← Book details Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 47

Sashe 21

Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

ta bu e musu, Ma'u kuwa ta na gefe ta ha e kai da guiwa tsirit da ita. Hajiya Laure ta ce "Boka ana ya takura mini akan hakan, ban san ya zan yi masa ba." Barore ya yi dariya sannan ya ce "Za mu rufe masa baki, ba zai ara hanaki yin abinda ki ke so ba" ta ji da in hakan ta yi masa godiya kana su ka mi e, yau ma kwana uku ya basu su dawo. Ma'u dai da kyar da kyar take iya tafiya, duk ta zama kamar sokuwa ba um ba um-um, su Hajiya Laure ma yamarta su ke ji da sun kalleta sai su tsartar da yawu su yatsine fuska, da haka har su ka dawo gida. Hajiya Laure ta yi Sa'a da su ka shigo gidan duk ba kowa a kusa don haka ta yi sauri ta balbale Ma'u da masifa akan ta je ta yi wanka ta dawo daidai, cikin yanayinta me kama da sokunta ta aiwatar da abinda Hajiya Laure ta ce. Ba laifi ta an dawo hayyacinta sai dai tana nan sukuti da ita. Husnee na kwance kan gado ta na malelekuwa kamar yadda ta saba don kwanan nan aikinta kenan, Mommy ce ta wala mata kira, ta amsa cikin muryarta da ta gama dashewa, Mommy ta ce "Zaman aki da kwanciyar nan naki ya isheni ya ishi kakata INDO ba dole cuta ta i warkewa ba ki na famar kwanciyar kamar an malele? anyi allura ansha maganin amma abu ya ci tira, fito ni ki tayani girki ko kya ji warin jikinki." Da kyar ta iya amsawa da "to" sannan ta yun ura ta tashi ta na bibango sabida wani an jiri-jiri da ke ibarta. Ta na fitowa daga akin daidai lokacin ullin asirin Boka Barore ya nufota gadan-gadan, iris ya rage ya fa a mata Razia ta fa o kanta da arfin gaske hakan ya sa ta walla ihu gami da fa uwa gefe ragab, a take ta sassan are kamar gawar sababi. tsafin Boka Barore kuwa ya fa asa ya one urmus tuni ya bi iska ya san inda dare ya yi masa. Hankali a matu ar tashe Mommy ta yo kanta ta na kiran sunanta, ta na ta ata ta ji ta sandare komai na jikinta ya dena aiki sai zuciyarta ce kawai ke bugawa, Addu'o'i ta fara jerowa ta na tofa mata nan fa hankalinta ya ara ololuwa wajen tashi ganin Husnee ta fara kananna ewa ta na wani irin lan washewa kamar jikin tsutsa gareta, ma'ana dai tamkar ba ashi a jikinta. Mommy ta fashe da kuka ta na ara karanto addu'o'i gami da janyota jikinta ta rungume ta na arin hanata lan washewar sai dai kash abin ya ci tira. ebi kusan minti shidda cikin wannan halin sannan kuma jikin nata ya dawo daidai ya wani saki lakaf kamar gawar da ta samu ziyarta lahira yanzu. wani azababben kuka ta saki ta na cewa "Mommy zan mutu kaina zai fashe wayyo Allah na" jin haka ya sa Mommy ta ara rungumota ta na cewa "Ki yi ha uri Husna ai cuta ba mutuwa ba ce, ki yi ta addu'a za ki samu lafiya in sha Allahu." inaa kukanta kawai ta ke yi ba ji ba gani don ko fahimtar inda Mommyn ta dosa ba ta yi ba bare ma ta yi addu'ar, su na nan zaune Mommy na Kuka Husnee na yi har wani lokacin kafin ta saki kai ta kama ciki ta na kukan cikinta na ciwo, ita dai Mommy ta ga tashin hankali, Ayatul Kursiyyu gami da Suratul Ba arah da sauransu take karantowa in ta saki wancan sai ta kama waccan gabaki aya ta burkice. Ta na cikin haka ta ji wani hucin zafi ya bugeta itama ta zame ta kwanta a wajen a sume. Russlan ne ya yi dirar mikiya a wajen ko asa bai sauka ba ya fizge Razia daga jikin Husnee su ka yi sama, nan take Husnee ta ji kamar cirar aya sai dai ko yatsanta ta kasa motsawa ji take kamar an daddatsa ta da adda, idanunta ma kansu sun yi mata nauyin da ko bu e su ta kasa yi, Mommy kuwa itama ta na kwance a sumenta ba me tashin wani tsakaninsu. Su na cikin wannan halin Muneeb ya shigo fakam-fakam tare da sallama bai bari an amsa ba ya ci gaba da cewa "Mommy kin ganni da wuri yau fita zan yi." da yake hanyar ban akin tsakar gida ya nufa sam bai lura da su ba sai da ya le a ban akin ya fito da nufin ajiye wayoyi da tarkacen jikinsa kafin ya shiga wankan, nan fa idanunsa su ka yi alaragab da su a sheme. cikin hanzari ya yi kansu ya na tambayar lafiya. Ya na ta a Mommy ya ji ta a sume zuciyarsa ta bada rimm!! idanunsa ya kai kan Husnee da take zubda wallar wahala ita ma ar siriri take bin gefen idanunta, hankali tashe ya ce "Ke Husnee lafiya??" ba za ta iya magana ba don haka bai samu amsa ba. Ruwa ya lalubo ya yayyafawa Mommy ai kuwa ta ja wani gwauron numfashi ta sauke ajiyar Zuciya sai kuma ta ci gaba da kuka ta na cewa "Ina Husna, kar dai sun auke mini ita" cike da mamaki da tsoro Muneeb ya ce "Me ya faru Mommy?? su waye za su auketa??" ba tare da ta dena kukan ba ta ce "Yauwa gwara da ka dawo, ashe da gaske Aljanu sun hau Husnee kar ka ga irin wahalar da su ka bata" ta yi maganar ta na arin tashi zaune, temaka mata ya yi ta Zauna, ganin Husnee kwance a kusa da ita ya sa farin ciki ya kamata, goge hawayen ta fara yi ta na cewa "Kalleta nan kar ka ga yadda su ka dinga cukurku a ta kamar ba mutum ba." sunanta ya kira ya na shafa gefen fuskarta cikin tausayawa, a hankali ta bu e ido ta na kallonsa sai kuma ta are baki ta kama kuka ta na cewa "Jikina ciwo ya ke yi ji nake kamar zan mutu!" ya ce ''Sannu kin ji, Allah i sauwa e ki dena cewa za ki mutu ai mutuwa sai lokacinta ya yi." Mommy ta ce " auketa ka mayar da ita aki, laifina ne ni nace ta fito." ta fa a ta na goge hawaye. Rungumarta ya yi ya kaita aki ya kwantar ya na ara jaddada mata sannu. SHARE FISABILILLAH Na Ku i ne.... Nomarl Grp 300 Posting ba kullum ba. VIP 500 Posting Kullum. domin arin bayani 09079885632 AN FARA PAYMENT INDO* [8/21, 11:31 PM] INDO: * SAHUN KEKE Ep 15
Chapter 21 · 0% Book details