Sashe 38
Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
sai don ya na son su cimma manufarsu akan Akhiee. Husnee duk da hankalinta ba a jikinta yake ba ta na jinsu, kuma ta fahimci Muddassir ya na goyon bayanta don haka ta wani gefen farin ciki ya lullu eta. Kasancewar Sheikh Auwal ya kira shi ya sa ya shigo gida da wuri tin arfe sha aya na dare, Lokacin wasu daga cikin Yaran Gidan sun yi bacci, Wasu kuwa Su na zazzaune curko-curko a tsakar gida kowa na jiran shigowarsa, wasu sun shirya yi masa rashin mutunci wasu kuwa gulma ce ta tsayar da su don su ji yadda za ayi. A tsaye ya tsaya fuskarsa ba walwala a ta aice ya ce "Ga ni" a tsawace Yaya Babba ya ce "A tsaye za ka tsaya mana sabida rashin abi'a?" Sai da ya doka dogon tsaki kamar ya tsaga gini sannan ya dur usa cike da tsanar an uwan nasa ya ce "A fa a mini abinda ya sa aka nemo ni, idan kuma bala'in ne ya motsa kowa sai ya yi nashi duk zan iya auka." Yaya Aminu ya rarumo takalmi a kusa da shi ya jefo masa gami da cewa ''Buhun Ubanka! mara kunyan banza shashasha; Baba Sa'idu bashi takardar nan ya ga tsiyar da ya jawowa kansa." Baba Sa'idu da ya zuba tagumi da duka hannayensa sai a lokacin ya ce "Uhm! to" Takardar ya mi a masa gami da cewa "Yarinyar da ka je ka Aura to iyayenta ne su ka kai ararka Kotu Ranar Alhamis me zuwa za a zauna sai ka tanadi abin gaya musu, Bai kamata ka yi haka ba Muhammad, ka ga mu ba mu san ka yi ba amma ka jawo mana maganganun da zagi na jama'a, gidanmu gidan mutunci amma ta sanadinka ana yi mana wani banzan kallo, ka arta ka saki yarinyar nan tin kafin ka ara jawo mana wani mugun tabon." A duniya in akwai abinda Akhiee ya tsana to na biyunsa a ce sanadinsa mutuncin gidansu ya zube, cikin acin rai ya fizgi takardar sannan ya ce "Ba kotu ba ko Duniyar za su ha o ta taru a kaina ba zan saki Asma'u ba bare wata Kotu, gwara ma ku dena wahalar da kanku kowa ya je ya yi baccinsa, Asma'u tawa ce sa anin ni kuma sai dai Mutuwa domin zan zubda jini akanta. Inna Huwaila Matar Baba Sa'idu ta sa salati da sallami kafin ta ce "Kai annan ka ji tsoron Allah, wai ni Huwaila ina ganin masifa a gidan nan!!, Yaro aya amma ya zama wake aya me ata miya??" Ai kuwa kamar jira su ke yi ta bu e musu hanya nan fa wasu daga ciki suka fara sako tasu maganar, duk cikinsu ba me fa ar da da i sai ba en maganganu abin har ya wuce kansa ya koma kan Mahaifiyarsu, wasu ma cewa suke yi ba Jinin gidan ba ne. Sheikh Auwal dai da abin Duniya ya ishe shi sai ya zame jiki ya wuce Turakarsa, ya na shiga ya nemi wajen zama dirshan sannan ya bawa kukan da ke cin arfinsa damar fitowa. "Allah ka fi mu sanin abinda ke tattare da Yaron nan, Ya Allah ka sani Mahaifiyarmu ba halinta ba ne haka Mahaifinmu ma Ya Allah indai ba jininmu ba ne Allah ka nesanta mu da shi ka fitar da shi daga cikinmu ka bayyanar da gaskiyar asalinsa." Addu'ar da yake yi kenan a cikin kukan nasa, Zuciyarsa cike take taf da unci da tarin damuwa ga zafi da unar abinda ke faruwa a cikin wannan Babban gida nasu. Zara kuwa ta kasa fitowa daga akinsu, ta na jin yadda suka are masa tatas ba abinda ta iya yi sai aikin kuka, har cikin ranta ta na ba in cikin irin abinda ake yiwa an uwan nata. Sai da ya gama saurarensu aya-bayan- aya sannan ya kakka e rigarsa ya tashi, kai tsaye akinsa ya wuce ya zauna gefen gado ya zuba tagumi, jin idanunsa yake yi tamkar an ora su akan garwashi ana gasa su, Zuciyarsa kuwa har wani turnu u take yi tamkar za ta fito ta baki, da zai iya yin kuka da ya yi ko zai samu salama sai dai kash!!! shi da kuka sun riga sun yi hannun riga tin kafin Mutuwar Mahaifiyarsa. "Come hare my son!" muryar Mother ce ta kara e kunnuwansa ya yi saurin ware idanunsa domin ganin ta inda ta ullo. Kasancewar akin ba haske ya sa ba ya ganinta sai dai hasken idanunta da su ka yi kalar Golden ya iya gani. Da sauri ya mi e ya nufi inda take ta yi saurin rungume shi tsam!!!!. nannauyar ajiyar Zuciya ya sauke Kafin ya fara maga cikin rarrabewar Murya "My Mo...therh!!!... me..yasa..... suke yi min haka??? Shin da gaske..... ni ba.....Jininsu ba ne???????" Yadda yake maganar ba aramin ta a Zuciyarta abin ya ara yi ba, ranta ya ara aci Zuciyarta ta ara dugunzuma, a gefe guda kuwa tsananin tausayin an nata ya na ara taso mata, ba ta iya bashi amsar tambayarsa ba sai dai ta ce "Yau ban amince ka kwana a gidan nan ba, ka kasance tare da ni ana....." Ba ta jira abinda zai kuma cewa ba ta auke shi su ka ace daga akin. INDO* [9/6, 7:41 PM] INDO: * Ep 22 Tinda ta aukeshi bai ara sanin inda kansa yake ba har sai da Asbah ta yi da ya ji Masallacin cikin gidansu an yi kiran Sallah sannan ya farka. Tin kafin ya bu e idanunsa ya ji umin Mutum a kusa da shi, ya yi shiru ya na sauraren Bugun zuciyarta da ya tabbatar masa ba kowace ba ne face Razia. Cikin nutsuwa ya sauke wata nannauyar ajiyar Zuciya kafin ya bu e idanunsa ya orasu akan kyakkyawar fuskarta. Bacci ta ke yi cikin mutsuwa da kwanciyar hankali, kallo aya ya yi mata ya gane ba aramin jin da in baccin take ba don da alamu ma ta da e ba ta yi me da insa, a take kibiyar tausayinta ta soki Zuciyarsa, ya zuba mata ido tamkar ba zai dena kallonta ba, ya da e cikin wannan yanayin kafin ya ara janyota jikinsa ya ringumeta tsam, ya na jinta har cikin ransa. Cikin baccinta ta ara jin sauyin yanayi don haka ta ara du uneshi ta ja mumfashi ta sauke ta ci gaba da baccinta. Mother ta ce shigo akin cikin suffar Mage, bayan ta zo daf da Gadon ta koma suffar Mutum, cikin tattausar muryarta ta ce "Rislan! kar ka biyewa Razia ka makara a Sallah fa." Lumshe ido ya yi gami da sauke wani gwauron nishi kafin ya yi magana tamkar wanda aka yiwa dole "Uhm! Uwa zan tashi; ba na so na nesanta da ita ne ta farka." Mother ta murmusa kafin ta ce "Abinda ya zama dole ne ana, a Masallaci fa har an idar da Sallah." Bai ce komai ba ya janye Razia daga jikinsa a hankali ya gyara mata kwanciya sannan ya sakko ba don ransa ya so ba, haka kawai yau ya tsinci kansa da son kasancewa tare da ita. Ya na idar da Sallah ya yi musu Sallama ya wuce wajen su Rahma don jin yadda suka kwana. Yau Ta kasance Ranar Alhamis, Ranar da wasu ke okin zuwanta wasu kuwa su na cike da fargabar ganinta. Sheikh Auwal, Babban Yaya, Baba Sa'idu, Akhiee Daddy, Mommy, Muneeb, Muneer, Husnee... Malam Kabiru, Malam Usaini Duk sun hallara a cikin Kotun yayin da ta auki shiru kowa ya mayar da nutsuwarsa akan abinda ke faruwa a cikinta. Ana kammala sauraren arar Wasu aka karanto ta su Akhiee, Me Shari'a ya bu aci Matar da Mijinta su fito. Bayan sun fito inda aka tanadarwa duk wanda zai yi magana su ka tsaya, Mai Shari'a Ya yiwa Husnee tambaya akan da gaske ne an aura Aure ta amsa masa da eh. Sannan aka dawo kan Akhiee aka tuhumeshi akan amsa laifinsa sai dai shiru bai ce ala ba, juyin Duniya ya yi musu banza har mai Shari'a ya gaji ya aga arar tare da cewa Akhiee ya nemo Lauya. Da haka aka tashi ba tare da an cimma wata matsaya ba kowa ya san inda dare ya yi masa tare da tunani iri daban-daban, musamman a angaren Husnee wadda ta cika da tsoro da firgici sabida jin ya yi shiru, ta na matu ar tsoron ya ce zai saketa. Akhiee kuwa ko ta kansu bai ara bi ba shima ya kama gabansa, Su Yaya Babba sai fa a su ke yi kamar za su ci babu, shi dai Sheikh Auwal ya yi musu banza. Hajiya Laure Sanye take cikin lintsumemiyar Atamfa tsadaddiya inkin riga da Zani ta cokara auri ture ka ga tsiya. Cikin takun asaita ta fito Falo agwas- agwas kamar budurwar agwagwa. Ma'u da Talatu su na ta an gyare-gyare kasancewar Yamma ce, kafin ta zauna ta kallesu fuska a dake cikin nuna yama da wula anci ta ce "Menene haka? wannan aiki ku ke yi ko iskanci?? wai ba na ce kar wannam azamar ta ara shigo mini Falo ba ma??" arasa maganar ta na tsare Ma'u da idanu. Ma'u kuwa tin da ta ganta jikinta ya au karkarwa domin kuwa mugun tsoronta gami da tsanarta ta ke ji, ko hanya ba ta son ha awa da ita a yanzu. Talatu ta rissina gami da cewa "Ayi ha uri za mu gyara." Dogon tsaki ta lafta kafin ta ce " azamar banza tarin najasa; za ku fice ku ban wuri ko sai na daddallawa Yarinya mari?? an matsiyata." Jiki na rawa Ma'u ta yi gaba ta na kuka asa- asa Talatu ta bi bayanta cikin sanyin jiki. Hajiya Laure ta yi wafa kafin ta karkace ta yi ja ar a kan Sofa. wani mugun ihu ta zurmu a jin ta zauna akan wani abu tamkar Allura, azaba ta ratsata har tsakiyar kanta, a dur ushe ta mi e ta ma kasa tashi tsaye sabida azaba gabaki aya mazaunanta sun auki wuta, lokaci guda idanunta su ka ciko da hawayen azaba. Sai da ta an huce sannan ta juya ta dudduba inda ta zauna in ko za ta ga wani abu sai dai fayau ba wani abu ba alamunsa. Canja mazauni