← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 92

Sashe 71

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin ne kuma Abubakar ba kunya ya amso Ɗiyarsa Afeefah a hannun Yusuf da matar sa, amma ita Zaynerb ya barta a Jigawa State a cewar sa ita ma zai karɓe ta amma sai bayan wani lokaci.

Rayuwa ta ci gaba da tafiya tana sauri sosai, Yayin da Abubakar Yake kula da Yarinyar sa Afeefah ko sauro baya bari ya taɓa ta, to a'ina ma sauro zai ganta.🤔

Afeefah ta taso Yarinya ce mai matuƙar kaifin basira da wayau, Sannan kuma sosai take ƙaunar Ƴan uwanta duka kamar yadda suma suke ƙaunar ta musamman ma dai Lailah, amma tsakanin ta da Momy Rafi'at kuwa sai dai kallo daga nesa, ko kuma gaisuwa amma in banda wannan, babu wani abu da yake shiga tsakanin su.

Dhekarunta uku a duniya aka saka su a school ita da Lailah Yayin da suke tafiya tare da sauran Yayyin su Haleesat da Nainarh Nailah sai kuma Abdulmaleek tsakanin ta da YaYarta Zaynerb kuwa duk da cewa ba'a tare suke ba, amma shaƙuwa ce ta musamman mai zaman kanta a tsakanin su, a dalilin kuwa duk a ƙarshen wata Abubakar yake haɗa kan Yaransa suje Jigawa State ziyara wani lokacin Momy Rafi'at tana binsu, amma wani lokacin saboda yanayin aikin ta haƙura take yi, Especially ma da mahaifinta ya gina ma ta asibiti nata na ƙashin kanta sai ya zama bata cika samun lokacin kanta ba.

_****______

Shekarun Afeefah Takwas a duniya Abubakar ya ɗauko Zaynerb daga Jigawa State, ya dawo da ita Abuja cikin Ƴan uwanta.
Rayuwa ta ci gaba da tafiya da yake Zaynerb yarinya ce mai masifar wayau da kaifin tunani shiyasa bata shiri ko kaɗan da Momy Rafi'at, domin kuwa ta fahimci ba ƙaunar su take ba, musamman ma idan ya kasance da mutane a wuri to nan ne fa zata dage ta dinga nuna musu ƙauna ta musamman, amma kuma suna kasancewa daga su sai ita, wahala take basu ba kaɗan ba, domin kuwa tasha ta zane Zaynerb ba sau ɗaya ba kuma ba biyu ba, amma kuma ita Afeefah ko tayi nin yar dukan ta kasawa take yi domin kuwa Zaynerb shiga tsakani take sai dai ita a dake ta amma bata bari ko ƙuda ya taɓa ma ta ƙanwa, wacca take shalele a wurin mahaifin su, Alhaji Abubakar Mai Kyau, sai dai kuma duk da ƙiyayyar da Momy Rafi'at take yi wa su Afeefah da Zaynerb bata taɓa nuna wa a gaban Yaranta ba, ko kuma mijinta cikin taku da tsare gida take abin ta.

A wata Ranar Jumma'a ne Ahalin Alhaji Sameer LamiÉ—o suka tashi da wani mummunar Labari na Rasuwar Alhaji Sameer LamiÉ—o ta farar É—aya cikin dare, wuraren uku na dare ya rasu, Yayin da kafin gari ya waye ita ma matar sa Hajiya Harirah ta ce ga garin ku nan tabi mijinta.

A lokacin ba ƙaramin Tashin Hankali gaba ɗaya Ahalin Alhaji Sameer Lamiɗo suka shiga ba, musamman ma Abubakar domin kuwa zai iya cewa wannan ne mutuwa ta uku da aka taɓa masa waɗanda ba ƙaramin Tashin Hankali ya shiga ba.

A lokacin kuma sai mutuwar masoyiyar sa Haleesat Rashid Rayyan da kuma matar sa Hajarah Ya dawo masa sabo a zuciya.

Gaba É—aya Ahalin basa cikin walwala sakamakon Rasuwar Alhaji Sameer LamiÉ—o, hatta mutanen France, Lagos, Kano, Mai Duguri da Adamawa States dama su Abubakar dake Abuja suka taru a Jigawa State jikin ko wannensu a mugun sanyaye.

Alhaji Sameer LamiÉ—o da matar sa Hajiya Harirah suna da watanni Biyar da Rasuwa zuwa lokacin tuni Dr_Raheemah da Hajiya Zuwairiya suka kammala taka ba.

A lokacin ne kuma suka gaza jurewa suka kasa zama a gidan dama Jigawa State gaba É—aya.
Bayan Raba gadon Alhaji Sameer LamiÉ—on. Mai matuqar Yawan gaske ne da akayi, Dr_raheemah ta tattare ya nata ya nata ta koma Kano da zama wajen Autan ta Sagir da iyalansa.

Yayin da ita kuma Hajiya Zuwairiya ta koma Mai Duguri wajen Yusuf da iyalansa.

____**__

Rayuwar ta ci gaba da tafiya ana gungura wa.
Yayin da a kullum dukiyar Alhaji Abubakar Mai Kyau ƙara bunƙasa take obaaaaa.

A lokacin ne kuma ya buÉ—e wurare da Yawa. banda waÉ—anda ya buÉ—e a baya, Ya buÉ—e wurare kamar su.

Mai kyau Chinese Restaurant.
Mai Kyau Indian Restaurant.
Mai Kyau Korean Restaurant.
Mai Kyau Spanish Restaurant. And Mai Kyau ethiopian Restaurant. Et.c.😘

Sannan kuma Ya buɗe Company na ƙera Takalma Wanda ya yi ma laƙani da.

'MAI KYAU ABBAN FEEFAH'
A Adamawa State, kana kuma ya buɗe wani Company shi kuma na ƙera Atamfofi, materials, laces a Borno State.

Kana ya buÉ—e wani company again na qera wayoyi shi kuma aka saka masa suna.

Mai Kyau
Bayan haka ya buɗe restaurant daban daban da kuma companies daban daban a kowani State na faɗin Nigeria, sannan kuma hatta ƙasashen waje akwai companies nasa da Yake ƙera kaya daban daban kamar irin ƙasar.

Amsterdam, Romanian, Spain, Poland, Greece, Austria, Italy, Egypt, Sudan, Libya, Eritrea sai kuma Germany Wanda acan companies nasa sunkai uku sai kuma Malaysia. E.t.c.💫💫

______**

Rayuwa ta ci gaba da tafiya ta ko wani ɓangare cikin sauri sauri Yayin da zuwa wannan lokacin shekarun Afeefah goma a duniya Yayin da suke kai ɗaya da Lailah gasu suna masifar kama sosai Like a twin's.

A wata Ranar lahadi da safe misalin ƙarfe goma sha biyu.

Afeefah tana zaune a palon gidan ta ƙura karantun Alqur'ani a plasma tv, na palon tana sauraro sai faman karatu take yi, da yake lokacin ita da Lailah sun kammala primary school sun ma zama Jarabawar fita.

Sai faman karatun ta take Yayin da Lailah take zaune daga ƙasan carpet sai roƙon Afeefah ɗin take a kan ta kashe karatun ta kunna musu cartoon su kalla, ita kuma Afeefah tayi ma ta kunnen uwar shegu.

Su biyu ne kacal a palon.

Daya ke shi Abdulmaleek Ya kammala secondary school Ya tafi ƙasar Russian karatu.
Yayin da su kuma Nainarh da Nailah suke a Boarding school suna karatu.
Ita kuma Zaynerb da taƙi Boarding, a ranar tana saman Bene a Bedroom ɗin ta tana karatu.
Yayin da Momy Rafi'at aka ma ta kiran Emergency a hospital É—in ta.
Shi kuma Daddyn su Alhaji Abubakar Mai Kyau kuma Ya fita company domin cike wasu Takardu, duk da cewar ba Ranar aiki Bane, da yake Yana shirin komawa ƙasar Jamus ne domin Ya qara bunƙasa Harkokin kasuwancin sa, na can.

Kallon Lailah dake faman sha re Hawaye tamkar an dake ta, Afeefah tayi tana dariya ta ce

"Allah sis kina Bani mamaki, ace ke kwata kwata bakya ƙaunar kiji an saka karatun Alqur'ani Mai Girma, a gida sai kace Ƴar maguzawa, to Indai kinaso na kashe karatun na kunna miki cartoon, sai kin Fara gogemun Ƙafata, amma idan kin yadda fa." 🌚

Da sauri Haleesat dake can Dining Room tana faman kai loma, kallon Afeefah jin abin da take cewa, sai dai da yake ita ɗin miskilar gaske ce, ba tayi magana ba, sai ma dakata wa da cin abincin da tayi, tana kallon drama ɗin su domin ganin yadda zata kaya, shin Lailah zata Yarda ta goge ƙafar Afeefah ɗin, ko kuwa?."
Ita dai Haleesat iya sanin ta da Lailah muguwar Ƴar girman kai ce, ga ta da mugun tsafta, ga aji, ga Raini ga.!! umm ummm.🧐

Ajiyar zuciya Lailah ta sauke sannan cikin murya irin na Wanda ya sha kuka Ya ƙoshi ta ce

"Idan na goge miki ƙafar zaki bani remote control ɗin, na kunna cartoon ɗin?."

Murmushi Afeefah tayi wanda ya bayyana dimples É—in ta duka biyun ga wushiryarta Mai Kyau, tana juya manyan dara daran kyawawan fararen idanunta ta amsa ma ta

"Yeah it's okay, idan zakiyi, to ga Remote sai na baki, ki kashe karatu ki kunna cartoon."

Da jin Haka Lailah tayi murmushin murna, sannan ta durƙusa dai dai saitin fararen ƙarfafun Afeefah dake sanye cikin farar safa.
Ta cire safar sannan takai hannu ta cire hular kanta, nan take dogon gashin kanta Wanda yasha kitson kalaba ƙanana ya zubo ma ta har gadon bayan ta.

Nan naɗe hular tayi, yadda zata ji daɗin goge ƙafar, sannan ta kamo ƙafar Afeefan ta ɗaura akan cinyarta, tana goge hawaye.
Yayin da Afeefah take dariyar murna, Lailah har takai Hannu ke nan zata fara goge ƙafar Afeefah ɗin, taji anyi sama da ita sannan an jefa ta saman 3sieter.

Da sauri gaba É—ayan su tun daga kan Haleesat dake zaune a Dining,nda Lailah da aka yi wurgi da ita saman 3sieter Like a Little kid, da kuma Afeefah wacca take saman 1sieter suka É—ago kansu a tare domin ganin mutumin da ya yi wannan aiki.

Momy Rafi'at ce tsaye sai Faman huci take yi, ga yarinyar ta xixi mai shekaru Takwas a duniya tsaye gefe.
Ashe tun lokacin da Afeefah taba Lailah zabi a kanta goge ma ta ƙafa sannan ta bata remote.
Momyn ta shigo ta tsaya ne domin ganin shin Lailah zata gogewa Afeefan ƙafar ko kuwa.

A mugun fusace Momy Rafi'at tayo kan Afeefah bata tsaya jiran komai ba, tasa Yatsun hannunta duka guda Biyar waÉ—anda Allah ya azurta ta dasu ta bawa Afeefah lafiyayen mari. Wanda sai da taga wuta tsaban azabar da ya ziyarci duka fuskar ta dama gangan jikinta.

Sannan ta fin ciko ta daga saman kujerar, nan ta shiga dukan ta kamar Allah ya aiko ta, tana dukanta tana Marin ta, ita kuwa Afeefah in banda kuka babu abin da take yi saboda tsananin azaba har muryar ta, ta dashe, da kyar ake iya jiyo kukan da take yi.

Lailah kuwa sai faman dariya take yi tana faÉ—in

"Ƙara ma ta, Momy ƙara ma ta."

Yayin da Haleesat dake Dining Room tayi shiru tana kallon ikon Allah cike da mamakin dukan da Momy take wa Afeefah, ita fa bata ga abin duka ba anan, sai dai bata ce komai ba, haka zalika bata miƙe ba a domin ta taimakawa Afeefah ɗin, sai dai ta ji babu daɗi a zuciyarta.
Chapter 71 · 0% Book details