← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 92

Sashe 88

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon ta Afeefah tayi cewa "Deejarh gyara na saka miki belt domin kuwa naga alamar baki iya ba."

_-_masu karatu shin kuwa ko kun san bakin surutun Deejarh ya mutu kuwa?_-_🤣😂😅

Dan haka ba tace komai ba, ta gyara sannan Afeefah ta gyara ma ta saka belt É—in, kana ta koma ta zauna.

To abin dai haka yake domin kuwa koda Jirgi zai tashi ƙara ƙanƙame Afeefah Deejarh tayi, harda hawaye wai tsoro take ji, Lailah kuwa ita da Yasira da suke Bayan su sai Faman dariya suke ma ta.

A haka dai har Jirgin nasu ya ɗaga cikin gajimare yana yawa tawa dasu.🛬

___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙

_-_💓The Nainarh Kd 💓_-_
*The Phone Number*
*08081129487*
*The Acct Number*
*8081129487*
*The Bank Name*
*Palmpay Bank*
*The Acct Name*
*Khadeejarth Sabi'u Yahyah*

*Sister wannan ne ƙarshen Book 1 kiyi sauri kiyi Payment 300 only kafin lokaci ya ƙure fa🙄, ta waɗancan bayanan na sama 🖕🖕 zaki turo 300 kawai 🤗*

*Ƴar uwa kar fa ki tsaya har sai an baki labari, 🥳 Tohm 😇*

*£nd Of Takun Farko*

Page*101&105*

~Last Free Page's~😸

*And*

🔚σϝ ϝιɾʂƚ ɱιԃԃʅҽ🔚

Zaune take saman ɗaya daga cikin kujerun Dining da aka ƙawata kitchen ɗin dasu. Yayin da take cin breakfast ɗin ta wanda kaiwa da komowa a cikin gidan Bai Bari ta samu taci ba sai Yanzu.

Hannunta kuwa wayarta ne yayinda gaba É—aya hankalinta yake akan wayar nata tana karanta littafin Mrs Aysib mai suna ZAN JIRA KA.

Message ne ya shigo wayar nata hakan ne yasa ta fita daga whatsApp da take ciki sannan ta buÉ—e, message da taga lambar Afeefah ne.

Waro ido tayi cike da mamaki tana tunanin anya kuwa ita ce, bawai mistake Afeefah tayi ba, idan ba haka ba mai zai sa Afeefah ta turo ma ta har 500k.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta buÉ—e message na farko da Afeefah É—in ta haÉ—o ma ta dashi kamar haka.

"Hi, Ummi ga waɗannan kuɗaɗen nasan dai ba zaki rasa hidimar da zakiyi dasu ba, please bana son ki watsa min ƙasa a ido wurin cewa a'a, Afeefah ce."

Wani murmushin jindaÉ—i Ummi tayi a fili take faÉ—in

"Aikuwa Afeefah nagode sosai, kamar kuwa kin san kuÉ—i nake nema ruwa a jallo."

Cikin sauri ta lalubo lambar ƙanwar ta Ummu Salma, tana ɗagawa ba tare da Ummi ta jira tayi wata magana ba ta ce

"Ummu Salma, Allah ya Rufa mana asiri Yanzun nan wata budurwar da nake aiki a gidan su ta turomin da 500k, saboda haka yanzun nan ba anjima ba, ki turomin lambar account naki domin na taro miki kuɗaɗen saboda a samu ayi ma Ummu Shaheedah aikin ƙarin da ya fito ma ta kinji ummu Salma?.
Yanzun nan fa zaki turomin."

Ajiyar zuciya ta ɗayan ɓangaren wacca Ummi ta kira da Ummu Salma ta sauke sannan ta amsa da faɗin

"Toh Auntie Ummi amma please ba dai roƙonta kika yi ba koh?."

Ɗan murmushi Ummi tayi tana bawa ƙanwar nata amsa da cewa

"A'a ko ɗaya ban roƙeta ba, ha sali ma ko faɗa ma ta ina cikin matsalar kuɗi, banyi ba, kawai dai ina zaune naga anyi min alert na 500k, Yanzu dai ya jikin ita Ummu Shaheedah ɗin ne?."

Ummi ta tambaya domin kawar da wancan maganar.

Kallon ƙanwar tasu, dake kwance saman gado irin na marasa lafiya, Ummu Salma tayi ta ɓangaren ta sannan ta bata amsa da faɗin

"Lafiya Alhamdulillah Yanzu ma ta sama Bacci ne, kuma ita Oumm Sun tafi Gida, domin suyi wanka ita dasu Uzair da Usman Sai kuma Ummu Shahuda da tazo duba lafiyar Ummu Shaheedah É—in."

"Okay,👌

Haka ake so yanzu Abin da nakeso dake, kiyi sauri ki turomin lambar account É—in naki kinji ko?."

Cewar Ummi sannan ta kashe wayar bayan Ummu Salma ta amsa ma ta.

Ajiyar zuciya ta kuma saukewa tana tunanin Ahalinta da irin Halin da Suke ciki.
A gaskiya ba ƙaramin taimakon ta Afeefah tayi ba, wannan turo ma ta kuɗin da tayi. Sai taji ta kuma ba Afeefah wani muhimmanci a Rayuwa.

BuÉ—e É—ayan message É—in da Afeefah ta haÉ—o ma ta dashi, tayi sannan ta fara karanta.

"Assalamu Alaikum, Ummi Ni ce feefah mai kyau, please kai tsaye maganar dama ita ce ki daure kiyi tunani akan Yaya mah'fuz ɗina, domin kuwa ƙaunar ki yake yi da gaskiya, shiyasa ma kika ga Yana miki wannan kallon ɗazun nan, please karki masa wani mummunar fahimta domin kuwa Yaya mah'fuz mutumin kirki ne shi, zai riƙe da amana Bayan Aure, saboda Haka ki daure kiyi tunani kafin nanda two days zamu dawo daga kano State, sai ki faɗamin abin da kika yanke, kinga ae sai ah haɗa bikin naku kawai dana Yaya Maleek shida Husnee.
Idan kina buƙatar lambar wayansa ba saikin nemeni ba, domin kuwa ga lambar nan ta ƙasa. Good Luck, Feefah Mai Kyau ce. Bye bye."😇

Ta karanta wannan message yafi sau goma, tana ƙarawa da dai ta gaji ne, ta tsaya dan kanta.

Murmushi tayi sannan a fili take faÉ—in "Afeefah ke nan Æ´ar Gidan Babanta. Yanzu haka ake rubuto kalaman huÉ—ubar saurayi a garin ku Abuja?. Wannan saiki saka naji ya gundureni fa."

Murmushin ta kuma saki tuno drama ɗin ta dashi na Safe, a lokacin sai da Auntie Yusra matar uncle Yusuf da ta ƙariso wurin ta tarar da abin da ke faruwa, ta saka Baki sannan ya haqura Yaci abincin.

"Ikon Allah shi kuma irin na shi salon ƙaunar ke nan?, amma fah hakan ya tafi da Ummu Sulaym highly highly, ae Afeefah Mai Kyau, karki damu ranki, domin kuwa tuni mah'fuz Ya yi nisa cikin heart na Ummu Sulaym tun kallon Farko Ya sace heart ɗina." 👩‍❤️‍👨💃

*KANO STATE*

Misalin ƙarfe 2:00 na rana Jirgin su Ya yi Landing a babban Filin Saukar Jirgin sama na garin Kano.

Aikuwa batare da da ɓata lokaci ba, gaba ɗaya suka shishshiga motocin Gidan Uncle Sagir, da Yazo ɗaukarsu shida kansa.
Nan suka Bar Filin Saukar Jirgin suka nufi Katafaren Gidan Uncle Sagir dake nan New Life Kano State.

Da Isar su Katafaren Gidan na Uncle Sagir Sameer Lamiɗo. Nan securities da Suke tsaron ƙaton wagameman gate na gidan Suka buɗe musu gate ɗin cikin sauri.

A Jere sannan kuma a tare tsadaddun motocin guda Bakwai suka yi parking a wangameman Filin ajiye motoci dake Katafaren Gidan.

Sannan gaba ɗaya Suka fiffito a tare, to da yake tare da matar Gidan Suke shiyasa basu tsaya ɓata Lokaci ba.

Gaba ɗaya suka nufa cikin Ainihin Gidan, da Shigar su Katafaren daular duniya ƙaton palon Gidan Uncle Sagir. Wanda yasha ya gaji da shan kayan Mo re Rayuwa Ba'a magana, gaba ɗayan su zama su kayi saman Royal sofa's da aka ƙawata ƙaton palon dasu.

Yayin da mutanen gaba ɗaya waɗanda akazo dasu tun daga kan Mah'eesha, Haseeya, da kuma mahaifiyar su Auntie Suwaiba suka shiga kitchen domin Bawa masu aiki umarnin haɗa lunch Wanda Baƙi zasu ci. Yayinda mah'fuz shi da Yasir ɗan Uncle Yusuf kuwa ko tsayawa a Palon basu yi ba. Kai tsaye ɓangaren mazan Gidan suka wuce domin sauke gajiya.😘

Shima dai Uncle Yusuf da shigowar sa Gidan tuni ɓangaren da Amma wato Hajiya Raheemah take ya nufa tare da Uncle Sagir domin gaisheta da kuma duba lafiyar ta.

Sai ya kasance gaba É—aya mutanen palon su Afeefah ne da kuma yaran Uncle Yusuf ma ta sai kuma Auntie Yusra matar sa da tabi Auntie Suwaiba kitchen domin tayata wasu ayyukan.

Tunda suka shigo wannan Katafaren Gidan har ƙuka ƙariso palon Suka zazzauna Deejarh tana maƙale da Afeefah. Yayin da take ƙarewa ƙaton palon wanda komai Ya yi zam zam domin kuwa ba ƙaramin kuɗaɗe aka zuba ba, sai dai kuma ita haryanzu bai kai kyan Gidan Mister mai kyau ba, mahaifin su Afeefah ba a wurinta, domin kuwa shi wannan Gidan part's part's ne da yawa gare shi. Tundaga kan na yara ma ta da kuma na maza sai kuma na Amma sai kuma na Uncle Sagir sai wannan wanda Suke ciki da ya kasance na Auntie Suwaiba matar Uncle Sagir.
Yayin da shi kuma Gidan su Afeefah a haÉ—e ginin yake kuma a tsare yake.

Kallon Afeefah Deejarh tayi sannan ta raÉ—a Mata magana a kunne Muryar ta rawa.

Da sauri Afeefah ta kalle ta, amma bata ce komai ba, ita kuma Deejarh ta Ma ta alama da ido, wai zata fita, miƙefwa Afeefah tayi sannan ta kamo hannun Deejarh suka bar palon.

Sai da suka fita daga palon sannan Afeefah ta saki hannun Deejarh da ta riƙe, kallon ta tayi tana faɗin

"Da gaske kike yi wai?."

Tayi maganar tana ƙarewa Deejarh ɗin kallo, ko zataga alama.
Rau Rau Deejarh tayi da idanunta kamar zatayi kuka ta ce

"Allah Balarabiyar India haka kawai naji jikina kamar Ruwa yana tsiyaya. Nifa tsoro nake ji ƙilama saboda nahau Jirgine, shiyasa nake zubar da jini ta da yawa kuma."

Ta ƙarishe maganar tana shirin fashewa da kuka.

Ganin Haka yasa Afeefah ta kamo hannunta sannan suka nufa wani ɓangare daban ba wanda suka fito daga ciki ba.

Kwankwasa ƙofar palon da suka tsaya gaban sa, Afeefah tayi sannan kuma har lokacin hannunta yana cikin na Deejarh wacca gaba ɗaya ta gama tsurewa, saboda tsoron wani Abu kamar Ruwa da take ji yana ma ta Yawo a jiki. 😲

Wata kyakyawar Budurwa ce ta buɗe musu ƙofar palon, jikin ta sanye da kayan bacci, da alama daga Baccin ta farka.
Ganin Afeefah tsaye yasa budurwar sakin ihun murna sannan ta ƙarisa da sauri ta Rungumo Afeefah tana faɗin

"Feefah mai kyau kece, Yaushe ku ka zo, ah ah ina su Haseeya da Mah'eesha ɗin ne, waima ya ya banji ƙarar shigowar motocin ku ba, saida fah na faɗa wa Dad idan zai tafi Airport ɗauko ku yayi min magana shi ne yaƙi ko?."

Budurwar ta ƙarishe maganar cike da Rashin jindaɗin ɗaukosu Afeefah da bata sama Damar yi ba.

"Oh My Auntie Hameeda zaki ɓallani fah."

Afeefah tayi maganar cikin murmushi, ita ma Hameeda murmushi tayi sannan ta saki Afeefah daga Rungumar da tayi ma ta tana kallon Deejarh, cikin murmushi ta ce

"Feefah wannan kyakyawar fa, daga ina kuka samo ta?."
Chapter 88 · 0% Book details