" Abi ya yi murmushi irin nasu na manya gami da cewa "Aff warai kuwa! ni ai na sani dama, ai wannan duk ba abin damuwa bane, amma da zarar ka dawo daga gona ka shirya ka je makaranta abinka, ka ji ko Malam?" "To Abhi in sha Allah" Hamza da ba in ciki ya ma ale masa a zuciya kasa dannewa ya yi ya ce "Wallahi Abhi arya yake yi" wani mugun kallo Akhiee ya zuba masa, wanda ya sa hantar cikinsa juyawa. Abhi ya ce "To fa! Dattijo!" "Na'am Abhina" ya amsa a agauce, " an uwanka ya ce arya ka ke yi, me ke faruwa bayan haka?" "Wallayi Abhi ranar nan ne aka samu akasi Yasayyadi Jameel ya doke ni shine fa na ji zafi raina ya aci, sai na an yi masa rashin kunya, shine fa wai a dole sai an gaya maka, kai ni naga ta kaina" ya arasa maganar ya na jimanta al'amarin. Abhi ya jinjina kai kafin ya ce "A Kul! kar a ara yiwa manya rashin kunya, kuma shi malaminka ne ai, Malami kuwa an uwan uba ne ya na da kima da daraja, lallai a kula, zan nemesu in gaya musu kar in ara jin ana zancenka." "Na gode Abhi, ni yanzu zan fita zan je gona in duba yanayin aikin