← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 92

Sashe 30

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

____💓𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝑸𝒖𝒆𝒆𝒏💓___________________________________________________________________☆☆☆☆☆Ⴆყ☆ƙԋαԃҽҽʝαɾƚԋ☆ʂαႦι'υ☆ყαԋყαԋ

*𝑷𝒂𝒈𝒆 29&30*

'ᴋᴡᴀɴᴀᴋɪ ʙɪʏᴜ ɢᴀʙᴀ'

𝑴𝒂𝒊_𝑲𝒚𝒂𝒖_𝑺𝒄𝒊𝒆𝒏𝒄𝒆_𝑪𝒐𝒍𝒍𝒂𝒈𝒆_𝑺𝒆𝒄𝒐𝒏𝒅𝒂𝒓𝒚_𝑨𝒏𝒅_𝑼𝒏𝒊𝒗𝒆𝒓𝒔𝒊𝒕𝒚💝

Ta furta sunan da taga an rubuta, a saman makarantar, akan laɓɓanta sai kuma ta kalla uniform ɗin dake jikinta skirt pencil iya gwiwa ash color, sai riga white color, sai kuma rigar sanyi a sama maroon color, tana sanye da safa doguwa wanda takai ma ta har gwiwa, ga takalmin ƙafafunta shima ash nd maroon color, mai igiyoyi.

Babu hijjab a jikinta sai dai wata hular saƙa, mai ɗauke da launi ash nd maroon color's, ga sumar kanta mai yawa wanda tasha gyara ya zubo ta bayanta.

Da sauri ta kalla Afeefah da tayi parking a cikin makarantar, tun kafin ta ce wani abu Afeefah ta rigata da faÉ—in.

"Surprised" tana dariya, ita ma Deejarh É—in dariya ta fashe dashi, sannan ta ce.
"Balarabiyar india, wai yaushe kika san inasan makaranta ne?,"
Afeefah tana dariya ta bata amsa da faÉ—in, "a mafarki naji kina faÉ—a wani lokaci, da nazo bedroom É—in ki, naji kina faÉ—in, 'wayyo makaranta ni a sakani a makaranta, kona gudu daga gidannan,"

Fashewa Deejarh tayi da dariya, Afeefah ta ce "koba haka bane?," rufe fuska Deejarh tayi tana dariya, Afeefah ta kuma cewa "shine, ni kuma nace bari nama Daddy magana ya sakaki a school, tun kafin," sai kuma tayi shiru tana murmushi bata ƙarisa ba.

Buɗe back seat tayi ta ciro wata haɗaɗɗiyar backpack ta miƙawa Deejarh.

Da sauri Deejarh ta karɓa tana murmushi ta ce "kai Balarabiyar india kina surprising ɗina highly, yau fa, thank you so much, Allah ya ƙarawa Daddy Mister Mai Kyau ake cewa ko?, to Allah ya ƙarawa dukiya albarka, kuma ta kasance mai amfani, da kuma yawa fiye da cikin duniyar nan💴💶😅

Ba shiri Afeefah tayi dariya tana amsawa da Ameen Ameen dear, hannun Deejarth ɗin ta kamo suka nufa office ɗin principal, Deejarh sai kalla kalle takeyi, na ƙauyanci, don har yanzu abin bai saketa sosai ba.

Kwankwasa glass door É—in office É—in principal É—in Afeefah tayi, daga ciki aka bada umarnin shiga, da sallama suka shiga ciki hannun Deejarh cikin na Afeefah.

Yana Zaune a Royal chair inshi tana juyi dashi, yaba ƙofa baya, saida ya gama shan mulkin shi, sannan ya juya kujerar ta juyo dashi.
Ganin wacca take tsaye tana kallon shi ga wata beautiful Girl kusada ita, yasa ba shiri ya miƙe tsaye.
Gabaɗaya ya da burce, ganin Afeefah wata ƙila bayyi tunanin ita bace, rasa mai zayyi yayi sai kawai ya ɗaga hannun shi dake rawa yayi salute ɗinta 😂

Ƙumshe dariya Deejarh tayi ganin wannan matashin dattijon wanda akalla ya kai shekaru arba'in da biyar yana saluting Afeefah abin gunin ban dariya.

Cikin Rawar jiki da na murya yake faÉ—in, "ah um madam, ah wai kece, dan Allah zazzzauna mana, ga guri ki zauna hajiya madam mai kyau," gabaÉ—aya cikin zare ido da inn ina yayi maganar in violence.

Zama Afeefah tayi a kujera, sannan ita ma Deejarh ta zauna kusada ita.
Sai lokacin shima ya zauna yana goge zufa amma fa na tashin hankali.
Murmushi Afeefah tayi dan ta fahimci abin da yasa yake duk wannan rawar jikin, toh kuwa yayi a banza.

Gyaran murya Afeefah tayi Sannan ta gaisar da shi, yana murmushi ya amsa sannan ya nuna Deejarh yace " ah madam wannan kyakyawar fa, kodai ƙanwar kice?,"

"E, Afeefah ta bashi amsa a taƙaice sannan ta cigaba da cewa "sunanta Khadeejah,"

Sai kuma tayi shiru batasan miye sunan mahaifin Deejarh É—in ba.
Kallon Deejarh tayi dan taji mai zata ce, da sauri Deejarh tace "My name is Khadeejah Abubakar mai kyau."

Da sauri Afeefah ta kalleta sai kuma tayi murmushi ta mayar da kallonta kan principal.
Cikin washe baki yace "aikuwa gashi kuma kuna kama, ita ma É—in kyakyawa kamar ku."

Afeefah ta ci gaba da cewa "na kawota ne yanzu, ya za'ayi za'a ma ta interview ne, sannan a sakata a class É—in da ya kamata da ita ko kuwa?."

Da sauri principal yace "ai duk abin da kikace, shi za'ayi madam,"
Maida kallon shi kan Deejarth yayi yana kuma washe baki yace "Nanah khadeejarthu, makarantar da kika fito a wani class kike?."

ÆŠan jim tayi sai can ta ce "j.s.s two, na kammala, yanzu zan shiga j.s.s Three ne."
Principal yana murmushi ya ce "yauwa Nanah Khadeejarthu, yanzu idan na tambaye ki wasu abubuwa zaki iya bani amsarsu kuwa?."

Deejarth ta ce "in Allah ya yadda."

Principal ya fara "a darasin £nglish, wato Turanci zaki iya faɗamin, How many part of speech?,"

Shiru tayi sai can ta ce "guda Takwas {8} ne,"

"Da £nglish zaki faɗa," cewar principal.

Gyara zaman ta tayi ta ƙara ƙanƙame backpack ɗinta sannan ta ce.

"£ight ne,"

"Good" cewar principal sannan ya kuma cewa "and what and what."

Ta ce

"Noun, Pronoun, Verb, Adverb, Adjective, Conjunction, Interjection, Prepositions,"

"Good, and What is Noun?,"

Gyara zamanta ta kumayi sannan ta ce.

"A Noun is a Name of Anything.,"

Murmushi principal yayi sannan ya cigaba da jefo ma ta tambayoyi akan £nglish language. Tana bashi amsa, wasu tayi daidai wasu kuma, yana ma ta gyara.

"Angama da £nglish saura basic science" cewar principal.
Ya kalla Deejarh yace.

"a darasin basic science, What is digestion ?,"

Yanzu ma saida tayi jim kafin ta fara kwararo masa bayani, wanda yasa Afeefah da ke gefe zaune, ta saki baki tana kallonta cike da mamakin ilmin yarinyar.

"Digestion is the process, by which injested food, material are broken down in to similar particle's."

"Wow, good, and Define what is Brain?,"

Ta ce, "The part inside your head, that controls your thoughts, feelings, and movements."

Haka principal ya ci gaba da jerowa Deejarh tambayoyi daban daban akan subjects kala kala kamar su.

National Value, Agriculture, £conomic, Computer Science, I.r.s, Civic £ducation, £.t.¢.

Daga ƙarshe ya rufe da faɗin, give me the Ten, word's of £nglish.

T@ ¢£!
1.perfect,
2, Dream,
3, Table,
4, Challenge,
5,Get,
6, Offer,
7, School,
8, chair,
9, office,
10, salute🤭😇

Tunda ta fara Afeefah ta saki baki tana kallonta tasha mamaki sosai, da Deejarh ta iya wannan.
Ashe abin ba haka bane da ake ganin wasu mutanen da ke ƙauye ko kuma waɗanda suke zuwa government school ake musu kallon, jahilai, kodai adinga musu wani kallo na dabam abin ba'a zuwa government school bane, maida hankali da kuma jajircewa ne, dan ba wanda ya taɓa yin ilimi yana zaune sai an tashi an zage damtse, an shiga rana sannan da wuya koda daɗi 👍

Amma tana tunanin ko'a haka ita Deejarh É—in tana cikin wa'innan mutanen da ake kira da Geniuses a turance kennan, sannan ita É—in gifted ce.

Murmushi principal yayi yana kallon Deejarh ta burgeshi sosai da hazaƙarta.

"Nice good girl, kin amsa duka tambayoyi sai dai Wanda ba'a rasa ba."

Sannan ya mayar da kallon shi akan Afeefah yana murmushi yace "ta cinye interviewing, duka dan haka za'a sakata a j.s.s.three, she deserved it."

Afeefah tayi murmushi ta ce "okay sir."

Telephone É—in dake ajiye kusada dashi, ya É—auka ya danna wasu lambobi sannan ya kira, cikin harshen turanci yake maganar har ya gama, sannan ya kalla Deejarh yace "Nanah khadeejartu, taso na kaiki class da kaina,"

Murmushi tayi sannan suka miƙe dukansu suka fita a ƙofar office ɗin.
Afeefah ta kalla Deejarh tana faÉ—in, "to Deejarh ayi karatu da kyau, idan an tashe ku, Moses driver zaizo ya É—aukeki kinji,"

"To shikenan babu damuwa," Deejarh ta amsa, sannan Afeefah ta nufi motar ta, Deejarh na É—a ga ma ta hannu.

Kana tabi bayan principal elevator taga ya nufa, ita ma tabi bayan shi suka shiga a tare hawa na uku taga ya danna bayan sun shiga.

Ba'a daÉ—e ba taga É—ofar ta buÉ—e sannan suka kuma fita.

Ita dai nata ido, don sai ƙarema makarantar kallo, takeyi sosai makarantar ta burgeta ga ɗalibai kala kala farare da baƙaƙe hausawa dama waɗanda ba hausawa ba.

Wani haÉ—aÉ—É—en class taga principal É—in ya shiga, kafin ta ankara, da sauri tabi bayan shi sai kuma ta tsaya cak ganin class mai kyau da tsari gashi duka É—aliban ciki basu wuce su ashirin ba kai bama sukai hakan ba.

Gaisar da principal ɗin, taga student's ɗin sunyi bayan sun miƙe, ya amsa musu fuska a tsume kamar bashi ke washe baki yanzu a office ɗin shi ba 😅

Nuna musu Deejarh yayi sannan yace "kunyi sabuwar New comer, kallon Deejarh yayi yace, "gabatar musu da kanki, a matsayin sabuwar É—aliba duk cikin turanci yake maganar.

Ta fahimci wani abu dan haka kallonta ta É—auke daga kanshi, ta mayar kan students na class É—in da suka zuba ma ta ido suna kallo.

Qara Riƙe backpack ɗinta dake bayanta tayi sannan ta fara magana.

"Hello class, am Nanah khadeejah Abubakar mai kyau, am New comer, kamar yadda mai girma principal ya faÉ—a da farko."

Da turanci take maganar tana haÉ—awa da hausa fa.

Ta ci gaba da cewa "am very Gladness to see you, ina fatan zaku karɓeni hannu biyu biyu ko?,"

ÆŠan shiru tayi tana kallonsu, sai kuma ta ce "ina fatan dai Æ´an uwan nawa É—alibai suna fahimtar abin da nake faÉ—a, saboda ni É—in ma Æ´ar koyo ce, ba komai na iya ba."

GabaÉ—ayan su students É—in suka haÉ—a baki wajen faÉ—in "munajin ki, kuma muna fahimtar ki, sannan kuma muma muna masu Farin cikin haÉ—uwa dake kuma muna fatan zaki kasance damu har lokacin da zamuyi Candy."

Dariya Deejarh tayi {Ɗalibai kenan, basu daɗe da shiga j.s.s Three ba amma suna tunanin fita daga school ɗinma gabaɗaya, ae haka muke ɗalibai akwai mu da Buri kala kala 🥰🇳🇬}

Ta ce "Nima haka, ina muku fatan nasara a rayuwa, sannan kuma, ku cinye jarabawar j.s.c.e. hadda ma s.s.c.e. gabaɗaya😇

Dariya sukayi hadda ita, principal yace "yanzu tunda kun gaisa kunsan juna saiki sama guri ki zauna."

"To," ta amsa masa, sannan ta nufi gurin zama, da sauri wata kyakyawar matashiyar budurwa ta ce "baki faÉ—amana wani abu ba."

Lokacin da tayi maganar principal ya fita kuma dama can ba teacher a class É—in.

Deejarh ta tambayeta, "Menene abun?," budurwar tana dariya ta ce "baki faÉ—amana, Menene burinki ba, sister,"
Chapter 30 · 0% Book details