← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 92

Sashe 75

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Oh Auntie na bazaki tunamin sunan ki ba ko?."

Afeefah ta faɗa hakan cike da shgagwaɓa. Wanda ba ƙaramin kyau ya ƙara ma ta ba.

Dariya xixi dake gefanta tayi kana ta ce "Sunanta Sis Leesat fa."

Waro ido waje Afeefah tayi, aikuwa bata jira komai ba, ta Rungumo Haleesat tana faÉ—in

"Am so sorry My Auntie Haleesat, sam ban gane ki bane fa."

Bayan sun kammala da Haleesat nanma suka yi da Momy sai dai Afeefah batayi hugging É—in Momyn ba, gaisheta kawai tayi sannan tayi gaba wajen xixi batare da, ta jira Momy É—in ta amsa ba.

Wanda hakan ba ƙaramin taɓa zuciyar Yaranta Ya yi ba, kawai dai shiru suka yi.

Nan ma gaisawa suka yi da ƙanwar nata xixi cike da farin cikin ganin juna sannan kuma....

Cak Afeefah ta tsaya tana kallon kyakyawan matashiyar budurwar dake tsaye gabanta, wacca ba zata haura shekaru goma sha shida ba a duniya.

Kallon ta take kamar yadda ita ma take kallon ta, a kalla ba'a kasara ba, sun É—auki tsawon mintuna uku suna kallon juna, suna tariyo komai da ya faru a shekaru shida da suka wuce tamkar Ranar Abin ya faru, tsakanin su.

Ita Afeefah a nata ɓangaren kallon da take yiwa Lailah bana komai bane Fa ce, kallon tsantsan kewar ta da begenta da tayi.

Yayin da ita kuma Lailah a nata ɓangaren take yiwa Afeefah kallon kin canza da yawa kin koma can kina Rayuwar ki, ko kewar mu bakiyi ba, kinyi kyau kin ƙara tsayi girma da komai da komai.

Gaza jurewa Lailah tayi da gudu ta ƙarisa ta rungumo Afeefah a chest ɗin ta tightly tana share qwallar da ya cika ma ta ido faɗi take

"Oh My Angel, Oh My Only One, wato baki damu da concern namu ba, shi yasa tunda kika tafi koda sau É—aya Bakiyi tunanin kiran mu a waya ba, ko kuma kizo mu ganki ba ko?."

Duk tana maganar ne cikin harshen Turanci tana surkawa da Spanish sannan kuma tana haÉ—awa da Harshen Jamus domin kuwa duk a tunanin ta Afeefah bata iya Hausa ba yanzu.

Murmushin farin ciki kawai gaba É—aya mutanen dake wurin suke yi barin ma dai Alhaji Abubakar Mai Kyau.

Murmushi Afeefah tayi bayan sun saki juna sannan ta buÉ—e baki zata yi magana. Domin kare kanta.

Da sauri Lailah takai fresh hand É—in ta wanda yake sanye cikin handgloves white color, ta rufe wa Afeefah baki sannan ta ce

"Kar ma kice komai ba. Yanzu ba tukunna, sai a gida yanzu dai mu fara komawa gida sannan ki amsa tuhumomi kala kala."

Dariya suka yi gaba É—aya sannan gaba É—ayan su suka shiga motoci suka bar airport É—in tare da Rakiyar escort services.

Mota É—aya Afeefah da Lailah suka shiga, sai kuma xixi. Yayin da Nainarh da Nailah da kuma Haleesat suka shiga mota guda, sai kuma É—ayar Motar Daddy Alhaji Abubakar Mai Kyau, da kuma Momy Rafi'at suka shiga. Motoci uku ke nan sai kuma motocin escort guda biyu.
Gaba da Bayan su ɗoɗar suke taka titin Abuja City suna fella gudu kamar ba gobe da jibi kai harda ma gata.🌚

___*💋 SARAUNIYAR KYAU 💋*_________ƚαƙυɳ ϝαɾƙσ__________________________________________________________💥👑𝑻𝒉𝒆 𝑮𝒍𝒂𝒎 𝐐𝐮𝐞𝐞𝐧👑💥____________________𝑩𝒚:𝑻𝒉𝒆 𝑵𝒂𝒊𝒏𝒂𝒓𝒉 𝑲𝒅____𝑲𝒉𝒂𝒅𝒆𝒆𝒋𝒂𝒓𝒕𝒉. 𝑺𝒂𝒃𝒊'𝒖. 𝒀𝒂𝒉𝒚𝒂𝒉🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆
💦𝑳𝒂𝒇𝒂𝒛𝒊 𝑾𝒓𝒊𝒕𝒕𝒆𝒓'𝒔 𝑨𝒔𝒔𝒐𝒄𝒊𝒂𝒕𝒊𝒐𝒏💦🤙

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

Page *91&92*
_-_Still Free Page fa_-_🥰

**

A cikin mintuna kaɗan suka ƙariso Katafaren Gidan Alhaji Abubakar Mai Kyau. Wanda ya ɗauki tsayin shekaru yana gina abin shi, sai wannan Lokaci ne ya kammala.

Wangale musu haɗaɗɗen gate wanda shikaɗai ma Abin kallo ne a yankin securities suka yi, sannan slowly jerin motocin guda Biyar suka cin na Hancin su cikin ƙaton gidan. Wanda ya gaji da haɗuwa ta kowani ɓangare.

Gaba ɗayan su fitowa suka yi a tare lokacin da securities suka bubbuɗe musu murfin motocin sannan gaba ɗaya suka haɗu wuri ɗaya sai faman ƙarewa gidan kallo suke yi, domin kaf cikin su babu wacca ta taɓa zuwa koda kuwa duba Yanayin gini da tsarin gidan ne, asalin ma basu san da Gidan ba, sai kwana kwana nan.
Gidan ya gama tafiya dasu fi ye da tunanin mai tunani.

A hankali sannan kuma cikin nutsuwa suke tafiya har suka ƙarisa bakin ƙofar palon, sannan kuma wani daga cikin securities na gidan ya danna wasu Lambobi a jikin ƙofar palon, sai ga ƙofar Glass ɗin ta buɗe, gaba ɗayan su, ɗunguma suka yi suka shiga cikin haɗaɗɗen palon. Wanda tsayawa faɗin irin haɗuwar sa ma kawai sai an shafe page's fi ye da kima babu a dadi ba'asani ba.
Domin kuwa gaba É—aya gidan bama iya palon ba kaÉ—ai ba.
Abin kallo ne amma dai bari mu gani ko lissafo Yanayin tsarin gidan da komai da komai zai yiwu ko kuwa.💫🌚

Da Farko dai Yanayin tsarin gidan shi ne.

Gidan Babban gida ne. Wanda Yanayin tsarin ginin gidan turawa ne dashi.
Kana shiga cikin gidan abin da zaka fara cin karo da shi a tsakiyar compound na gidan shi ne wani ƙayataccen fountain ma'ana marmaro. Wanda yake feshin ruwa fari kar kar Abin gunin ban sha'awa da burgewa.
Ga wasu flowers da aka ƙawata wurin dasu suka yi ma wannan fountain Zobe.

Daga can gefe daga ɓangaren hannun dama kuwa, wani haɗaɗɗen parking lot ne. Wanda a kalla ba'a kasara ba, sai ya cinye tsala tsalan motoci guda tara masu Rai da motsi.

Gaba ɗaya filin ƙaton gidan a ƙawace Yake da Grass carpet koraye ɓashau dasu, gasu gunin ban sha'awa da ƙayatarwa.

Daga can gefe kuwa ɓangaren hannun hagu wani Katafaren madaidaicin garden ne. Wanda aka zagaye shi da Net white color daga ciki kuwa, zasu wild Animals haɗe da dabbobin gida kyawawa dasu ana kiwa tasu a ciki ne, dabbobin ciki sun haɗa da.

•birds=tsuntsaye masu kyau da ban sha'awa, sai faman karkaɗa wings nasu suke gunin burgewa, da saka nishaɗi, ga mai kallo.🕊️🐦🦜

•dogs=sai kuma karnuka wasu sky Brown dasu irin na Turawa suma sai faman karkaɗa Tail nasu suke gunin burgewa da saka feeling better ga mai kallo .🐕

•squirrel=kurege ne, seagull=tsuntsun seagull ne, peacock=ɗawisu, ostrich=jimina. E.t.c.

Kai idan na tsaya lissafo kalar dabbobin ciki sai mu ƙare labari ba'a gama ba, saboda wajen da Gidan baki ɗaya an ƙawata su ne da gini na musamman wanda ba'a ko'ina ake samun kalar sa ba.

To daga Can gefe kuma na gidan, wani Katafaren swimming pool ne. Wanda Ruwan cikin sa yake sky blue gashi gare gare dashi harda wani madaidaicin Bene, a jiki Wanda Idan mutum ya kammala abin da zai yi a ciki zai kama su ya fito daga can jikin swimming pool ɗin, dai still harda wurin da mutum zai dan na idan yanaso Ruwan swimming ɗin Yayi dumi Idan kuma cold Yake so tohm.😎
Daga waje kuma bakin swimming pool ɗin, ga wasu haɗaɗɗun kujerun hutawa da aka ƙawata gefan swimming pool ɗin dasu.

*Again*
Daga wani ɓangare na gidan kuma still wani ƙayataccen Katafaren Garden ne, na hutawa. Wanda cikin sa aka ƙawata da bishiyu kamar na.
•Apple=tufa, Banana=Ayaba, grapes=innabi, pear=gwaiba, pineapple=abarba,
•gasunan dai Taura, kwakwa, magwaro da sauran su.

Can gefe kuma still a cikin garden É—in wasu kujeru da seesaw na Lilo ne, a jere gunin burgewa.
Gaba ɗaya ƙasar wurin grass carpet ne garden ɗin ya haɗu obaa.

Kai masu karatu bafa zaku fahimci abin da nake nufi ba, saboda ginin gidan ya haɗu sosai, daga can gefe kuma filin wasan ni ne ƙato mai girman gaske.

Daga Asalin Gidan kuwa gini ne mai hawa uku, kana ƙari sawa Bakin ƙofar palon. Wanda yasha fenti fari mai shaining kalar wannan Farin mai ɗaukar Hankali da burgewa.

Daga ɓangaren dama wani haɗaɗden glass staircases ne. Wanda Idan mutum Ya Bishi kai tsaye zai sadaka da wani Arnen part na musamman. Wanda Yasha kayan duniya a hawa na Biyu. Wanda shi ne ɓangaren Abdulmaleek na musamman da aka gina masa.

Sai kuma ɓangaren hagu shima dai Glass staircases ne waɗanda Idan mutum yabi kai tsaye zai sadaka da Wani part shima a hawa na uku. Wanda shi kuma Yake a matsayin ɓangaren Alhaji Abubakar Mai Kyau.

Sai kuma Idan aka dawo ga tsakiyar ginin kuma, wajen bakin ƙofar palon ita kanta ƙofar ma Abin kallo ce, domin kuwa ta glass ce, irin wannan ɗin glass. Wanda na ciki ne kawai zai hango na waje Yayin da shi kuma na waje bazai hango na ciki ba.

Sannan kuma ita kanta Door É—in, sai an danna wasu special numbers sannan zata buÉ—e, kana kuma tana amfani da zanen Yatsa wato fingerprint.

Daga cikin palon kuwa aljannar duniya ke nan, palon ya haɗu fi ye da tunanin mai tunani, domin kuwa ƙaton palo ne, Wanda Yaji kayan mo re Rayuwa kala kala, ba abin da babu babu ne kawai babu a ciki.

Daga tsakiyar palon wasu Royal sofa's ne set Biyu, masu Launin sky Milk color Yayin da cushion É—in su suke coffee and light orange and Ash color.

Komai na palon sky Milk and coffee color ne, hatta curtains É—in palon sky Milk and coffee color ne.

Qofar palon yana daga Right hand sai ya kasance daga West and North na palon wasu haɗaɗɗun Arnayen staircases ne, wa'inda aka ƙerasu da zallar glass, domin kuwa hatta da handrail na staircases ɗin da kuma step's ɗin duk na glass ne.

Sai dai kuma staircases ɗin dake ɓangaren west Yamma wanda ya kasance twin's ne, ɗaya kai tsaye zai wuce da mutum izuwa part na Abdulmaleek da yake hawa na Biyu.

Yayin da shi kuma É—ayan kai tsaye zai wuce da kai part na Mister Mai Kyau, Alhaji Abubakar dake hawa na uku.

Sai kuma staircases wanda yake ta ɓangaren North Arewa shi kuma kai tsaye zai wuce da mutum hawa na ɗaya wanda shi kuma yake a matsayin part na Momy Rafi'at.

Bedrooms Huɗu ne Manya Manya daga ko wani part na Palon Yayin da akwai ƙaton kitchen wanda shima yasha kayan Mo re Rayuwar duniya ba'a magana, sai kuma Dining Room shima wanda yake wada ce da glass chairs guda goma sha biyu jere.
Chapter 75 · 0% Book details