← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 92

Sashe 62

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da suka kwashe tsawon sati ɗaya suna zuwa duba lafiyar Hajarah, zuwa lokacin taji sauƙi sosai, sannan kuma ba ƙaramin shaƙuwa bace ta shiga tsakanin ta da family ɗin Abubakar Mai Kyau dashi kansa dama matarsa Rafi'at, ai ba'a ma maganar Yara su Abdulmaleek domin kuwa wata kalar shaƙuwa ta ban mamaki tayi da Yaran a sati ɗaya kacal.

Zuwa lokacin kuma Abubakar ya gama binkcike akan Hajarah ya gano cewar.
Ita ɗin Ɗalibar psychology ce a wata University dake a nan Abujan, sannan kuma ta kammala karatun gaba ɗaya a Ranar murnar kammala karatun nasu ne ma, bayan an gama, kowa ya watse ita ma tana hanyar ta komawa gidan da take zaune da yake ba'a hostel take zaune ba, shi ne fa wannan hatsari ya auku da ita, Motar da take ciki wasu Ƴan fashi suka tare, ta fito a domin ta gudu wata mota ta bigeta shikuma mai mota yaji tsoron kota mutu ne shi ne ya gudu bai taimaketa ba, shi ne fa su Abubakar suka tsince ta a wurin da abun ya faru hadda jini a jikinta that is all.

To koda Abubakar ya tambaya Hajarah abin da ya faru, anyi sa'a bata manta komai ba, ita ma dai haka ta faÉ—a masa, a lokacin Rafi'at ta tausaya ma ta sosai domin kuwa abin akwai ban tausayi ace mutum ya manta gaba É—aya memory nasa wanda ya faru a tsakanin sa da Ahalin sa daÉ—in daÉ—awa kuma ace hatta sunan State da yake ya manta abin akwai ciwo obaaaaa.

___*_____*

Satin Hajarah biyu a asibiti mutanen Jigawa State, suka diro Abuja sakamakon kiran su da Abubakar ya yi a waya ya faÉ—a musu halin da ake ciki.

Kai tsaye Asibitin da aka kwantar da Hajarah suka wuce suma dai bayan isansu suka kuma tabbatar da abin da Abubakar ya faɗa sun tausaya ma ta sosai, musamman da ya kasance suɗin likitoci ne sun san matsalar abin Especially ma Hajiya Zuwairiya da ya kasance ita ɗin ɓangaren ta karanta wato Brain.

___*

Kwanan su biyu suka juya Jigawa State da Hajarah a bisa shawarar da gaba ɗaya suka yanke na qwara ta koma hannun su da zama, kafin asan abin yi tunda ba za ta iya tuna komai ba, indai ɓangaren da ya shafi Rayuwar ta da family nata ne.

Wannan konawa Jigawa State da zama na Hajarah ba ƙaramin faranta Ran Rafi'at ya yi ba, domin kuwa a da sosai ta damu da inda Hajarah ɗin zata zauna tsoro take kar ta barta a gida ita gata ba mazauniya ba wani abu yazo ya shiga tsakanin ta da mijinta. 🤦

Su kuwa ta ɓangaren Yara ba ƙaramin kewar Auntyn su Hajarah suke ba domin kuwa a ɗan sati biyu da suka yi a tare da ita, shaƙuwa ce sosai ta shiga tsakani domin ko Ranar da su Hajiya Harirah zasu koma Jigawa State da ita ba ƙaramin daru aka sha dasu ba.

Shi kuwa ta ɓangaren Malam mai kyau ni dai Nainarh kd ban ma san abin da zan iya rubutawa da alƙalamina ba, saboda Rayuwar sa ya ci gaba da gudanar wa kamar ko yaushe cike da Nasara ta gefe ɗaya kuma ga Ahalin sa.

Sai dai kuma me?.

Sati É—aya ya wuce, aka zo sati biyu, ita ma ta wuce sai kuma a lokacin Abubakar ya fara jin kewar ta amma dai ya daure, sati É—aya ya kuma wucewa abu ya kuma girmama, aikuwa ba shiri ya kwashi matar sa Rafi'at da Yaransu suka bi jirgin yamma sai Jigawa State a cewar sa ganin gida zasuje, aikuwa anyi murna da Farin cikin zuwan su sosai barinma dai Hajarah da tayi kewar Yaranta kamar yadda take faÉ—a, a lokacin kuma Sagir da matar Suwaiba sun daÉ—e da kammala karatun su, da farko a Rivers State suka fara zama sai kuma daga baya suka koma Kano É—ungurun gun da zama, suma dai sunzo ganin gida da Yaran su biyu a lokacin aikuwa nan aka haÉ—u.
Kwanan su Abubakar uku a Jigawa State suka koma Abuja saboda yanayin aikin su.

***

Rayuwa ta ci gaba da tafiya Yayin da da Abubakar ya tsiri sabon abu duk bayan wata ɗaya ko sati biyu sai ya uzzurawa Rafi'at sun tafi Jigawa State haka take haƙura suje su dawo.
Da dai taga abin nashi bana ƙarewa bane, wata Ranar lahadi da dare da ya same ta da maganar zuwa Jigawa State gobe sai ce masa tayi.

"Ita fa Wallahi wannan zuwa Jigawa ta gaji dashi, wai tukunna mai yake zuwa yi ne da yake uzzurawa sai an tafi?."

A lokacin murmushi Abubakar ya ma ta sannan Yace

"Nan da lokaci kaÉ—an zaki sani ko menene..."
Daga haka kuma ya sha re maganar suka dauko wata.

Washe gari kuma ya same ta da maganar zuwa Jigawa aikuwa kai tsaye ta ce masa "ita da Yaranta ba inda zasu sun yafe."

Rayuwa ta ci-gaba da lulawa yau da daɗi gobe babu yayin da Mister Mai Kyau a duk ƙarshen wata sai yaje Jigawa State abin da bayayi a baya.

___*

A wani zuwa da ya yi ne wata Ranar Saturday mahaifin sa Alhaji sameer Lamiɗo ya yi masa wata tambaya, lokacin da suka kaɗaice a palon Alhajin tambayar da ta saka shi yin murmushin jin kunya yana yin ƙasa da kansa

A lokacin kallon ÆŠan sa Abubakar Alhaji Sameer LamiÉ—o ya yi cike da kulawa sannan ya nisa bayan ya kira sunan Abubakar ya amsa ya ce.

"Wai kuwa nace wannan zuwa da ake mana ba hutu anya ba wani abu ake nema a wurin mu ba kuwa?."

Ya yi maganar mai harshen damo cikin kulawa yana ƙarewa ɗan nasa kallo.

A lokacin ƙasa da kai Abubakar ya yi cike da kunya tabbas maganar Abbhee haka ne daga ƙarshen ƙarshe dai bayan Haleesat Rashid Rayyan yaga wata Ɗiya mace da yaji yana ƙaunar ta fi ye da komai na Rayuwa yana son ta yana ƙaunar ta fi ye da komai idan yace komai tofa koman komai yake nufi.

Ajiyar zuciya ya sauke a karo na ba adadi sannan ya É—ago yana kallon mahaifin su Alhaji Sameer LamiÉ—o kamar yadda shi ma shi É—in yake kallo, ko kafin ya sama zarafin yin magana Alhaji Sameer LamiÉ—o ya riga sa da faÉ—in

"Iyalinka tasan da maganar kuwa?."

ÆŠan waro ido Abubakar ya yi sannan kai tsaye Yace

"A'a bata sani ba, amma dai zata sani nan bada jimawa ba."

Murmushi Alhaji Sameer Lamiɗo ya yi sannan ya kuma cewa ita ɗin ta sa ni kuwa ko kuwa soyayyar ɓangare ɗaya ne?."

"Eh tasani amma dai ta ce wai tana jin kunyar ku, da kuma mata ta."

Abubakar yaba mahaifin nasa amsa Yana dariya ƙasa ƙasa.

Shi ma dai Alhaji Sameer dariyar yake cike da jin daÉ—i domin kuwa ya yaba da Tarbiyar Yarinyar obaaaaa.

Suna cikin haka saiga Hajiya Harirah ta shigo da yake ita keda turaka, ƙarisawa ciki tayi tana faɗin

"Ikon Allah kace zance ya yi daɗi tunda naga ana faman sheƙa dariya."

Kallon matar nasa Alhaji sameer ya yi "Bayan ta sama wuri ta zauna, har yanzu fuskar sa a washe take yace

"To dai ÆŠanki ya sama mata."

"ÆŠana kuma wanne a ciki, kuma wacece matar?."

Tayi tambayar tana binsu da kallon jiran amsa.
"ÆŠan ki dai Abubakar Wanda yake zaune a gaban ki a halin Yanzu shi ne ya sama mata kuma ita É—in ÆŠiyarki ce."

Alhaji sameer ya bata amsar tambayar ta.

Cike da farin ciki fuska washe Hajiya Harirah ta kalla Abubakar sannan ta rangaÉ—a buÉ—a tana faÉ—in

"Aikuwa muna ta yashi murna, sai dai kuma abu É—aya har yanzu ban fahimci wacece matar da ya samu ba fa."

"Toh tunda har yanzu baki fahimta ba kawai kije ki kira mana ÆŠiyarki Hajarah zaki fahimci komai ai."

Cewar Alhaji sameer, aikuwa ba musu ta miƙe ta fi ce daga palon ba'a daɗe ba.

Sai gata ta dawo Hajarah na take ma ta baya, wuri ta samu ta kuma zama ita kuma Hajarah ta zauna a ƙasa daga can gefe, sannan ta kuma gaisar da Alhaji sameer ya amsa cikin kulawa sannan
Ya kalle ta cikin kulawa ya fara magana

"Hajarah ÆŠiyata kinji haka ake yi, kawai sai muji batu waje. Ashe ÆŠiyata tayi miji bamu sani ba."

Ya yi maganar ne cikke da Zoyala.

Qasa da kai Hajarah tayi cike da kunya sai dai bata ce komai ba, ganin haka yasa Alhaji sameer ya ci gaba da cewa

"To Yanzu dai ÆŠiyartawa tana son Yayan nata ko kuwa dai..."

Sai ya yi shiru bai ƙarisa ba.

Tun daga kan shi kanshi da ya yi maganar har Abubakar mai neman Auren 😋 da kuma Hajiya Harirah dake gefen mijinta gaba ɗaya suka mayar da kallon su akan Hajarah suna jiran amsar da zata bada.

Tsuru tayi idanun ta na kallon lallausar carpet da da take zaune akai Yayin da zuciyarta ke tariyo ma ta abubuwan Alkhairi da wannan family mai tarin albarka suka ma ta tun daga kan rescue nata da Abubakar ya yi shi da matar sa, da kuma É—aukota da Alhaji sameer shi da kanshi da kuma iyalansa sukayi daga Abuja zuwa Jigawa State, duk da cewa ta manta da memory nata akan Rayuwar ta da gaba É—aya Ahalinta hatta sunan State da take ba zata iya tunawa ba.

{ kuma dai masu karatu nasan da yawa daga cikin ku zasu ce to me yasa ba'ayi cigiyarta a gidajen Radio ba, to ku sani cewa wancan lokacin ba ɗaya yake da wannan lokacin ba. Yanzu zamani ya sauya ci-gaba yazo sosai, amma kuma wancan lokacin da babanci nesa ba kusa ba🤳 }
**The Nainarh Kd 🔥
Writer 🔥**

Suka ɗaukota daga Abuja suka dawo da ita Jigawa cikin su, suka ci gaba da riƙe ta da gaskiya da amana ba tare da saran zata biyasu da komai ba, wannan shi ne mutun taka ta gaskiya waɗannan Ahali sun kasance masu mutunci.
Ita kuwa idan taƙi Auren Abubakar to ai tayi musu mugun butulci kuwa.
Chapter 62 · 0% Book details