← Book details Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 92

Sashe 29

Sarauniya Kyau Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ban taɓa aikata zina ba, ko lesbian, amma anso asakani a hanyar yi,"

"a'ina kuma suwa?,"

Haleesat ta jero mata tambayar, Heart ta ce "a school kuma ƙawayena," ta cigaba da cewa "baso ɗaya ba, ba kuma sau biyu ba ƙawayena sunsha ɗaureni, suce sai sunyi raping ɗina amma basu taɓa samun dama akaina ba, abin har mamaki yake bani,"

"Saboda me" cewar Haleesat ido waje, Heart ta ce "nima dai bansani ba, amma dai wasu suna cewa saboda kyawuna ne, yayinda wasu suke faÉ—in saboda diri,"

Dariya Haleesat tayi ta ce "ai sun faÉ—a gaskiya, shiyasa akeso mace ta dinga suturta jikinta da hijjabi a koda yaushe."

"Menene kuma hijjabi?," Heart ta tambaya, É—an murmushi Haleesat tayi tama, manta ko wacece a gabanta, ta ce.

"Sanya hijabi bin umarnin Allah ne da annabin sa, kariya ne daga fitina, alamace ta tsarkin zuciya, kyakkyawan ɗabi'a ce, garkuwa ne daga faɗawa halaka, sutura ce daga al'aura, kariya ne da ga mazaje marasa mutunci fasiƙai, kariya ne daga aljanu, kariya ne daga shiga cikin azabar Allah da fushinsa, bautar Allah ne sanya hijabi."

Ajiyar zuciya Heart ta sauke jin Haleesat takai aya, sannan ta ce "to zan iya saka hijjab É—in?," murmushi Haleesat tayi ta ce "zaki iya mana."

Juyawa tayi tana kallon su Zuree da Feenah da sukayi tsuru tsuru dasu ta ce "me kuka yima Jenny?,"
Da sauri Zuree ta ce "Feenah ce ta saka mata qwayar bacci a lemu."

Girgiza kai Haleesat tayi sannan ta ce "kunyi ma kanku, kuma ban yafe ba, ta faɗa tana miƙewa saman bed ɗin, tahau ta ɗauko ribbon's ɗinta da hularta ta saka.

Kallon Heart tayi bayan ta dawo ta zauna a ƙasan ta ce, "sunana 'Haleesat Abubakar Mai Kyau', am very amazing to meet you," ta ɗanyi shiru sannan ta ci gaba da cewa.

"zamu iya ƙulla ƙawance dake?, tayi ma ta tambayar tana miƙa ma ta fresh hand ɗinta.

Hannun Haleesat kawai Heart take kalla sannan ta sauke ajiyar zuciya ta ce.

"yanzu bakiji haushin abin da naso ayi miki ba?,"

Haleesat tayi dariya sannan ta ce "ko kaÉ—an banji haushi ba, saima darasin rayuwa dana koya, da ma can tun farko laifi nane da nake zuwa Night club, amma yanzu, na fahimci wani abu a rayuwa, wannan abun shi ne bada kowa ake yadda ba, a duniya, komai dangantakar ka da mutum kuwa."

Murmushi Heart tayi sannan ta miƙawa Haleesat hannunta tana faɗin "kamar yadda na faɗa miki a farko sunana HEART CHENG JUNG' Naji daɗin haɗuwata dake."

Murmushi ita ma Haleesat tayi sannan tasa hannunta cikin na HEART suka ƙulla ƙawance.

Clock ɗin dake manne a wall na ɗakin ta kalla lokaci yaja sosai ƙarfe huɗu na asuba saura.

Kallon su Feenah tayi ta galla musu harara kamar qwayar idonta zai fito, sannan ta kalla Heart ta ce inaga fa saidai mu kwana ana gidan, saboda lokaci yaja sosai,"

"Okay baki da damuwa Heart ta bata amsa, tana murmushi.

Tashi Haleesat tayi ta shiga toilet bata daɗeba ta fito, kan bed ta haye abinta kallon Heart ta kuma yi, tayi murmushi sannan ta ce "saida safe, sabuwar ƙawa,"

Heart da ɗan mamaki ta ce "bakyajin tsoron su kuma yunƙurin yi miki wani abun?," tayi ma ta tambayar iyakar gaskiyar ta, dariya Haleesat tayi ba shiri sannan ta ce.

"Idan na amince da mutum na gama nawa, saura ya rage nasa ya kyautatamin ko ya ha'inceni, Nikam banada matsala shida Allah."

Heart ta ce "kina burgeni sosai fa,"

Haleesat tayi dariya, "da gaske nake fa" cewar Heart, "ai na sa ni," Haleesat ta bata amsa.

Murmushi Heart tayi sannan ta kwanta a saman doguwar kujerar da take.

Lumshe ido Haleesat tayi tana tuno kyakyawan mutumin da ta haÉ—u dashi É—azu da kyakyawar surarshi, mutumin da ko ainihin fuskarshi bata sa ni ba, balle kuma sunan shi.

*🩸ʂαɾαυɳιყαɾ ƙყαυ 🩸*

*☆ƚԋҽ ɳαιɳαɾԋ ƙԃ☆🤙*

Kiran sallah ne ya tasheta da ga baccin da ya fara ɗaukarta, a hankali ta buɗe kyawawan idanunta, bakinta ɗauke da addu'ar tashi daga bacci saukowa tayi daga kan bed ɗin toilet ta shiga ta ɗauro alwala, sannan ta fito, dagewa tayi iya ƙarfinta ta ɗakawa Zuree duka, a firgice kuma ta gigice ta tashi zaune tana zare ido.

"Bani key ɗin motar ki," Haleesat ta faɗa a dake kuma fuska a ɗaure, ba musu Zuree tasa hannu a trouser pocket ɗinta, ta ciro key ɗin sannan ta miƙa ma ta.

Karɓa Haleesat tayi sannan ta fita can parking lot motar Zuree ta buɗe ta ciro hijjabinta da kuma handbag ɗinta.

Cikin bedroom É—in ta dawo bata ga Heart ba, da alama toilet ta shiga handbag É—inta ta buÉ—e ta ciro wani madaidaicin scarf shimfiÉ—a shi tayi bayan saka hijjabinta ta tayar da sallah, tana idarwa bata tashi daga wajen ba saida tayi azkhar.

Wall Clock ta kalla ƙarfe bakwai da rabi na safe, kallonta ta mayar kan Heart da tun fitowar ta daga toilet taga tana sallah ta zuba ma ta ido ba ko gyaftawa.

ÆŠan murmushi tayi sannan ta ce "barkanki dai madam yanzu zan iya tafiya gida?," murmushi Ita ma Heart tayi sannan ta amsa da "yauwa barka, zaki iya."

Tashi Haleesat tayi ta É—auka handbag É—inta, bayan ta saka scarf É—in aciki.

Waje suka fito dukansu hadda su Feenah da Zuree waÉ—anda ko sallah ma saida rana ta fito gatsau sannan suka gudundura.

"Ko zan iya rage miki hanya" Heart ta tambaya tana kallon Haleesat É—in.

Haleesat bata ce ma ta komai ba ta nufi motar Heart É—in, har zata shiga kuma saita juyo, ta kalla su Feenah ta ce "daga yau nida ku anyi baram baram kar É—ayanku tayi gigin koda kirana a waya ne daga yau nida ku b.s.b.s.,"

Tana gama faÉ—in haka ta shige motar Heart taja suka bar gidan, ba wanda ya iya magana acikin har suka iso unguwan su Haleesat É—in, sai kuma lokacinne Haleesat ta fara jin faÉ—uwar gaba daurewa kawai takeyi.

Guri Heart ta samu a gefen wata tree a unguwan tayi parking, fitowa Haleesat tayi ta zagaya ta ɓangaren da Heart take, ɗan kwankwasa glass ɗin window tayi.

Buɗewa Heart tayi tana kallon Haleesat ɗin, murmushi Haleesat tayi sannan ta ce "nagode fa, amma please karki ƙara tunanin sannin wannan abun,"
"saboda me?," Heart ta tambaya, "saboda babu kyau," Haleesat ta bata amsa ta cigaba da cewa "zan iya samun phone number É—inki?,"
Heart ta ce "sosai ma, why not," wayarta ta ciro a cikin handbag É—inta tana rubuta lambar wayar da Heart take karanto ma ta.

Ƙurawa wayar ido tayi bayan ta gama rubuta lambar da Heart ɗin ta karanto ma ta ganin lambar bana Nigeria bane yasa ta kalla Heart ta ce "wannan lambar fa?,"

"Number nane na ƙasata, Ƙasar France yau zan koma na gama abin da ya kawoni nan ƙasar,"

Heart ta bata amsa.
Qura ma ta ido Haleesat tayi ita sai yanzu ma take ƙarewa Heart ɗin kallo yadda ya kamata.

Kyakyawa ce sosai, don bata mayi kalar ƴan nigeria ba, da gani ma bata da wata alaqa da ƙasar, amma kuma meyasa taga kamar tana mata kama da wata?, amma kuma ta kasa tuna koda wa Heart ɗin take kama.

Sha re tunanin tayi, sannan ta kalla Heart ta ce "okay Allah ya tsare hanya, bari na shiga gida," ta faÉ—a bata jira amsar taba tabar gurin.
Ganin haka yasa ita ma Heart taja motar ta tabar haÉ—aÉ—É—iyar unguwan.

Kwankwasa ƙaramar ƙofar gate ɗin Haleesat ta farayi zuciyarta na harbawa jin ba'ada niyyar zuwa a buɗe ma ta ne, yasa ta ƙara ƙarfin bugun amma shiru, can taji alamar za'a buɗe, ɗan matsawa tayi gefe.
Isah ne ya buÉ—e gate É—in yana faÉ—in "bama za'a bar mutum ya samu koda baccin sa fe yayi ba, anzo an takura da bugu nasan ma bazai wuce Æ´an maula ba, to ai sai aja please a rungumi sorry domin Alhaji Abubakar Sameer LamiÉ—o bayanan kuma ma.......

Sauran maganar da yayi niyyar gasa ma koma waye ne, ta maqale a bakin shi, sakamakon ganin wacca take tsaye a ƙofar, da sauri ya matsa gefe yana goge zufar da ta fara wanke mishi fuska, dan kuwa bai manta wahalar da ya sha ba a lokacin da yayi ma Lailah dariya ba, da tasa aka kusa korar shi daga aiki saida ƙyar ya samu Lailah ta haqura.

Haleesat ko kula sannu da zuwan da Isah yake ma ta batayi ba ta shige ciki gabanta na bugu da qarfin gaske.

Knocking ɗin ƙofar palon ta shiga yi baji ba gani, a zuciyarta kuwa tunanin yadda zazu kwashe da ƴan gidan take, dan ma sauƙinta ɗaya taji Isah na faɗin Daddynsu Mister Mai Kyau baya nan.

Jin an buɗe ƙofar ne, yasa ta ɗago daga tsugunawar da tayi, domin har wani ciwon mara takeji.

Ajiyar zuciya ta sauke ganin ERINA ce mai gyara palo, hanya Erina ta bata ta wuce ciki, shiga palon tayi bakinta É—auke da addu'o'i kala kala.
Bata ga kowa a palon ba, dan haka da saurinta ta nufi hanyar bedroom ɗinta, har ta saka ƙafa zata shiga ɗakinta taji muryar Auntie Nainarh tana kiran sunanta.

Rumshe idonta tayi da ƙarfin gaske sannan ta juyo dahm da dahm taji zuciyarta ta bada bugu saboda tsananin tsoro.

Duka Ƴan gidan ne zaune a dinning table hadda Momy da ta warke tsaf tana tafiya abinta.

A hankali ta fara taka ƙafafunta tana ƙarisawa dinning ɗin, yayinda gabaɗaya sassan jikinta babu inda baya rawa kamar mazari, cak taja tunga ta tsaya a tsakiyar palon taƙi gaba taƙi baya, kamar suna jira ta tsaya gabaɗayan su suka taso sukayo kanta da tambayoyi kowa da kalar tambayar da yake jefo ma ta.

Ganin haka yasa Momy Rafi'at ta daka musu tsawa cikin faÉ—a ta fara magana.
"wai ku wasu kalan mutane ne, a haka ne zata baku amsa koya da kalar tambayar da yake ma ta, taya zata iya baku amsa, ku sama guri ku zauna mana."

Umarnin ta suka bi gabaɗayan su suka zazzauna Nainarh, Nailah, da kuma Zaynerb a Three sieter, sai kuma Afeefah, Lailah a two sieter, sai Deejarh one sieter, sannan momyn ta kamo hannun Haleesat ta riƙe suka zauna a three sieter a tare da ya ke kujeru set biyu ne a palon.
Chapter 29 · 0% Book details