← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 92

Sashe 82

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba É—aya dariya suka kuma yi habba daga haka kuma fira ta kuma shiga tsakani cike da nishaÉ—i.
Shidai Maleek shiru ya yi yana kallon Ahalin nasa gaba ɗaya sun canza sosai. Jinsa yake tamkar wani sabo cikin su, sai yaji yau ya kuma yarda da wannan maganar da ake cewa 'Duk Wanda Yabar gida, Tofa Tabbas Gida Ya barsa'. Home is not a place it's feeling for All people.💞

*KANO*

Wannan karon da tsananin mamaki ya kuma kallon mahaifiyar tasa jin abin da take faÉ—i, shifa sam kansa ya É—aure ya kasa fahimtar komai yadda ya kamata.

Murmushi tayi sannan ta ci gaba da cewa

"Umarni nake baka, akan kaje ka nema soyayyar Jiddarh saboda sai da hakan burina na tsawon shekaru fi ye da ashirin zai cika, idan kuma ba haka ba, zan san abin yi."

Murya na É—an rawa Yace

"Ni nifa ina da wacca nakeso kuma zan Aura, sannan kuma da kike maganar na nema soyayyar jiddarh nifa matsayin ƙanwa na ɗauke ta sannan kuma..."

Katse sa tayi cikin tsananin ɓacin rai sannan cikin tsawa da ɗan ɗaga murya ta fara magana

"Heesham, indai ni ce mahaifiyar da ta haife ka ina baka umarni da kaje ka nema soyayyar wannan yarinya jiddarh, domin sai da hakan Burina zai cika."

Sai kuma ta É—an sassauta murya tana tambayarsa da cewa

"Menene sunan ita yarinyar da kakeso ka Aura É—in?."

Wannan karon cikin sanyin murya ya fara maganar domin kuwa mahaifiyar tasa a maimakon mamakin ta da ya faraji, tofa yanzu tsoro ta fara bashi, ganin yadda take maganar cikin kakkausar murya.

"Sunanta Bilkisu ne."

"Bilkisu. Bilkisu.."

Auntie ta maimaita tana ya mutsa fuskar ta, wacca ta ɓaci da Bleaching ta gode Allah.

"Ita ɗin Ƴar ina ce haka?".

"Katsina ne mahaifarta."

Ya bata amsa cikin sauri sauri, wata ɓoyayyar ajiyar zuciya ta sauke, jin ba wacca take tunanin ba ce, sannan ta ce

"Babu damuwa ita ma zaka iya Aurenta, amma fah Bayan ka Aura Ƴar uwarka Jiddarh. Zuwa lokacin Burina na tsayin shekaru ya cika sannan...."

Gyara zaman sa Ya yi saman swivel chair da yake kai sannan ya kira ta da sunan da sukafi kiranta dashi.

"Auntie."

Ta amsa sannan ya ci gaba da cewa

"Shin zan iya sannin wannan Burina naki da kike cewa har saina Aura Jiddarh shi ne zai cika?."

Murmushi tayi kalar na cikakkun wayayyun Mata tana kaÉ—a ido ta amsa masa da faÉ—in

"Oh no Heesham har yanzu kai yaro ne ba zaka fahimci komai ba, koda na faÉ—a maka."

"Kai, Auntie ni ne Yaron? nafa Haura Twenty five highly fa."

Cewar Heesham yana zare ido jin an kira shi da Yaro.

Still it's her cheek have clear smile, shiru tayi sannan ta kuma cewa

"Habba My first Born, just chill Boss, mana daga wasa to na yadda kai ɗin, ba yaro bane, Kocin ne."🥳

Tayi maganar tana Æ´ar dariya sannan ta ci gaba da cewa

"Wato Heesham misali kai ne kana da wata Riga wacca wannan Riga ta kasance tana da wani masifar kyau da tsada, kowa sonta yake kaima hakan, kana masifar ƙaunar ta, sai kuma ya kasance ita wannan Riga daga ka ɗaukota ka saka ta a jikinka zata dinga yi maka ƙaiƙayi ta ko wanne ɓangare na jikin ka har sai ka cire ta, ka ƙona ta da wuta da fetur ta zama babu ɓurɓushinta sannan zata dena wahalar da kai shin idan kai ne ya zaka yi da wannan haɗaɗɗiyar Riga da kake masifar ƙauna?, shin zaka a jeta ne gefe ka dinga kallo kanajin daɗi, ko kuwa zaka ƙonata ne ka huta saboda bata da wani amfani?..."

Murmushi Heesham Ya yi Yana nazarin maganar ta, tabbas idan ya fahimta wato dai Hausa take masa cikin Hausa, sai dai kuma daga maganar ta bai fahimci komai ba, saima É—aure masa kai da maganganun nata suka yi, ajiyar zuciya ya sauke yana kallon ta, sannan ya bata amsa da cewa

"Gaskiya idan ni ne mutum mai wannan Rigar tunda ina ƙaunar ta sosai, kawai zan saƙaleta ne na dunga kallon ta kullum tunda saka ta bazai Yiwu ba."

"Oh Heesham wannan maganar naka is not a efficacy, bazai yiwu ba, kawai kabar zancen nan, domin kuwa yafi ƙarfin tunanin ka."

Heesham zayyi magana yaji Alamar za'a shigo Bedroom ɗin, hakan ne Yasa sa fasa faɗar abin da zai ce, sannan ya mayar da kallon sa kan ƙofar.

A hankali ta tura ƙofar ɗakin ta shiga jikin ta sanye cikin Elegant Beauty Dress doguwar gown c.green color, wacca daga gaban gown ɗin Anyi ado da wasu stones sky green masu shaining, gown ɗin mara hannu ce, gashi ta matse ta gam gam, kanta babu hula sai gashinta Wanda Yasha gyara ta mishi style in braid.

"Oh Jiddarh lafiya kuwa naga kina faman dafe kan ki haka?."

Cewar Auntie a ɗan ruɗe, ƙari sawa wurin ta Jiddarh tayi sannan ta zauna kusa da ita, ta jingina kanta da Headboard na gadon da Auntie take zaune saman sa, tana faɗin

"Auntie kaina ciwo yake min kamar zai tsage gida biyar, haka nake ji."

"Oh sannu fah, kin sha magani kuwa?."

Auntie ta tambaya tana kamo ta jikin ta, ganin hankalin mahaifiyar tashi ya koma kan Jiddarh ne. Yasa shi tashi da sauri yabar bedroom É—in, kai tsaye staircases ya nufa yana taka steps ya lalubo wata lamba kana ya dan na ma ta kira.

"Oh no Way gaskiya Auntie kema kin san bama shiri da magani ko kaÉ—an, kawai dai Yanayin hayaniyar dana shiga Yaune Ya ka womin Headache, amma nasan zuwa anjima zan dawo Normal nawa fa."

Cewar Jiddarh tana kyaɓe Beauty face nata. Domin ta tsani magani sama da komai.

*ABUJA*

*Wuraren Ƙarfe Biyar Da Rabi Na Yamma*

Gaba ɗayansu Ahalin Gidan suna tsai tsai ye a parking lot na gidan. Tun daga kan Daddy Mister Mai Kyau, da kuma Momy Rafi'at sai Nainarh, Nailah, Haleesat, Zaynerb, Afeefah, Lailah sai Deejarh sai kuma sauran baƙi.

Suna yiwa su Mamy Zuwaira da kuma Mamy Jawaheer, da Sakeenah harda Jummai waÉ—annda a yau zasu koma Jigawa State. Yayin da sauran kuma sai zuwa gobe zasu wuce ta Kano sannan su wuce States nasu.

Sai faman waige waigen ta inda zata hangosa take amma bata hango kowa ba, tayi mamakin Rashin ganin sa cikin mutane.
Kamar ance ta ɗaga kanta wajajen part nasa, aikuwa ta hango sa tsaye yana leƙen su ta ƙaton glass window dake palon sa. Yana sanye cikin Black t-shirt and short white color hannun sa riƙe da coffee cup yana sipping a hankali.

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta masa alama da hannunta cikin iska wai zasu Tafi fah, baizo Ya yi mata bye bye bah 👋.

Murmushi ya yi daga inda yake tsaye sannan shima Ya yi ma ta Bye bye daga inda yake tsaye.
Maƙe kafaɗa tayi wai a'a, sannan ta kuma yi masa alama da tafiso Yazo.
shima maƙe ma ta kafaɗar Ya yi sannan Ya koma saman Royal sofa nasa ya zauna kana ya ɗauki remote control ya danna curtains na wurin suka koma suka Rufe.

Murmushi Tayi sannan cike da nishaÉ—i ta shige cikin tsadaddiyar motar su cikin zuciyarta kuwa faÉ—i take

"Oh my God wallahi Yaya Maleek is so adorable highly, nidai wannan zuwa Gidan Uncle Mai kyau gaba ta kaini tunda na sama dami a kala."

Murmushi kawai Afeefah dake lura da Love drama tsakanin Buddy nasu da Husnee take yi cikin zuciyarta faÉ—i take

"Ah Yaya Maleek kaga ta kanka indai Husnee ce wallahi."

Sai da suka ga ficewar motocin kaf daga gate na gidan nasu sannan suka juya suka yi ciki. Bayan sun shiga ƙayataccen palon ga tsananin maɗaukakin mamakin su part na Maleek suka ga Daddy mahaifin su Mister Mai Kyau. Ya nufa.😸

Ganin haka shima Uncle Yusuf da sai gobe zai koma Mai duguri da iyalansa yabi bayan sa.

_+_🥴🥴Oh Oh Malam Mai Kyau Yada Sauri Hakan?..🥴🥴_-_

Gaba É—aya murmushi suka yi harda Momy Rafi'at sannan Ita ma ta nufa staircases tana taka steps tana qwalawa Haleesat dake zaune saman 2sieter kira, tashi ita ma Haleesat tayi kana tabi Bayan Momyn nata.

Yayin da gaba É—aya suka zazzauna saman Royal sofa's dake Palon suka dasa sabon fira tsakanin su.

Afeefah da kuma Auntie Yusra matar Uncle Yusuf da Yaranta waÉ—anda suka zo da kuma Auntie Suwaiba matar Uncle Sagir da Yaranta wa'inda suma sai gobe zasu wuce Kano tare da su Zaynerb.

A hankali Deejarh takai fresh hand nata cikin pocket na gown dake jikin ta ta ciro wata siririyar chain, bata zinare bace sannan kuma bata diamond bace, kawai dai normal chain ne, amma fah Kalar wannan chain ne wacca bata komai.

Murmushi tayi sannan ta kuma mayarwa cikin pocket gown nata.

Kallon Afeefah dake zaune gefanta tana latsa waya tayi, kana ta ce

"Balarabiyar India kin san Menene kuwa?, a'a sai kin faÉ—a."

Cewar Afeefah.
"Toki Rufe idon ki."

Deejarh ta faɗa lokacin da ta miƙe tsaye ta koma tana fuskan tar Afeefah ɗin. murmushin da ya bayyana dimples tayi sannan tana faɗin

"Oh My Deejarh, Menene zakimin Idan na Rufe?."

"Kedai kawai ki Rufe."

"Okay."

Jin haka Yasa Afeefah ta Rufe idanunta tana jiran taji abin da Deejarh zatayi gaba.

Dariya Deejarth tayi sannan tasa hannunta cikin gown pocket dake jikin ta, ta ciro wannan Ƴar siririyar chain mai ɗaukar ido Like a diamond, sannan ta ce

"Yanzu ki buÉ—e, a hankali ta buÉ—e manyan dara daran kyawawan idanunta, aikuwa taci karo da wannan haÉ—aÉ—É—iyar siririyar chain mai tsananin É—aukar ido.
Dariya Deejarh tayi sannan ta miƙawa Afeefah ɗin chain ɗin tana faɗin

"Wannan ita ce kyauta na ta musamman a gareki."🤗

Fashewa gaba É—aya mutanen palon suka yi da dariya, Zaynerb na faÉ—i

"A gaskiya anyi son kai wannan haÉ—aÉ—É—iyar chain a rasa wacca za'a ba sai Afeefah Bayan Wanda ta samu Wajen gasa."

Haseeya da take É—iya wurin Uncle Sagir ta ce "Ah ta cancanta ne, shiyasa kika ga ta bata."

Ita kuwa Afeefah bakinta yaƙi rufuwa tsaban farin ciki, a Rayuwar ta tanaso ayi ma ta kyautar Abu, kamar dai sarƙa ko zobe kodai dangin waɗannan babu abin da take yi sai faman juya sarƙar a hannunta.
Chapter 82 · 0% Book details