← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 92

Sashe 87

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sannan ta fito chest ɗin ta ɗaure da towel Pink color, ga wani ƙarami tana goge doguwar sumarta, wacca ta zubo ma ta gaba da baya.

Qari sawa tayi gaban Dress mirror sannan taja swivel chair É—n ta zauna tana kallon kanta cikin mirror É—in, murmushi tayi sannan a fili ta furta.

"Feefah Mai Kyau, shalelen Daddyn ta Mister mai kyau, da kuma Yayarta Zaynerb Mai Kyau, sai kuma YaYanta Maleek sannan kuma SARAUNIYAR KYAU ta garin Abuja.

Murmushin farin ciki ta kuma yi, sannan ta fara shafa tsadaddun lotion a jikin ta, bayan ta kammala miƙewa tayi ta ƙarisa can gefen bed, sannan ta ɗauko wani ƙaramin suitcase, kana ta dawo ta zauna akan swivel chair ɗin na Dress mirror sannan ta ɗaura saman mirror kana ta buɗe kid ɗin.

Ɓangarori Biyu ne da kid ɗin, ɓangare ɗaya make-up artist ne kamar su.

•Jagira-concealer-eye shadow-eye liner, gel liner-mascara-foundation-
•Highlighter-contour-Setting powder-finishing-powder-Lipstick, JamBaki and
•Lip glows-moisturizer, primer da kuma make-up setting spray-Blush-Brushes set
•Eye Lashes-Brow gel-Shimmer_Beauty blender spong {BBS}.

Yayin da ɓangare na biyu kuma kayan ado ne na mata ciki _-_jewelry_-_ kamar su.

•Ring-chain-earrings-stud-Necklace-Bracelet-wristwatch-Da sauransu domin kuwa gasunan dai sai wanda ta zaɓa.

Ajiyar zuciya Afeefah ta sauke tana kallon waÉ—annan uban tilin make-up artist and jewelry kamar Hauka, ita fah bata cika son waÉ—annan abubuwan ba. Tafi ganewa Normaly Natural beauty Nata bawai ayi ta shafe shafe ba.

Mayar da kid ɗin gefe guda tayi sannan ta zaɓa waɗanda zata iya amfani dasu, tabar waɗanda ba zata iya ba.

Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta zauna ta tsara heavy light make-up a saman kyakyawar fuskar ta, wanda ba ƙaramin kyau tayi ba, sai ta fito sak Queen ɗin ta 💞👑💞

Miƙewa tayi bayan ta kammala yin kwalliyar sannan ta nufa closet ta zaɓa kalar tufafin da zata saka jikinta.

Nan ma sai da ta kwashe tsawon mintuna goma sannan ta shirya cikin Atamfa Dresses.

Doguwar gown na atamfa wacca aka ma ta É—in kin fitted rigar tayi ma ta Bala'in kyau, musamman ma da ya kasance É—in kin dai dai ita ne. Rigar ta zauna ma ta É—amas.

Dawowa tayi gaban mirror sannan ta tsaya ta tsantsara ɗaurin ta na manyan Gayu. Sannan ta ɗauki earrings ta maƙale a kunnen ta, kana ta saka sarƙar tare da da Bracelet sannan ta ɗauki diamond ring ta saka a yatsarta na ƙarshe sai da ta kammala duka abin da ya kamata tayi, sannan ta ɗauki veil wanda yake Pink and sky purple color, ta riƙe a hannu daya ke gaba ɗaya shigar da tayi shigar Pink and sky purple color ne.
Hatta atamfar jikin ta launin sky purple and Pink color ne, kai komai da komai na jikin ta ma Haka ne, gashi tasha wankan diamond ta ko'ina diamond ke walwali a jikin ta gata Ita ma ɗin kanta Diamond ce guda.💓

Qari sawa tayi wajen doguwar softened stool dake bedroom É—in, sannan ta É—auki handbag nata Ita ma Launin Pink and sky purple color ce.

A taƙaice dai duka wankan jikin ta wankan Pink and sky purple color ne, domin kuwa Afeefah favorite color nata shi ne sky purple color, ita Haka take komai nata ya banbanta dana kowa.😇

Handbag ɗin ta riƙe a Left hand nata Yayin da veil nata shima da bata yafa ba. Yake Riƙe a right hand nata kallon agogon bedroom ɗin Tayi 12:00am ta gani fa.😺

Da sauri ta nufa ƙofar bedroom ɗin, tana faɗi a fili

"Shikenan kuma nasan ma kowa ya shirya ni kaÉ—ai ake ta jira ma."

Fresh hand ɗin ta, ta saka sannan ta buɗe ƙofar bedroom ɗin, aikuwa tamkar ana jiran ta buɗe, nan suka shiga jera ma ta pictures wasu da camera Yayin da wasu kuma da wayoyin hannayensu Suke yi.

Da sauri takai tafin hannunta na dama Wanda Yasha Jan lalle, tana rufe fuskar ta saboda kar hasken Ya yi ma ta illa, sai hakan da tayi ya zama kamar style.

Aikuwa tamkar ta ce ku ci gaba na canza style ne. Haka suka ci gaba da jero ma ta Hotuna gaba ɗaya palon bakajin komai sai ƙaran flash flash jika ke

Tas!, tas Tattas tas tas.🤩

Haka kawai kake ji gaba É—aya palon.

Afeefah dai da taga hotunan ba zasu ƙare ba, Yasa cikin sauri Ita ma ta shige cikin su tana dariya ta ce

"Kai Auntie Nainarh, Mah'eesha YaYa Yasir da YaYa mah'fuz harda ke Lailah Yasmin please ku dena Allah na gaji fa."

Tayi maganar cike da shagwaɓa.

Gaba É—aya dariya suka fashe da ita cike da nishaÉ—i

"Okay Tunda Haka ne, gaba É—aya kawai ku jeru ayi pictures É—in na Ahali kawai."

Cewar Yasir cikin murmushi.

"Mene ae sai dai kuwa idan zaku bari acan Kano ayi, domin kuwa lokaci yaja sosai, duk Shalele ce ta janye mana lokaci."

Gaba É—aya juyawa suka yi domin ganin mai maganar.

Uncle Yusuf ne tsaye shima cikin shirin sa na alfarma, gefan sa Mister Mai Kyau ne shi kuma kamar ko yaushe sanye cikin Business suit Maroon color.

Yasira ce da take ita ma ɗaya daga cikin Yaran Uncle Yusuf ɗin, ta kalla mahaifin nasu cike da shagwaɓa ita ma take cewa .

"Kai Abbhu ae hotuna fa, kawai zamay..."

Tun kafin ta ƙarisa Uncle Yusuf ya katse ta da faɗin

"Okay wato dai kece shagwaɓaɓɓiya ina faɗin lokaci Yaja shi ne zaki kawo wani checking nonsense ko?, shige muje ƴar jakar.🤫 Ko kuwa nayi jifa dake daga nan har mota kuwa."😂

Ya ƙarishe maganar yana ma ta nuni da Hanyar wajen.

Simimi simi Yasira tazo ta wuce ta gaban sa, sannan ta fita daga palon, suma sauran suka mara ma ta baya su Lailah suna ma ta dariya.🤣

Da sauri Afeefah ta kamo hannun Deejarh a lokacin da suke shirin fita daga ƙofar palon tana tambayar ta faɗin.

"Ke Deejarh, Wanene ya miki wannan make-up Haka, sannan kuma ya naga kunyi shiga kala É—aya dasu Auntie Nainarh da Lailah harda ma Zaynerb da Haleesat faÉ—a min gaskiya kinji ko."

Dariya Deejarh tayi tana amsa ma ta da "Auntie Lailah ce tayi min wannan kwalliyar kuma ita ta bani kayan nan na saka mu kayi anko dukkanin mu."

Murmushi kawai Afeefah tayi tasan Halin Lailah tsaf indai ba wani Abu take nema wurin Deejarh ba. Tofa ba zata taɓa ɓata lokacin ta wajen yi ma ta kwalliya ba, amma dai ko miye zasu haɗu da Lailah ɗin sai taji koma menene.

Afeefah tana shirin magana ke nan ta lura da irin kallon da mah'fuz yake ma Ummi da take Yima su Zaynerb Bye, bye.

Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta ƙarisa kusa da shi, ɗan ɗigil-gile tayi sannan ta kai tsayi dai dai nasa kana cikin kunnen sa take raɗa masa.

"Wato dai Yaya mah'fuz ya kamu da love ko, amma fa karka damu indai Ummi ce, niɗin nan Feefah mai kyau, ɗiya wurin Mister mai kyau sannan kuma SARAUNIYAR KYAU ta garin Abuja zan shawo maka kan Ummi domin kuwa muna Bala'in shiri da ita sosai.😇

Qayataccen murmushin jindaÉ—in maganar ta mah'fuz ya saki, sannan ya kalle ta, tana shirin shiga tsadaddiyar mota bayan ta gama faÉ—a masa maganar.
Yace

"Kamar dai me da me kike so, faÉ—a inaji yanzu kiga aiki da cikawa."

Juyowa Afeefah tayi tana murmushi ta ce dashi

"Ɗan ihsani da kuma wannan ring naka, da nace ka bani kaƙi, toh yanzu iya suma, sun isa kawai."

Tana faÉ—in hakan ta buÉ—e Motar ta shige ciki, ita ma Deejarh dake bayanta ta shiga motar tsaleliya da ita.

Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon ring dake hannun sa. Wanda Afeefah ta nace masa ya bata, saboda ring ɗin ba maza ba mata duka ana sakawa. Wancan yaqi bata, amma kuma yau ba gobe ba, zai bata saboda Ummi .😎

BuÉ—e mota shima Ya yi sannan ya shiga ciki.

Gaba É—ayan su shishshiga tsadaddun motocin suka yi sannan as slowly motocin guda shida, suka fice daga gate na gidan, sannan bayan fitarsu gate man ya mayar da gate É—in ya rufe.

A hanya Afeefah tana zaune a motar da ta shiga, gefanta Deejarth ce ita ma tana zaune tsit.

Ƙarar da wayarta tayi alamar shigowar message ne, yasa ta karɓa wayar daga hannun Deejarh da take game, sannan ta duba.

Message É—in daga mah'fuz ne, kuÉ—aÉ—e ya turo ma ta 500K.
Murmushi tayi sannan ita ma kai tsaye batare da ɓata lokaci ba, ta turawa Ummi duka kuɗaɗen tare da message har kaloli byu daga ƙasa, sannan ta Mayar ma da Deejarh wayar, ita kuma ta ci gaba da kallon hanya cikin yanayin mai daɗi.

_-_
Da isar su katafaren filin sauka da Hawan Jirgin sama na Mister Mai Kyau, gaba É—ayan su suka fiffito daga tsala tsalan motocin su na alfarma.

Sannan suka fara tafiya izuwa wurin hawa jirgi, a tare tafiyar nasu ma kaÉ—ai mutum ya gani, sai sun basa sha'awa da burgewa, balle kuma azo ga yanayin shigar alfarma dake jikin ko wannensu ma, Humm abin dai sai wanda ya gani gaskiya, domin kuwa gaba É—aya hankulan kowa da kowa na Airport É—in ne ya dawo kansu.

Kallon kowa yake cike da sha'awa, ga Deejarh ita ma da ta saje dasu kai idan ka ganta ba zaka ce, Yarinyar da ta zo daga ƙauye Bane, wacca ko sati biyu bata cika a Garin Abuja City ba.

Kai idan ka ganta zaka rantse Ɗiyar wani Ambassador ce, ko kuma wani minister ko ɗiyar wani ƙaton ƙusa a ƙasa.☺️

Ba tare da wani ja ko kuma ɓata lokaci ba, gaba ɗaya suka shishshiga cikin Jirgi.

Yayin da Mister mai kyau shi kuma zai bi ɗayan Jirgin nasa izuwa ƙasar Austria domin gudanar da harkokin kasuwancin sa.

Yayin da ita kuma Momy Rafi'at kai tsaye driver zai wuce da ita Katafaren Hospital nata, shi kuma Maleek da ya Rako su driver ya koma dashi Gida domin kuwa bare dashi za'ayi tafiyar Bah.

In Banda zare fararen idanunta tana ƙara ƙanƙame Afeefah sannan kuma tana bin cikin Jirgin da kallon tsoro, babu abin da Deejarh take yi, har suka zauna a first class ita da Afeefah.

Yayin da ita Afeefah take ɓangaren window ita kuma Deejarh take zaune kusa da ita.
Chapter 87 · 0% Book details