← Book details Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 47

Sashe 39

Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta yi zuwa kan kafet don kuwa ta ji attaruhu ko za ta ara zaman kan kujerar ba yanzu ba, a asan ma a karkace ta zauna ta na yi ta na yatsine fuska don kuwa har yanzu ba ta dena jin zafi ba. Ta na nan zaune ta na hutawa ba a fi minti biyar ba ta ji wani irin taku waras- waras ya na tinkarota, ta shiga kalle-kalle amma ta ga fayau kamar ba a ta a halittar mutum ba, tsoro da firgici su ka arsu a Zuciyarta lokaci aya, Talatu ta fara walawa kira da tunanin ko itace a wajen, jin shiru kuma ga takun ta na ji ya sa ta yun ura ta mi e cikin sauri ta nufi hanyar da zata bar Falon. Garam!! ofa ta rufe, nan take wata muguwar dariya irin ta Boka Barore ta kara e Kunnuwanta, Ihu ta fara kwararawa sai dai kash!! ta na farawa ta ji kamar an sa buredi an toshe mata ma ogoro muryar tata ta dena fita. Inuwar Mace ta gani a gabanta ar siririya sai yalwar gashi har ugu shima ga inuwarsa nan buzu-buzu, Haj Laure ta ara zazzaro ido gwale-gwale kamar sa fa asa, Zuciyarta na wani mugun duka tamkar ana surfe da sussuka a cikinta. Da kyar ta samu ta taka da gudu don komawa Bedroom, ta na zuwa ofar bedroom in taga wannan inuwar a gabanta, sai juyi take ta na kwarkwasa ga ugun nan tamkar na babe sai fa in mazaunai an ciri-ciri. Wani mugun burki ta ja wanda ya sa ta kusa shi ewa sabida Salon bugun Zuciyarta da ya canja. Tsere su ka shiga yi ita da Inuwar a Falon ta na gumi ta na kuka ta na majina ta na yarcewa ita kuwa Inuwa ta na ci gaba da razanata, sai da ta galabaita sosai har ta kai ba ta iya tafiyar ta zube a wajen turuss!! sannan inuwar ta matso daf da ita ta na wata mahaukaciyar dariya, ba tare da ta dena dariyar ba take magana cikin murya marar da in ji "Ba a raina aikin Boka Barore!!!, sannan ba a cin Amanarsa a canja wuri, ba a zaginsa ko a bayan idonsa!!!!, idan ya fara yiwa mutum aiki har sai ya yi nasara yake denawa ba zai ta yale ku ku je wajen wani Bokan bahahahaha!!!!" ta arasa maganar gami da aro sautin dariyarta, Ta kai minti aya a haka sannan ta ace tamkar ba ta ta a wanzuwa a wurin ba. Haj Laure ba ta iya tashi ba sai ara bajewa da ta yi ta kwanta ta saki wani anyen kuka me matu ar ta a Zuciya. Su Ma'u su na fita su ka ci karo da Yazeed ya na arin shigowa, ya na ganinta tana kuka ya yi caraf ya ri o hannunta, a zafafe ta fara arin fizgewa sai dai ya hanata damar hakan, Cikin sassanyar murya ya ce "Ki nutsu don Allah ki fa a min abinda ke damunki, Mommy ce ko???" A tsiwace ta ce "Ni ka yaleni, ka sakar min hannuna ni ba ar iska ba ce wallahi, kuma zalumcin da aka yi mini Allah zai saka min." "Ke Talatu yi tafiyarki" ya fa a ya na kallonta, ta sunkuyar da kai sannan ta ci gaba da tafiya. mayar da hankalinsa ya yi kan Ma'u tamkar me shirin fashewa da kuka ya ce "Don Allah ki yi ha uri ki saurareni, ki kar i kukana sannan ki ji aina Ma'u! maganar gaskiya kin jefani cikin wani yanayi, na rasa nutsuwata ba dare ba rana tunaninki nake yi, ina son sanin abinda ke damunki." Cikin tsananin tsanarsa ta ce "Ba zan ta a gaya maka abinda ke damuna ba azzalumi, kuma ka yaleni ba na son ganinka na tsaneka!!!" ta yi maganar ta na kuka tamkar ranta zai yi fitar burgu ya bar gangar jikinta. imammun idanunsa da su ka riki a zuwa kalar ja ya zuba mata na an lokaci kafin ya fara magana tamkar zai yi kuka "Ma'u gareki sam ban zamo azzalumi ba kuma ba zan ta a zamowa Azzalumi gareki ba, burina kullum na inganta rayuwarki domin ina bu atar rayuwa tare da ke, Ina...sonki Ma'u, ko da za ki tsaneni hakan ba zai sa na canja ba, sai dai in kasheni ki ka yi shine na san dole zan barki, kuma in na mutu ki sani na mutu da tsananin Sonki, ko da ba ki kasheni ba idan na mutu ko a yanzu ko anjima ke ce silar mutuwata domin ba ni da wata damuwa a yanzu face ke!!" ya arashe maganar cike da son nuna asalin gaskiyarsa. "Ni ba zan ta a yarda da kai ba, kuma ba zan ta a sonka ba, na tsaneka!! na tsaneka!!!! kuma tsakanina da ku sai Allah ya yi mana Hisabi, ni ka sake ni in tafi." Gudun zuciyarsa ne ta aru, lokaci guda yanayinsa ya ara canjawa damuwa da tashin hankali su ka kawo masa hari lokaci aya, "Ma'u me na yi miki? me yasa ba za ki soni ba??, indai wani hali nawa ne ba kya so Wallahi zan dena indai har za ki zamo gatana; Ma'u Bansan ya akai ba kawai na wayi da narkon Sonki a Zuciyata, wallahi ji nake idan na rasaki tamkar zan rasa raina, idan na ji kin ce kin tsaneni tamkar ana watsa min ruwan wuta haka nake ji, ki tausaya min kar ki hukunta ni ta wannan hanyar ko da kuwa na yi miki laifi, wallahi ba wasa ba yaudara a cikin zancena; duk yawan Matan Duniya ke ka ai nake yiwa irin wannan Makahon so, Ma'u kar ki bari rayuwata ta salwanta ta sabauce sabida soyayyarki Please!!!" daga yadda yake maganar za ka gane ya na cikin mawuyacin hali gami da tashin hankali, Ma'u kuwa ta gaji ma da jin muryarsa, ji take da akwai wani makami a kusa da ita ba abinda zai hanata buga masa ta wace hannunta, ba ta ce masa cikal ba sai kuka da take yi kamar ma ogoronta zai tsage sabida shashsheka. Sakar mata hannun ya yi gami da cewa "Allah ya huci Zuciyarki, ba yadda na iya ne dole sai na gaya miki, na kamu da cuta kuma ke ce ka ai maganinta." "Allah ya sa ma ka mutu na huta azzalumi" abinda Ma'u ta fa a kenan ba tare da ta jira amsa ba ta arta da mugun gudu. Da ido ya rakata har ta acewa ganinsa sannan ya kutsa kai Falon Haj Laure. Su na gama turnu u da inuwarta ta kwanta ya shigo. Ya yi mamakin ganinta a tile a gefe kamar kayan wanki, amma da yake hankalinsa ba a jikinsa yake ba bai bi ta kanta ba ya nemi wuri kan Sofa ya zauna gami da buga tagumi ya lula duniyar tunani. A hankali sautin kukanta ya fara dawo da shi hayyacinsa ya yi saurin mi ewa ya na cewa "Mom what happened to you??" ar zaninta da ya kwance ta janyo ta face hanci sannan ta ce "Ba abinda bai faru ba ma, inuwar mata na gani ta na bina ta na tsorata ni, kai kuma ba ka tashi shigowa ba sai da ta tafi, inda kasheni ta yi sai dai ka zo ka au gawata kenan ko?" zama ya yi a gefenta ya ce "Ke ce ba ki da aiki sai bin bokaye Mommy,, ila ma wani kika yiwa asiri ya dawo kanki, ai ga ranarta nan sai ki dena." Ta ja numfashi ta sauke, cikin muryar kuka ta ce "Ba za ka gane ba ne Yazeed ka barni da abinda yake damuna!" rai a ace ya ce "Nima ina da damuwa me tsanani ma kuwa, kuma ko shakka ba na yi kece tushen damuwar tawa; Allah ya sawwa e to" ya na kaiwa nan ya tashi ya bar mata Falon. Ya na fita kuwa tsoro ya ara kamata ta yi sauri ta tashi ta fita can harabar gidan don kar ma a ara ritsata a aki. 01:32AM kowa ya rintsa amma ita baccin ya gagari idanunta, kwanciyar ma har ta isheta don haka ta tashi ta zauna gami da zuba tagumi ta ci gaba da tunane-tunane, ta na cikin wannan Halin ta ji wayarta na ara a ashin filo, jiki a sanyaye tamkar wadda aka zarewa laka ta zura hannu ta janyota, zuba mata ido ta yi na an lokaci sannan ta auka da wani kiran ya ara shigowa. "Yau ma ba ki yi bacci ba Ko?" cusa kanta ta yi a tsakankanin guiwoyinta ba tare da ta ce masa ala ba, jin ta yi shiru ya sa shi cewa "My wife!!" ya yi maganar cikin wata kasalalliyar murya me unshe da sa onni daban-daban wanda kai tsaye ta fito tun daga asan Zuciyarsa, ta yi saurin lumshe idonta gami da sauke sassanyar ajiyar Zuciya, cikin muryarta da ta dashe ta ce "Akhiee!! tunani ya hanani bacci, da na rufe ido nake fara mafarkai." "Idan ki na gaya min haka hankalina gaza kwanciya yake yi Asma'u, ki samu nutsuwa don Allah." a kai ta yi tamkar ya na kallonta. Sun auki lokaci su na sauraren numfashin juna ta wayar ba tare da kowa ya yi magana ba, Akhiee ne ya kaste shirun da cewa "Ki na da babban matsayi a wajena, kar ki cutar da kanki ta hanyar bin son Zuciyata, ki nutsu ki yiwa kanki za i duk hukuncin da kika yanke na amince; Asma'u! ba wani abu da zai sa na sake ki sai dai in kece kika furta cewar ba kya sona ko kuma ba kya so ki rayu tare da ni, indai kin furta hakan a take nima zan sakeki, sa anin haka kuma ba zan iya rabuwa da ke ba, indai kina son farantawa iyayenki ta hanyar rabuwa da ni kina da dama; Ki yi bacci sosai Sai mun ha u a Kotu gobe." Daga haka ya katse ba tare da ya bata damar ta yi magana ba, bin wayar ta yi da kallo kalamansa na dawo mata, nan take su ka shiga yi mata juyi a walwa, menene mafita? ta bi iyayenta ta rabu da shi? ko kuwa ta za eshi a matsayin abokin rayuwarta??, shawarwarin da take
Chapter 39 · 0% Book details