← Book details Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 47

Sashe 2

Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

gani don haka ke ki yi gaba ina zuwa, zan tafi da wannan me gadin naku don ba yadda za'ayi a ce bai san anyi wannan kisan ba dole da sa hannunsa." Hajiya Laure ta sharce walla gami da majina cike da farin cikin jin furcinsa ta ce "Na gode IP sai kun zo in." kai ya gya a mata kana ya nufi hanyar fita cikin takunsa na asaita da jin kai, Hajiya Laure ta bi bayansa, Constable Saleh kuma ya cukumo Tala me gadi. Har Inspector Khalil ya aga afa zai shiga mota Constable Saleh ya dakatar da si da cewa "Sir!! na yi arin danne abinda ke raina amma na kasa, wallahi da alama ka fara aiki a wannan Office da afar hagu domin da alama SAR A ta yi Rikicinta a wannan gida." Fasa shiga motar ya yi cikin rashin fahimtar inda kalamansa su ka dosa ya zuba masa idanu kana ya ce "Me ka ke nufi da haka? wacece SAR A??" "Ba mace ba ne, Sunansa na gaskiya MUHAMMAD RISLAAN MUHAMMAD amma kowa da kalar sunan da yake kiransa sabida ya buwayi duniya, Sir! ina ganin a lalla a Hajiyar nan a rufe wannan Case in in ba haka ba kai ma zaman Office innan sai ya gagareka, na ga irinka da yawa wa anda su ka zo su ka koma sabida buwayar Yaron nan." Murmushin rainin hankali Inspector Khalil ya yi kafin ya ce "Ina ne gidansu??" Cikin zaro ido Constable Saleh ya ce "Ka yi mini rai ka gafarce ni Yalla ai kar ka ce za ka kama bawan Allahn nan, wallahi idan ya san ni na gaya maka shi kenan na mutu, Yalla ai ina da mata da a uku yanzu ma ta na auke da juna biyu, ka temaka min kar ka yi silar zaman iyalina marayu." Inspector Khalil ya dafa kafa arsa cikin sigar rarrashi ya ce "Kai fa Jami'i ne akan me za ka ji tsoron wani karanka a miyar mutum? kar ka damu ba zan bari ya san kai ne ka fa a ba, yanzu bani information nashi, a ina za mu same shi?" Jiki na rawa Constable Saleh ya ce "Ban sani ba Yalla ai shi kamar iska ya ke ba shi da tabbas, idan ka ganshi anan a yanzu za ka ganshi a can, amma ina da lambar an uwansa malamin wata makarantar Islamiyya idan ka kira ka tambaya tayuwu ya na makarantar amma fa sai sa'a za a same shi." Cike da jin da in hakan Inspector Khalil ya an bubbugi kafar Constable Saleh ya na wani irin murmushi me cike da ma'anoni, cikin salonsa na iyayi ya ce "Jami'i me basira, ba ni lambar." Cikin rawar jiki Constable Saleh ya mi awa Inspector Wayarsa ba tare da ya ce komai ba don kuwa ya hau dokin tsoro da firgici, ya gama sallamawa ya sa a ransa kwanansa ya are. sai da kiran farko ya katse a na biyu aka aga tare da yin sallama, Inspector Khalil ya amsa sannan ya ci gaba da cewa "Ina magana da Sheikh Auwal ne??" a aya angaren Sheikh Auwal ya ce "Eh ni ne amma ban gane me maganar ba." "Sunana Inspector Ibrahim Musa Rano wanda aka fi sani da Inspector Khalil, ina neman Muhammad Rislaan Muhammad ne." dimm!!!! Zuciyar Sheikh Auwal. "Muhammad Rislaan Muhammad?? What Happened??" Sheikh Auwal ya fa a cike da tsoron abinda zai fito daga bakin Inspector. "I suspect him of murder, so i will arrest him, i need his informations, ina son sanin inda zan sameshi, ka ba ni ha in kai Ya Sheikh kar ku wahalar da hukuma." wani irin tu i zuciyar Sheikh Auwal ta ke yi gami da tsalle tamkar za ta fasa irjinsa ta fito, cikin tsantsar acin rai ya ce "Kar ka kuma tambayata bayanan Akhiee domin ba shi da tabbas, yau dai ka yi sa'a ya zo makaranta, ka zo nan ka same shi." Farin ciki ne ya lullu e Inspector Khalil, ya murmusa sannan ya ce "Godiya nake Sheikh Auwal sai na zo in." Constable Saleh ya ce "Yalla ai na ga ka na murna?" "Na samu inda ya ke cikin sau i, ka ga dole ne na yi murna, ba ka sani ba ne dominsa aka turo ni nan aiki ba zan gushe ba har sai na ga bayansa, yanzu Asibitin ya kamata mu je ko Makarantar?" "Yalla ai na san ana bu atarka a asibitin nan ko ba za ka yi komai ba ya kamata a ganka, mu je can in in yaso daga baya sai a je makarantar" Constable Saleh ya yi maganar cikin rawar murya kamar zai fashe da kuka. Dariya Inspector Khalil ya yi sannan ya ce "Ka na da tunani me kyau, ya kamata ka zama babban Jami'i." Daga haka ya shige mota, Constable Saleh ma shiga ya yi a ransa ya na cewa "Bayan ka gama kashe ni tin yanzu" Tala me gadi kuwa banda kuka ba abinda ya ke rusawa ya rasa ma ko bakin magana bare ya ce musu shi bai san anyi kisan ba. Kai tsaye Asibiti su ka nufa don ganin yadda komai ke tafiya a angaren binciken gawa. Babbar Makaranta ce me auke da sassa da ajujuwa daban-daban, makarantar na auke da umbin alibai masu yawa manya da anana, mata da maza, akwai wadatattun malamai masu koyar da ira'a daban-daban ba wanda ba'a yi a makarantar indai na Islam ne. a wani babban Aji me auke da mata da maza kowanne gefen zamansu daban, duk insu sun du ufa akan karatunsu, dadda an sautin karatun Qur'ani ne ke tashi ta ko'ina a ajin gwanin sha'awa. Sheikh Auwal na zaune kan kujerarsa ta Malami ya zuba tagumi da duk hannayensa, tunanin ma irin hukuncin da zai yiwa Rislaan ya ke, a duk iya tunaninsa ba hukuncin da zai iya yi masa wanda ya wuce yi masa shegen duka. ewa ya yi tsaye ya na rarrabawa aliban nasa idanunsa da su ka yi jajir sabida acin rai, "A dakata!" ya fa a cikin kamilalliyar muryarsa. Shiru ajin ya yi kamar ruwa ya cinye mutanen cikinsa, an kai 10 second cikin yanayin shirun sannan Sheikh Auwal ya ce "Zahra'u Muhammad!" cikin sanyin jiki ar budurwar ta mi e gami da cewa "Labbaika" Ganin irin halin mugun acin ran da an uwan nata ke ciki ya ara karyar mata da zuciya, zirrrr hawaye su ka fara sharara akan kumatunta. Sheikh Auwal bai bi ta kan kukan nata ba ya ce "Maza ki hau sama ki kira min Akhiee, sannan ki bi duk ajujuwan makarantar nan ki tattaro min duk Malaman cikinta ina bu atarsu a yanzu!" Da kyar ta aga afarta wadda ke faman kakkarwa ta nufi hanyar fita, ta na fita kukan da take dannewa ya samu nasarar kufce mata, shi kenan yau Akhiee ya mutu abinda zuciyarta ke issima mata kenan don haka kukan nata ke ara arfi. Duk ajin da ta yi katari da shi sai ta shiga ta kira malamin cikinsa sannan ta wuce har ta hau sama.... Tsaye yake hannunsa dafe da arfen kariya na bene... SHARE DOMIN ALLAH Paid Book ne....... *INDO* [8/12, 4:55 PM] INDO: * SAHUN KEKE Ep 3
Chapter 2 · 0% Book details