← Book details Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 47

Sashe 1

Sawun Keke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry WordDocument 0Table Data [8/12, 4:55 PM] INDO: * SAHUN KEKE Ep 1 NA Ayeesha Abdulkareem INDO Marubuciyar.... DOGON YARO TAJMAHAAL IDO HU WATA HANYA A JINI AAMINAT (Bazawara) da sauransu... 4/8/2023 *Mikiya Writer's Association* Bismillahirrahmanirrahim Garin Kano Misalin arfe 03:00am.... Dare mahutar bawa,, a duk lokacin da dare ya tsala sahu kan auke kowane an Adam ya killace kansa a makwancinsa domin samawa ruhinsa salama. a wannan dare yayin da Asbahi ke shirin aratowa daidai lokacin hadari ya fara gangami, cikin lokaci ani ya gama ha owa ya fara sakin iska me arfi gami da wal iya me tsananin haske ya na wani irin rugugi kamar zai ci babu. auki lokaci cikin wannan yanayin kafin ya saki ruwa me arfin gaske. Sai da aka kira Sallar Asbahi sannan ruwan ya tsagaita ya koma yaf-yaf a hankali a hankali, ba shi ya tsaya cak ba sai da gari ya fara haske. mamakon ruwan da aka sha ya haddasa lullumi gami da wani irin sanyi me matu ar da kasancewar safiyar Lahadi ce ya sa titina har ma da cikin unguwanni babu yalwar jama'a kowa ya nabba'a a gida, tin daga kan an makaranta har an kasuwa, tsirarun mutane ne kurum ke yawo sai ababen hawa na haya su ma ba su gama fitowa ba, domin kuwa yadda asa ta sha ruwa ta ji u ga sanyi na ratsa jikkuna ba kowa ne zai so fitowa a irin wannan lokacin ba. HOTORO Hajiya Laure ce zaune kan aya daga cikin ha un kujerun Falon, ta har afa ta na danne-dannen waya fuskarta ba alamar walwala, ta ha e cikin leshi inkin Buba ta doka aurin ture ka ga tsiya, adon nata ya ara fito da asalin suffarta ta Hajiyoyi, Jiran shigowar Alhaji Salisu kawai ta ke yi don ta sauke masa buhun masifar da ta kwana ta na issimawa akansa. Yazeed ne ya shigo falon ya na tafe ya na jan afa zagaraf-zagaraf bai bi ta kanta ba ya saita hanyar bedroom insa, cike da takaici ta ce "Ai ko ba za ka gaishe ni ba ya kamata ka fa a min inda ka je." fasa wucewa bedroom in nasa ya yi ya dawo kusa da ita ya zauna idanunsa asa- asa ya ce "Why are u doing this to me?? you're my mother fa kin fi kowa sanin ba yaro bane ni Mummy, maganar gaskiya kin fiye kishi da ni" tsaki ta doka kafin ta ce "Ubanka ne ya lalata ka ba wani ba, na san ba zai wuce daga biye-biyen an mata ka ke ba, inda zan yi kishi da kai kuma ai ba zan ma haifeka ba yaro, kawai don ba ka son gaskiya ne." e baki ya an yi cikin ko in kula ya ce "Ina Daddy?" a masife Hajiya Laure ta ce "Ka ban ajiyarsa ne?? tin jiya ya yi min al awarin zai dawo ya same ni amma ya i dawowa." "Wani gurin ya je??" ''To ai in wani gurin ya je ma da auna, ya na sashinsa, wai wani ba o zai yi za su tattauna shine har da ce min kar in sake in zo sashinsa har sai ya dawo ya same ni, to ka ga da bai iya cika al awari ba ya i dawowa, sai ka tashi ka je gurin nasa tinda dama ai shi ka ai ya haifeka ni ar karere ce, idan ka je kace masa ya fito ina jiransa." Dariya Yazeed ya yi gami da cewa "Gaskiya kina da yawan fa a Mum, ki dinga ha uri mana Daddy fa ya na da aiyuka sosai ki dinga yi masa uzuri, kuma ba na so in ji ki na cewa ba na martaba ki innan Please Mum, martaba ki ya zama dole bayan ke ba ni da wata." ta e baki ta yi ta juya masa eya alamar ba ta gamsu ba. Tashi ya yi ya wuce sashin Daddy ya na jiyo Hajiya Laure na mita shi kam sai dariya yake don abin nata dariya yake ba shi. an madai-daicin Parlor ne wanda ya ji kayan Alatu na more rayuwa, an zuba ku i wajen tsara shi da awata shi komai ya ji banda tsiya inji maro Banda sanyin AC gami da amshi ba abinda yake tashi. a tunanin Yazeed ya na shiga zai tarar da Daddynsa a Falon ya na karatun Jarida kamar yadda ya saba don haka ya fara cewa "Dad!!! ka na ina? ka shirya fa a da Mum don kuwa ta yi fus........" maganar tasa ce ta ma ale a ma oshinsa, cikin zazzaro ido ya ke kallon jini da ke kwance malala har ya gangaro ashin Kujera ya fito kasancewar saitin kujerun a tsakiya suke. cikin tsananin firgici ya zagaya don ganewa idonsa abinda ke zubda irin wannan jinin haka. Ihu ya kurma gami da yin tsalle ya yi baya idanunsa kamar za su fa asa sabida zaro su da yayi, dandanan jikinsa ya auki wata irin tsuma, zuffa ya shiga karyo masa duk da irin sanyin AC da sanyin gari da su ke ka awa. Baya-baya ya fara yi ya na cewa "No!! wallahi ba dai Daddyna ba, lallai yau na tabbata Jaki, naje na sha giya ta zo tana nuna min Daddy cikin jini haka? Impossible! dole ma in dena shaye-shaye!!" maganar yake cikin fitar haiyaci don kuwa tashin da hankalinsa ya yi ya wuce mizani. Da gudu ya juya ya koma Parlo ya na wallawa Mummy kira, gabanta ne ya yanke ya fa i Rimmmm!!!!!!! ta yi saurin tashi ta na cewa "Me ya faru??" Yazeed ya na haki ya ce "Daddyyy!!! zo mu je ki gani, na fara haukacewa!!." ya arasa maganar ya na jan hannunta, cikin sauri gami da sassarfa ta bi bayansa su ka koma Falon Alhaji Salisu. Sai da ya danganata da gawar Alhaji Salisu sannan ya saki hannun nata ya koma baya ya ri ugu ya na jiran ta ce masa ai giya ta sa ya fara gane-gane. ya na kwance cikin jini ko ina a jikinsa raunin wu a ne faca-faca anyi masa wani mugun kisan gilla wanda ko Dabba mutum ya ga anyiwa dole hankalinsa ya tashi bare Mutum an uwansa. Hilis Share Mutanena an Amana Paid Book ne..... 09079885632 INDO [8/12, 4:55 PM] INDO: * SAHUN KEKE Ep 2 NA Ayeesha Abdulkareem INDO *Mikiya Writer's Association Ihu da kururuwa Hajiya Laure ta fara yi, ba ta bi takan Yazeed ba ta fice ta na ihun neman auki. Yazeed kuwa jin haka ya tabbatar masa ba gane-gane ya fara yi ba da gaske Daddynsa ne aka kashe, ja ar ya zauna a asa dafa'an murar kwa i, gami da fashewa da kuka kamar aramin Yaro ya na cewa "Wallahi ko waye ya kashe min Daddy sai na kashe shi ba zan ta yale shi ba." abubuwan da ya ke ta fa a ya na maimaitawa kenan. Hajiya Laure kuwa ta na fita harabar gidan me gadi ya taso da sauri ya na tambayarta, cike da masifa ta ce "Maza-maza kira min an-sanda wallahi ba zan yarda ba duk wanda ya aikata da me hannu a ciki sai na yi shari'a da shi kuma sai na sa an kashe shi, maza ka kira min su!!." ta arasa maganar cikin tsawa, jiki na tsuma Tala ya ce "Hajiya ai bansan me zan ce musu ba ne" Kamar za ta cinye shi da masifa ta hayayya o masa ta na cewa "Ka ce musu Alhaji Salisu aka kashe, su yi sauri su zo tin kafin wanda ya aikata ya bar garin su kama shi don wallahi ba zan yale ba ko uban waye shi." Jin furucin kisan Alhaji ya ara aga hankalin Tala me Gadi, cikin rawar murya ya ce "To Hajiya ku na da lambar an-sandan??" tasssss ta wanke shi da wani lafiyayyen mari, jikinta ya auki tsuma sai huci take sabida acin rai gami da tashin hankali da su ka yi karo da juna a cikin Zuciyarta. "In banda kai an iska ne? a kashe Alhajin shine za ka zauna ka na tambayata lambar Police Dan Ubanka? kai ba za ka iya zuwa da kanka ka nemo su ba? Ba akwai mukullin mashin in da nake aikenka a wajenka ba??" Ta yi maganar ta na huci kamar bujimin Sa. Tala Me Gadi ya na jin haka ya juya akinsa da gudu, ba da ewa ya akko mukullin ba tare da ya dawo gurin Hajiya Laure ba ya zabari mashin ya fice kamar ya tintsira sabida sauri. Har su ka dawo tare da an Sanda Hajiya Laure tana harabar gidan ta na zagaye, daga ta kai mari sai ta kai gwauro, sai surutai ta ke yi tamkar sabuwar mahaukaciya. Ta na ganin an Sandan ta yo kansu ta na cewa "Wai kamar ni za a kashewa Miji?? Alhaji Salisun za a kashe?? shekararmu kusan Talatin da Aure amma yau aya a kashe min shi? Inspector lallai ka kama kowaye ya aikata sannan ka tabbatar an hukunta shi, wallahi ko me ka ke so zan baka, kai ko duka dukiyar da Alhaji ya bari ce zan baka ni ban damu da cin gadon dukiyarsa ba kawai Fansar Ruhinsa nake bu ata!!!." Inspector Khalil ya jinjina kai kana ya ce "Mu je ki raka mu inda abin ya faru." kafin ya rufe baki ta juya ta na cewa "Ku tawo." Bin bayanta su ka yi zuwa Falon Alhaji Salisu, har lokacin Yazeed ya na gurin ya na arza kuka tare da fa in sai ya au Fansa. Har an Sanda su ka gama bincike-bincikensu su ka yiwa Hajiya Laure da Yazeed da Tala tambayoyi ba abinda su ka fuskanta game da kisan, illa iyaka sun shaida wanda ya yi kisan ba aramin makashi bane don kuwa ba wata alama da ya bari wadda za ta nuna cewar shi ne. Gawar Alhaji Salisu an Sanda su ka auka zuwa Asibiti, wurin ya rage daga Inspector Khalil sai Constable Saleh sai Hajiya Laure da Tala. Har zuwa lokacin ro onsa take kamar ta yi masa sijjada akan ya nemo mata wanda ya kashe mata miji. Cikin salonsa na iyayi da kwainane ya ce "Kar ki damu Hajiya ai hakan aikina ne, yanzu kamata ta yi mu je Asibitin mu
Chapter 1 · 0% Book details